Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ruwa ya cinye mutane takwas yayin tsere wa harin ƴan bindiga a jihar Neja
Hukumomi a jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Najeriya sun tabbatar da mutuwar akalla mutum takwas yayin da ake ci gaba da neman wasu ƙarin biyar a ruwa, bayan da kwale-kwalensu ya kife.
Mutanen dai na ƙoƙarin tserewa daga ƙauyensu na Galkogo da ke yankin Munya ne sanadin wani hari da 'yan bindiga suka kai a ƙauyen.
Waɗanda suka mutu a hatsarin jirgin ruwan sun haɗa mata biyu da ƙananan yara shida.
Ga karin bayanin da Darakta Janar na hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar ta Niger, Ibrahim Ahmad Inga ya yi wa Ishaq Khalid na BBC.
Ibrahim Ahmad Inga: Kawo yanzu mu ma muna da wannan labarin kuma mun riga mun shaida wa mai girma gwamna ga abin da ke faruwa a yankin Zumba - wasu mutane ne da ake zaton ƴan bindiga ne suka afka wa garin Kalgoko.
To a wajen ƙoƙarin ƴan garin su tsere zuwa wani wuri wanda suke tunanin akwai tsaron da ya fi inda suka bari saboda wannan hari da aka kai musu, sai wannan hatsari na jirgin kwale-kwale ya faru.
BBC Hausa: Kawo yanzu, kamar me wannan hatsari ya haifar?
Ibrahim Ahmad Inga: Eh to akwai matan aure biyu da Allah Ya yi musu rasuwa a ciki, akwai kuma ƙananan yara shida da su ma an riga an yi jana'izarsu.
Sannan akwai wasu mutum biyar da har yanzu ana ƙoƙarin zaƙulo su ko a raye ko a mace tun da ba a san halin da suke ciki ba kawo yanzu.
BBC Hausa: To yaya adadin waɗanda suka tsira kuma fa?
Ibrahim Ahmad Inga: Saboda yanayin yadda abin ya faru babu adadin yawan mutanen da suka shiga kwale-kwalen. Sai dai yawan waɗanda aka ga gawarwakinsu da kuma waɗanda ba a gani ba.
BBC Hausa: Mene ne ake tunanin ya janyo kifewar wannan kwale-kwale?
Ibrahim Ahmad Inga: To abu biyu ne dai. Na farko akwai maganar yawan jama'a a cikin kwale-kwalen saboda akwai firgici da tashin hankali da suka samu kansu a ciki.
Sannan kuma mai yiwuwa kwale-kwalen ya tsufa kuma jama'a sun masa yawa. To zai yi wahala a iya samun wani kyakkyawan sakamako saboda halin da aka samu kai.
BBC Hausa: Wane irin ta'adi ƴan bindigar suka yi a harin da suka kai ƙauyen mutanen?
Ibrahim Ahmad Inga: Wannan ya zarce hurumina tun da ni ba jami'in tsaro ba ne. Idan kuna son ƙarin bayani wannan jami'an tsaro ne za su yi ko kuma kwamishinan ƙananan hukumomi da tsaron cikin gida, suke da hurumin yin bayani a kan wannan.
BBC Hausa: Wane ƙarin bayani za ka yi a kan aikin ceton da ake yi na waɗanda ba a ga gawarwakinsu ba?
Ibrahim Ahmad Inga: Eh, ana nan ana kan nemo su a cikin ruwan.
BBC Hausa: Akwai wasu bayanai da ke cewa waɗanda suka rasa rayukan nasu sun kai 20, me za ku ce kan waɗannan rahotanni?
Ibrahim Ahmad Inga: To wani lokacin a kan samu labari marar sahihanci, in ka bi shi kuma ba shi da tushe.
BBC Hausa: A ina ne taƙamaimai jirgin ruwan ya kife, a wane kogi ne?
Ibrahim Ahmad Inga: A wannan rafin ne da ake cewa River Kaduna (Kogin Kaduna), wanda shi aka yi wa madatsa aka yi Shiroro Dam.