Ku San malamanku tare da Sheikh Muhammad Suru

An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon hira da Sheikh Ahmad Kanoma:

Fitaccen malamin addinin musuluncin nan na Najeriya Sheikh Muhammad Bin Abdalah Suru, ya ce wani mafarki da ya taɓa yi ne ya sa shi rungumar ɗariƙar Tijjaniyya duk da cewa mutane da dama sun ba shi shawarar ya karɓe ta.

''Karɓar ɗarikar Shehu Tijjani a garin Suleja na daga cikin ni'imar da ubangiji ya mini, domin akwai wata muƙabala da aka yi a kan ɗarika kuma Allah ya bani gagarumar nasara, to a wannan lokaci sai wani malami ya bani shawarar ya kamata in karɓi ɗariƙa, ya yi ta min nasiha amma ni ban amsa ba'' in ji shi.

Ya ci gaba da cewa ''A wannan lokaci sai bayan na koma gida na yi wani mafarki, inda a ciki na gan shi mun je taro wani wuri, ba zan iya gane wurin ba, amma dai ga shi an saukar da mu wani sabon gida an gama sama da ƙasa, ba ɗakin da yake da shimfiɗa, kowa yana ta gudu yana kama ɗaki, sai nima na faɗa wani ɗaki da aka cika shi da shimfiɗa, sai nima na ce na samu nawa ɗakin, sai wasu suka shigo suka ce ai wannan ɗakin Shehu Ibrahim ne, sai na farka ranar Laraba wayewar garin ranar Alhamis wannan abun ya faru, a ranar ne kuma na karɓi wuridin Shehu Tijjani''.

Ya ce tun daga wancan lokaci har zuwa yanzu yake yin ɗarika, kuma ya samu rabo iri-iri sakamakon wannan wuridi, domin babu wani malami da zai zauna a gabansa ba tare da Allah ya sanya shaƙuwa a tsakaninsu ba.

Tarihin rayuwarsa

Malamin ya ce ainihin sunansa shi ne Muhammad Bin Abdullahi, babban limamin masallacin tunawa da Alhaji Muhammadu Sanusi Ɗantata da ke tsakiyar babban birnin Najerya Abuja.

An haife shi ne a garin Suru, a wancan lokaci jihar Sokoto, a shekara ta 1381 bayan Hijira, dai-dai da shekarar 1962 Miladiyya.

Ya ce ya tashi ne a hannun ƙanin mahaifinsa wanda shi ma babban malami ne, kuma ya yi makarantu da dama, kama daga kan wacce ya yi a garin Gafadi, inda ya yi saukar alƙur'ani.

Ya ce ya shafe shekara biyu tare da shi yana karatu da neman na kai, kafin daga bisani haɗarin mota ya rutsa da su, a lokacin ne ƙanin mahaifin nasa ya rasu.

Ya ce daga nan ya koma hannun wasu malamai daban-daban har zuwa lokacin da ya fara fita garuruwa irin su Sokoo, inda ya karanci Ƙawa'idi da Fiƙihu da su Ishmawi da Izziyya da Askari da dai sauransu.

Kana a ɓangaren Lugga ma ya karanci manyan littattafai irinsu Zuhudu, da Badamasi da Albudda da Ishiriniyya da Muƙamatul Hariri a wajen malamai daban-daban, har zuwa lokacin Shagari, inda ya koma Suleja da sunan kasuwanci.

''A nan Suleja ɗin ne inda nake kasuwanci nake zuwa masallacin malamina limamin Malam Isyaku Turaki, limamin masallacin Juma'a na Turaki, wanda shine malamin da ya nemi in shiga Tijjaniyya ya nemi in dawo da iyalina nan, ya bani gidan da zan zauna''. in ji shi.

Abun da ba zai manta da shi ba

A cewar malamin babban abun baƙin cikin da ya same shi shine lokacin da ya samu labarin rasuwar Khalifa Shehu Tijjani Inyass.

''A lokacin har ina tunanin idan Shehu ba ya duniya idan na je Kaulaha na san ba ya duniya wani hali zan samu kaina ?, ko kuma in je kabarinsa in san cewa shine nan, wani irin yanayi zan samu kaina ?''

''Har ina faɗa idan na je taro a baya cewa idan Allah ya kawo ajalin Shehu ni ya ɗauki rayuwata a ƙyale ta shi, domin shi ya fini amfani ga jama'a, sannan idan ni na tafi zai yi mun addu'a'' in ji Sheikh Muhamad Suru.

Surar da ta fi ba shi wahala

Malamin ya ce surar da ya jima yana shan wahala kafin ya iya ta ita ce Walfajir, domin ya shafe tsawon lokaci yana ƙoƙarin ya ga ya haddace ta.

''To amma daga baya sai ya zamana kullum ina karantata a Sallah har yanzu da yake Allah ya sauƙaƙe abun, ta ba ni wahala sosai.

Iyali da buri

Ya ce yana da ƴaƴa 2 da jikoki da dama, domin dama ya jima yana roƙon ubangiji ya ba shi ƴaƴa da yawa.

Ya ce babban burinsa a yanzu shine Allah ya ba shi ikon gina katafariyar makaranta ta zama markazi, inda ko an ba da hutu za a samu ɗalibai masu ɗumin zuwa da za su rika karatu a cikinta''.

Burina shine kullum a riƙa koyar da ɗalibai ilimin addini da sauran darussa da suka shafi addini a cikinta'' in ji malamin.