Yakin Ethiopia da Tigray: Labarin birnin Mekelle da aka raba da sauran duniya

People wait in a line to enter a bank in Mekele, the capital of Tigray region, Ethiopia, on June 25, 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wadannan mutanen suna layi domin cire kudi daga banki
An wallafa

Yarjejeniyar da aka amince da ita a makon jiya ta barin kai kayan agaji zuwa yankin arewacin Tigray a Habasha, ta sa an samu kwarin gwiwa game da kawo karshen yakin da aka kwashe watanni 17 ana gwabzawa.

Tuni aka katse al'amura da yankin na watanni masu yawa, abin da ya bar miliyoyin mutane cikin matsananciyar bukatar abinci da sauran kayayyakin amfani yau da kullum. Wani mazaunin yankin Mekelle babban birnin Tigray da yake zaune a karkashin mulkin kungiyar TPLF ya shaida wa BBC yadda rayuwa ta kasance a wadannan lokutan.

Short presentational grey line

"Kullum cikin jiran tsammanin samun abubuwan bukatar rayuwa muke," in ji shi.

A matsayinsa na mahaifi mai 'ya'ya biyu kanana, abu ne mai ciwo a ce ba ya iya samarwa iyalinsa abin da suke bukata.

"Ba zan iya komai da kudaden da nake da su ba saboda bankuna ma ba sa aiki baki daya. Da yawanmu muna fuskantar wannan matsalar.

Ba na iya amfani da asusuna na banki tun watan Yunin bara, karshe dai na koma aron kudi a wajen 'yan uwa da abokan arziki domin ganin na saya wa iyalaina abinci.

'Yan uwa da ke kasashen waje na da kudurin taimaka mana, amma saboda an yanke layukan waya da intanet abubuwan ba za su yiwu ba.

Bayan haka kayan abincin sun yi tashin goron zabi.

Geron da ake sayarwa da hatsi da fulawa da sauransu sun zama tamkar gwal.

Shekara guda baya, muna sayen kilogiram 100 na hatsi a kan kimanin dala 80, amma yanzu ya kai dala 146.

Berries on sale in a wheelbarrow
Bayanan hoto, Yanzu haka ana sayar da wasu kayan marmari wadanda a baya ba a amfani da su a kan tituna

An ce mu rika shuka kayan miya a gidajenmu kuma muna yin hakan. Amma matsalar ita ce dole mu nemo ruwan da za mu rika ba su.

Muna sayen lita 200 ta ruwa da za ta iya kai mu mako guda, amma yanzu ba ma iya yin hakan sai dai mu nemi ruwan a rijiyoyin da suke cikin gari.

Sabbin kaya da kuma cin nama a wajen kananan yara sun zama abin jin dadi."

Ruwan famfo da lantarki abubuwa ne da aka kayyade, ba kullum ake samunsu ba - sai a kwashe wasu ranaku masu yawa ba a samu wuta ba.

Da yawan mutane sun rasa ayyukan yinsu, mafi yawan masu shaguna da masu kasuwanci a Makelle sun rufe, saboda ba za su iya biyan hayar shagunansu ba.

People walking past an open market
Bayanan hoto, An rufe kasuwanni da dama a Mekelle amma har yanzu mutane suna sayar da kayan marmari a bakin tituna

Sakamakon haka, mutane sun fara sayar da kadarorinsu kamar motoci da kayan daki da kuma gwala-gwalansu domin su sayi abinci. Kuma dole ce ke sanya su karya farashin kayan.

Mutane suna karyar da kadarorinsu ya zama ba su da abin sayarwa za su fara bara, kuma yara da mata ne kan gaba a kan titi suna barar.

Babu komai a shagunan sayar da magani.

Masu fama da rashin lafiya sosai suna ta mutuwa saboda karancin magani.

Bikin addinai da na aure ko suna sun zama wani abin tarihi a yankin.

Samun labarai masu zafi sun zama wuya.

Mutumin ya ce ba ya samun shiga intanet "maimakon haka wajen masu sayar da jarida nake zuwa domin karanta labarai."

Rashin iya sayen fetur

Yanzu da dana ya dawo daga makaranta ina yawan yin tattaki. Wayata na cewa ina taku dubu tara zuwa dubu 12 a kowacce rana.

Ina tafiyar kilomita biyu kullum da safe idan zan kai shi makaranta. Matata kuma tana dauko shi daidai lkacin cin abinci.

Ina zuwa ne a mota na kai shi a baya, amma yanzu na ajiye ta sama da wata 18 saboda ba zan iya sayen mai ba.

Za ka iya sayen mai amma sai dai a wajen yan bunburutu. Litar da ake saya dala 10 yanzu da muna sayenta 0.42 kafin yaki.

Ba za mu iya daukar babura masu kafa uku ba domin yakai dala 2.

Yanzu keken doki ake amfani da shi domin zuwa unguwanni.

The back of a donkey-drawn cart

Mutane da dama sun koma amfani da kekuna, amma yanzu kuma ya yi tsada.

Mutane da yawa na fatan wannan rikici ya zo karshe, kuma mun ji dadi lokacin da muka ji an ce an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Suna jiran su ga idan da gaske ne za ta yi aiki, bayan da aka kawo kayan agaji na farko a ranar Juma'a, da alamun komai zai iya sauyawa.

Na ji dadi na tsira da rayuwata kuma yanzu har ina bayar da labarina na san wasu na cikin damuwa sama da tawa wasu kuma sun mutu.