Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku tare da Usman Isa Taliyawa Gombe
Malamin addinin Musuluncin nan na Gombe Sheikh Usman Isa Taliyawa ya ce su suka soma kafa Fitiyanul Islam a Kano zuwa Gombe, karkashin jagorancin Modi Salga da Aliyi Alkali.
Sheikh Usman Taliyawa wanda ya shafe tsawon shekaru yana koyarwa da da'awa ya ce ba shi da wani buri a yanzu ganin ya rabu da duniya cikin imani da rufin asiri.
Malamin wanda shi ne mataimakin Bala Lau shugaban kungiyar Izala ya shaida haka ne a shirin Ku San Malamanku na BBC.
Rayuwar Malam Usman
An haife Sheikh Usman Taliya a wani gari da ke arewacin Kumo da ke Gombe. Ɗan asalin wani yankin da ake kira Taliyawa kuma anan ya soma karatunsa a gidan wani limaminsu Malam Muhammad.
Bayan ya sauke AlKur'ani sai ya koma Kumo a 1962 ya rinka wasu karatuttukan litattafai har na tsawon shekara biyu. Kana daga bisani a 1963 ya koma unguwar Yakasai da ke Kano ya ci gaba da karatunsa.
A 1974 ya samu aikin koyarwa a wata makaranta a Kasheren Gombe a mastayin malamin Arabiya. Haka abubuwa suka rinƙa sauyawa na rayuwa da aiki.
Sai dai a 1978 ya sake komawa Kano domin ƙaro ilimi inda ya yi difloma a fanin shari'a wanda ya kammala a 1981. Daga nan ya koma aikin kotu a matsayin rajistira. Amma bai jima ba ya ajiye aiki da kafa ta shi makarantar.
Sanna ya bayyana yada rayuwarsa ta kasance cikin aminci da malaman da suka koyar da shi a unguwar Kabara ta Kano.
'Na ji dadin karatuna a Kano'
Malam Usman ya ce akwai bambanci sosai a yanayin dalibcin Kano da wasu yankunan saboda a Kano ana yiwa dalibi hidima na samun saukin rayuwa. Shiyasa a zamaninsu suka fi son tafiya Kano karatu.
Ya kuma shaida yadda suka rinka fuskantar kalubale da dama musamman lokacin azumi da wajen tsaftar jiki, amma kuma komai daga baya ya zama tarihi a garesu.
"A lokacinmu litattafan da ake karatawa sun ɗan bambanta da na yanzu, saboda akwai litattafai da dama da a lokacinmu ba a san da su ba.
"Sai dai ci gaban zamani da yada aka rinƙa aika dalibai kasashe irinsu Misra da Sudan da sauran kasashen Larabawa suna karatu. Wannan ya taimaka mana wajen sake samun sani da rungumar wasu litattafan."
Ya ce a zamanin baya duk wata fatawa da za ayi a fikihu ake yinta amma daga baya an samu yalwantar abubuwan kamar su hadisai.
"A shekarun baya an rinka samu masu fitowa suna sukar fikihu suna masa kallon kamar ra'ayi ne ba a cikin hadisi ko Kurani aka dauko su ba. Amma sannu a hankali mutane sun fahimci cewa ba hakan abubuwa suke ba".
Gwagwarmaya
Malamin ya ce kafin zuwan Izala su suka kafa fitiyanul Islam a Gombe karkashin Modi Salga da Aliyu Alkali su suka kasance Jagora. Zuwansa Hajji na farko 1978 sunyi koyi da tafiyar da kungiyoyi da dama.
Sannan da Izala ta zo nan ma sai aka ci gaba da tafiya a dungule a cewar Malamin. Amma sannu a hankali kuma sai rabuwa tazo da fari kamar babu dadi amma daga baya sun ga fa'idar hakan wajen bunkasar su.
Abubuwan da ke faranta masa rai, shi ne ganin kusan duk rayuwarsa ta dogara ne kan karantarwar AlKur'ani da koyarwar addinin Musulunci.
Abinci da Iyali
Ya ce yana son cin tuwo da kunu, amma yanzu da shekaru suka zo yafi son shan shayi.
Yana da mata hudu da yara 31, maza 16 da mata 15.
Babban Burinsa shi ne ya mutu kan imani da rufin asiri da fatan canji kan abubuwan da yake koyarwa.