'Najeriya: Yan Majalisar wakilan Najeriya sun yi barazanar tafiya yajin aiki saboda tsaro

Majalisar wakilan Najeriya
An wallafa

Yayin da matsalar tsaro a Najeriya ke ci gaba ta'azzara, 'yan majalisar wakilan kasar sun ce za su tafi yajin aiki har sai sun ga canji a al'amuran da suka jibanci tsaro.

Hon Aminu Sulaiman Goro, daya ne daga cikin 'yan majalisar ya shaida wa BBC cewa, kullum suka zauna zaman majalisar suna samun rahotannin matsalar tsaro iri-iri.

Ya ce kuma tabarbarewar tsaron ta fi zafi daga bangaren arewacin Najeriya, shi ya sa kusan kullum sai sun yi muhawara a kan abin da ya shafi tsaro.

Dan majalisar, ya ce" irin masifun da ake shiga a ce yau an kashe mutane, gobe an sace mutane jibi an kona mutane, masifar ta kai ga cewa tsaro ya lalace."

Hon Aminu Goro, ya ce dama tuni an kori mutane daga titi, jirgin kasa da ake bi shi ma yanzu an je an jefa bam, abin takaicin ma hatta filin jirgin sama an je an kai hari.

Dan Majalisar ya ce, ''wannan ya nuna cewa an kama sama an kama kasa gashi nan dai, to bai san me suke so su yi ba.''

Hon Goro, ya ce," Mu a matsayinmu na 'yan majalisa mun ga cewa dukkan abin da gwamnati ta nema na harkar kasafin kudi ko doka, ba mu taba bata lokaci ba muna amincewa, to amma kullum masifar nan kara ta'azzara take".

Ya ce, ''muna ganin kamar jama'ar da muke wakilta sun fara gajiya ba wai da gwamnati ba, har mu kanmu'' in ji shi.

Dan majalisar,ya ce "Duk abin da za mu yi mun yi don ganin an inganta harkar tsaro, to amma kullum jiya i yau, don haka muka ga cewa lallai lallai ya kamata mu yi wani abu daban na rufe majalisa mu tash.''

Ya ce, " Za mu tashi har sai jami'an tsaro sun zo sun gaya mana menene yake faruwa? kuma menene za su yi?, sannan idan sun gaza me suke bukatar mu yi musu?".

Hon Goro, ya ce sun san cewa wasu abubuwan gwamnati na aiwatarwa, wasu kuwa ba su san dalilin da ya sa ba a aiwatarwa ba.

Ya ce, " Don haka idan mu ma za mu bi sahun ASUU ne, mu ma mu shiga yajin aiki, gara mu rufe mu tafi har sai an tabbatar mana da cewa jama'ar da suka turo mu, mu wakilce su, lalle lalle lafiyarsu da dukiyarsu da kuma rayukansu za su zamanto cewa an kares.''

Karin bayani

Harin da 'yan bindiga suka kai kan jirgin ƙasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin da daddare ya ɗaga hankalin ƴan Najeriya tare da sanya fargaba a zuƙatan mutane da dama.

Al'amarin ya jawo asarar rayuka da har yanzu hukumomi ba su fadi yawansu ba, sannan wasu sun jikkata sakamakon buɗe wuta da maharan suka yi bayan da jirgin ya taka bam din da suka dasa a kan hanyarsa.

Wannan batu ya zama matsalar tsaro ta baya-bayan nan mafi muni da ta faru a ƙasar da kuma ta ɗimauta mutane, musamman ganin akwai a ƙalla fasinjoji 970 a cikin jirgin.

Hanyar Abuja zuwa Kaduna ta zama jigo mai sada miliyoyin mutane da arewacin ƙasar daga babban birnin tarayya Abuja da kuma kudanci.

Wannan layi ne