Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Turai za ta bukaci China ka da ta taimaka wa Rasha kan Ukraine
Tarayyar Turai za ta bukaci China da kada ta samar da makamai ga Rasha a yakin da take yi da Ukraine, sannan kuma kada ka taimaka wa Shugaba Putin a kan takunkumin da aka sanya masa.
Shugaba Xi, wanda ya ki ya fito fili ya yi Allawadarai da matakin da Rasha ta dauka na mamayar makwabciyarta zai yi wata tattaunawa ta bidiyo da jami'na Tarayyar Turai ciki har da shugabar hukumar Turan Ursula von der Leyen.
Za a yi taron ne na bidiyo a lokacin da alaka tsakanin Tarayyar Turai da China ta yi tsami.
A farkon watan Fabrairu, China da Rasha suka fitar da wata doguwar sanarwa, wadda a ciki suke bayyana cewa alakarsu ba ta da iyaka.
Shugabannin Tarayyar Turai sun damu kan abin da suka gani a matsayin wata manufa ta sake fasalin tsari da manufar duniya, daga wannan sanarwa da kasashen biyu suka fitar ta alakarsu.
'Yan makwanni kadan bayan nan ne sai Shugaba Vladamir Putin ya kaddamar da yakin mamayar Ukraine.
Jami'an Tarayyar Turai a yanzu sun yi amanna gwamnatin Rasha ta bukaci taimakon soji daga China da kuma taimakon da za ta samu sassauci daga takunkumin da aka sanya mata.
Kafofin Tarayyar Turai sun ce Shugaba von der Leyen za ta bukaci Shugaba Xi na China da ya yi watsi da wannan bukata ta Rasha, a maimakon haka shugaban ya yi amfani da karfin China wajen kawo karshen
yakin, suna masu cewa illar da yakin zai yi ga tattalin arzikin duniya aba ce da za ta shafi kowa.
To amma kuma ministan harkokin wajen China a wannan makon ya ma yaba wa Rasha ne inda yake cewa alakarsu da Rasha na tafiya yadda ya kamata
jami'an Tarayyar Turai ba sa tsammanin samun wata yarjejeniya ta a zo a gani a taron na ranar Juma'a, amma dai suna sa ran shawo kan China ta sa Shugaba Putin da kada ya yi amfani da makaman kare dangi a yakin da yake yi da Ukraine.