Kungiyar agaji ta Red Cross ta kasa shiga Mariupol

An wallafa

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce ta kasa shiga birnin Mariupol, wanda dakarun Rasha suka yi kawanya a Ukraine, amma kuma ta ce za ta sake gwada shiga a ranar Asabar nan.

Kungiyar ta ICRC ta aika da manyan motoci da yawa dauke da kayayyakin agaji zuwa birnin, da zummar kai kayan da kuma kwashe farar hula wadanda ke son ficewa daga birnin amma shigarsu ta gagara.

Ana ganin farar hula akalla dubu 150 ne suke a birnin na Mariupol, ba tare da ruwa ko wutar lantarki ba.

Ayarin ma'aikatan na kungiyar ta Red Cross su tara na fatan shiga birnin a ranar Asabar, domin kai agaji ga wadanda suka zabi su ci gaba da zama a birnin a wannan yanayi.

Sannan kuma ma'aikatan agajin za su kuma jagoranci kwambar wadanda ke son ficewa daga birnin na Mariupol, zuwa wani sashen kasar ta Ukraine.

Sai dai abin da ake gani shi ne aikin agaji irin wannan na samun nasara ne kawai idan wadanda ke fada sun amince a shiga a taimaka.

Yunkurin kungiyar na farko na shiga birnin ya gagara ne saboda halin da ake ciki ba zai bar ta ba, saboda haka ne ta dage wannan yunkuri sai sai washe gari, Asabar ta gwada.

Ita dai kungiyar ta yi niyyar kai kayan agaji na kula da lafiya a manyan motoci akalla biyu zuwa birnin na Mariupol, a karkashin yarjejeniya, to amma kuma sai ya kasance Rasha ba ta da niyyar barin su su wuce.

Wannan ya sa dan karamin ayarin masu agajin da ya bar birnin Zaporizhzhia ranar Juma'a ya kasance ne da kananan motoci uku kawai.

Wadannan motoci da ma'aikatan Red Cross da suke musu rakayi suna da jan aiki a gabansu, inda za su kula da kwashe fararen hula daga Mariupol da sauran yankuna na kewaye a cikin motocin safa-safa akalla 40, wadanda gwamnatin Ukraine ta bayar.

Bayan wasu matsalolin, yadda za a iya kammala wannan aiki na kwashe mutanen a cikin rana daya kacal kamar yadda aka tsara, abu ne wanda kamar ba zai yuwuwa, idan aka yi la'akari da nisan tudun-mun-tsira a birnin Zaporizhzhia da Mariupol, da kuma yawan shingayen bincike na sojojin Rasha, banda ma kuma wuraren bincike na sojin Ukraine ma.

Hatta a lokacin da ayarin Red Cross ya bar Zaporizhzhia ofishin magajin garin Mariupol ya fitar da sanarwa cewa, har yanzu akwai hadari sosai a birnin, sannan kuma a takaice sanarwar na nuna cewa babu hanyar da wani zai shiga birnin.

Ba shakka duban mazauna birnin sun samu sun gudu da kansu, galibi ta hanyar amfani da motocin da hare-haren bam suka babbata, ta hanyar ratsawa wadannan wuraren bincike na sojin Rasha da kuma hanyoyin da aka dasa nakiyoyi.

To amma duk da haka har yanzu akwai dubban mutane a birnin, ba tare da ruwa ko abinci ba.

Bukatar agaji na magani da sauran kayayyaki na amfanin jama'a ta yi yawa sosai, kuma kusan babu wani gini a birnin da ya kasance hare-haren Rasha ba su lalata shi ba.