Hotunan Afirka na mako: Daga ranar 18 zuwa 24 ga watan Maris 2022

An wallafa

Ga kayatattun hotunan na wannan makon daga sassan Afirka da ma wasu wuraren:

Short presentational grey line
A woman mixing a drink in Adjame, Abidjan, Ivory Coast - Sunday 20 March 2022

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Lahadi a Abidjan babban birnin Ivory Coast, wata mata ke hada shayi
The Real Boys train in a dance studio in Abidjan, Ivory Coast - Saturday 19 March 2022

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A nan kuma wasu yan rawa ne na kungiyar Real Boys 'yan kasar Ivory Coast ke rawa ranar Asabar a birnin.
Puppets backstage at the Carthage International Puppet Arts Festival in Tunis, Tunisia - Tuesday 22 March 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A nan kuwa ana kokarin shigo da mutum-mutumi cikin wani daki a babban birnin Tunis a ranar Talata...
A child looking at a puppet during he Carthage International Puppet Arts Festival in Tunis, Tunisia - Saturday 19 March 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A birnin ake gudanar da babban bikin nuna mutum-mutumi na duniya mai suna Carthage International Puppet Arts Festival.
A visitor poses for a photo with long-legged clowns at the Carthage Puppet Arts Festival in Tunis, Tunisia - Saturday 19 March 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An dakatar da bikin tsawon shekara biyu sakamakon annobar korona.
Classic cars taking part in the International Desert Palaces Festival in Tataouine, Tunisia - Wednesday 23 March 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A nan kuwa wani taro aka yi ranar Laraba a Tataouine da ke kudancin Tunisiya, an yi jerin gwanon motoci irin na da.
A woman carrying dried grass seen on the streets of Harar, Ethiopia - Saturday 19 March 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A nan kuwa wani mai daukar hoto ne ya dauki hoton wani layi da ake hada-hada a Harar da ke gabashin Ethiopia ranar Asabar.
A man sits next to two wheelbarrows on a pavement in Harar, Ethiopia - Saturday 19 March 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nan wani mutum ne ke hutawa a layin.
Two cyclists race in the mountains above Somerset West, Cape Town, South Africa - Monday 21 March 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mahaya kekuna sun yi gasar tseren kekuna mai taken Epic ta tsawon kilo mita 60 a birnin Cape Town da ke Afrika ta Kudu ranar Litinin.
People picking tea at a plantation near Limuru, Kenya - Thursday 24 March 2022

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Nan kuma wasu manoma ganyen shayi ne ke aiki a wata gona kusa da garin Limuru da ke Kenya a ranar Alhamis.
An orphaned baby elephant covers itself with soil at the David Sheldrick Wildlife Trust elephant orphanage near Nairobi, Kenya - Sunday 20 March 2022

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Nan kuwa wata karamar giwa ce ta rufe kanta da kasa a wani gidan dabbobi marayu da ke kusa da Nairobi babban birnin Kenya a ranar Lahadi.
People pictured on the banks of the River Loya, DR Congo - Saturday 19 March 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kafin ranar, aka dauki hoton wasu mutane na zaune a bakin gabar Kogin Loya a yankin gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo inda yan tawaye suka yi sansani.
Supporters hold fans that have the face of CAR President Faustin Archange Touadera at a rally in Bangui, CAR - Friday 18 March 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A nan kuma, wadanda suka yi gangamin siyasa don nuna goyon baya ga shugaban Afrika ta Tsakiya ne a Bangui babban birnin kasar ke hutawa a ranar Juma'a.
Two bodybuilders at the Ashoor Classic championship in Tripoli, Libya - Saturday 19 March 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Washe gari, wasu masu motsa jiki ne nan suke nuna kyautar da suka ci a gasar Ashoor a Tripolis, babban birnin Libya.
Liberian athlete Ebony Morrison jumping over a hurdle at the he World Athletics Indoor Championships in Belgrade, Serbia - Saturday 19 March 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Haka kuma a ranar Asabar din, wata yar kasar Laberiya Ebony Morrison ke gudun fanfalaki a zagayen kusa da karshe na gasar tseren mita 60 ta duniya a Belgrade.
Ronald Ssegawa, 22, shows two fingers he partially lost after he was allegedly tortured in Kampala, Uganda - Monday 21 March 2022

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A nan kuma wani dan bangaren adawa dan kasar Uganda mai shekara 22 ke nuna wani bangare na yatsunsa biyu da ya rasa, inda ya zargi jami'ai da gallaza masa har ya rasa wani sashen yatsun nasa. Hukumar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta fitar da wani rahoto inda take Allah wadai da gwamnati kan gaza daukar mataki kan irin wannan keta haddi.
A roadside vendor in Lagos recharges his clients' smartphone in Lagos, Nigeria - Tuesday 22 March 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Nan kuma wani mai shagon caji ne a gefen hanya a Lagos ke cajin wayoyin salula ranar Talata. Rashin wutar lantarki ba sabon abu ba ne a Najeriya.
People looking at the scene of a fire in Apongbon market under Eko Bridge in Lagos, Nigeria - Wednesday 23 March 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A nan kuma, mutane ke kallon inda gobara ke ci a wata kasuwa da ke karkashin daya daga cikin manyan gadoji a Lagos washe gari.
Firefighters on Eko Bridge, Lagos, Nigeria - Wednesday 23 March 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Gobarar ta tankwara gadar Eko, yan kwana-kwana na kokarin kashe ta.
A smiling woman carrying aid supplies in Niamey, Niger - Wednesday 23 March 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A nan kuma wata mata ce aka dauki hotonta a Niamey babban birnin Niger na dauke da kayan abinci da kasar Turkiya ta raba kafin shigar watan azumi.
A chapati chef in Kigali, Rwanda - Wednesday 23 March 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A nan kuma wani mai aiki a gidan abinci ke gasa gurasa a gidan abincinsa a Kigali babban birnin Rwanda, ranar Laraba.

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka