'Akwai jituwa tsakanina da Tambuwal da Saraki kan takarar shugaban ƙasa'

An wallafa

Wasu da ke neman takarar shugabancin Najeriya a karkashin Jam`iyyar PDP daga arewacin Najeriyar sun ce suna ci gaba da tuntuɓar juna da nufin mara wa guda daga cikinsu baya.

A makon da ya wuce ne Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da tsohon shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki, suka ziyarci Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad inda suka tattauna a kan hanyoyin daidatawa da juna.

Jam`iyyar ta PDP dai ba ta ce komai ba kan yankin da za ta bai wa takarar shugaban kasa.

Amma a yayin hira da BBC, Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ya ce tuntubar da suke yi ta yi nisa, kuma idan da so samu ne, arewa ce ya kamata a kebe wa takarar shugaban kasa.

Ya bayyana cewa tsakaninsa da Bukola Saraki da Aminu Waziri Tambuwal akwai jituwa sosai dangane da wannan lamari kuma tattaunawarsu ta yi nisa.

"Wannan takara ba muna yi ba ne saboda kanmu, muna yi ne saboda ƙasa da kuma arewa da muke wakilta da Najeriya, kada mu yi wani abin da zai kawo mana akasi shi ya sa muka ce ya kamata mu fara tattaunawa mu ga mun samu matsaya," in ji Gwamna Bala.

Gwamnan na Jihar Bauchi ya ce a kwanakin baya sun yi bincike domin gano dalilin da ya sa suka faɗi zaɓe a 2019 inda ya ce sun gano abubuwa da yawa.

Ya bayyana cewa daya daga cikin abubuwan da suka sa suka fadi zaɓe akwai rashin haɗin kai ganin cewa mutane da dama sun fito takara yawancinsu daga arewa.

Gwamnan ya ce a yanzu wannan tattaunawa sun fara ne su uku kuma suna sa ran faɗaɗa ta, ta hanyar tattaunawa da sauran masu sha'awar tsayawa takarar.

Ya kuma soki tsarin da ake kai na karɓa-karɓa a Jam'iyyar PDP inda ya ce "Ba daidai ba ne a ce PDP ta shekara 16 tana riƙe da shugabancin ƙasa kuma arewa ta yi shekara biyu ne kacal a cikin 16 kuma a ce za a rufe arewa saboda Buhari yana shugaban ƙasa, Buhari a Jam'iyyar APC yake ba a PDP yake ba," in ji shi.