Wasu 'yan Najeriya sun ce 'yi wa Ukraine yaki ya fi zama a nan'

    • Marubuci, Soraya Ali
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa

Yayin da Rasha ta kaddamar da mamayarta a Ukraine a watan jiya, abin ya fusata wani matashi dan Najeriya Ottah Abraham mai shekara 27.

Ya daki wayar shi ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: "Ina son shiga tawagar da ke yaki."

Yana zaune ne a wani karamin gida a Legas da ke da nisan kilo mita 8,700 zuwa inda ake yaƙin.

Dalibin da ya karanci ilimin nazarin halittar dan Adam, daya ne daga cikin ɗaruruwan 'yan Afrika da kasashe irinsu Najeriya da Kenya da Senegal da Afrika Ta Kudu da kuma Aljeriya, wadanda suka ce suna da fatan shiga cikin yakin Rasha da Ukraine, wani mataki da suke son dauka domin kauce wa halin matsin rayuwa da matasan nahiyar ke ciki.

"Mun sani sarai cewa yaki ne, ba wasan yara ba," kamar yadda ya shaida wa BBC. "Amma zama sojan yaki a Ukraine zai fi dadi kan zama a nan.

"Watakila a bar ni na ci gaba da zama a can in yakin ya kare. Bugu da kari, zan zama gwarzo kuma babu wanda zai yi musun cewa na yaƙi maƙiya."

Wasu mayakan sa-kai daga fadin duniya sun amsa kiran Shugaba Volodmyr Zelensky na cewa suna neman mayaka 'yan kasar waje 'su yi wa Ukraine fada'.

Gwamnatin ta dan saki bizarta ana bayarwa ga wadanda suke bukata kuma za ta bayar da kayan aiki da albashi ga masu fasfo din kasar da ke da horon zama sojoji. Amma babu tabbacin cewa za a kyale 'yan kasashen waje su ci gaba da zama a kasar bayan gama yakin.

Kereti Usoroh, wani dan Najeriya da ke zaune a Abuja babban birnin kasar, ya ce zama dan kasar Ukraine ko kuma matsalar kudi ba sa cikin abubuwan da za su sanya shi ya je yakin.

"Ina rayuwa mai kyau a nan. In ina son zuwa Turai ya kamata na bi ta hanyar ilimi ba ta hanyar yaki ba," in ji lauyan mai shekara 29.

"Wannan magana ce ta yakar azzalumi, rashin adalci kan mutum daya daidai yake da kan kowa."

Ba a murna da sojojin haya

Sai dai ofishin jakadancin Ukraine a Najeriya ya yi irin abin da takwarorinsa na sauran kasashe suka yi, sun janye bukatarsu ta neman 'yan kasashen waje su shigar musu yakin.

"Najeriya ba ta goyi bayan amfani da sojojin haya a ko'ina a duniya kuma ba za ta yarda da da daukar 'yan kasarta ba a matsayin sojojin haya," kamar yadda ministan harkokin wajen Najeriya ya bayyana a wata sanarwa.

Bohdan Soltys, wani jami'i ne a ofishin jakadancin Najeriya, ya ce ba za su biya 'yan Afrika da za su yi masu yaki ba - kuma ko wanene zai je Ukraine sai ya biya kudin jirginsa na zuwa.

"Akwai banbanci tsakanin mayakan sa-kai da sojojin haya," ya shaida wa BBC.

Daga baya ya yi bayanin cewa an ba shi umarnin mayar da duk wani mayakin sa-kai da yaje ofishin.

Senegal ta yi wa 'yan kasarta gargadi kan shiga yakin, tare da neman wakilin Ukraine a kasar ya goge bayanansa da ya wallafa a Facebook na neman 'yan sa-kai daga Senegal, inda ta kira hakan haramtaccen abu a doka wanda zai iya janyo a hukunta mutum."

Ministan harkokin wajen Algeria ya yi irin wannan gargadin da ofishin jakadancin Ukraine a kasarsa.

"Kasata ta ce bai kamata in tafi ba. Na yi kokarin rubuta wasika ga ma'aikatar harkokin wajen. Amma ba ta amsa mani ba, amma zan kara gwadawa," in ji Belhadj Hani Amir wani matashi dan shekara 28 ya shaida wa BBC.

"Ina son zuwa Ukraine amma ina fatan wannan yakin ya zo karshe nan ba da jimawa ba."

Wakiliyar Ukraine a Afrika Ta Kudu da Mozambique da Botswana Liubov Abravitova ta shaida wa BBC mutane da dama daga kudancin Afrika na ta hankoron shiga wannan yaki ko kuma su yi aiki da kungiyoyin ba da agaji - amma ba za ta iya komai ba kan bukatunsu, har sai ta ji daga bakin gwamnatocinsu. Afrika na da doka mai tsauri game da sojojin haya.

A takaice, shafin daukar sojojin sa-kai na Ukraine ba yi bayanin cewa bukatar ta su ta game da 'yan kasashen Afrika ba.

' 'Yan uwan Rasha'

Kasashen Aljeriya da Senegal da kuma Afrika Ta Kudu na cikin kasashe 17 daga cikin 54 da suka ki jefa kuri'ar watsi da mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine da Majalisar Dinkin Duniya, suna gudun kada su ba ta wa Rasha.

Ba wani abu ba ne wannan a wajen Rasha samun goyon bayan 'yan Afrika. Idan aka yi bayanin tasirin da take da shi a nahiyar ta fuskar soji, tana taimakawa Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya da Libya da Mali da kuma Sudan a yakin da take yi da masu ikrarin jihadi.

Wani bidiyo ya nuna sojojin CAR na son haduwa da 'yan uwansu na Rasha' yana nan ya karade shafukan sa da zumunta, duk da cewa BBC ba za ta ita tabbatar da ingancin daga ina ya fito ba, kuma jami'an gwamnati ba su bayar da amsa ba kan neman sanin da muka aika musu.

A Juma'ar da ta gabata ne, ministan harkokin tsaron Rasha Sergei Shoigu ya ce "sama da mayakan sa-kai 16,000" ne daga Gabas Ta Tsakiya suka mika bukatarsu ta yaki tare da Rasha - babu dai tabbaci ko hakan ya hada da 'yan arewacin Afrika.

Watsa kasa a ido

Ga wasu mutanen kamar su David Osagie Adeleke daga jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya wannan ba karamin watsa kasa a ido ba ne.

Dan shekara 21 da ya yi aiki da hukumar ba da agajin gaggawa ta Red Cross, ya shirya tsaf ya shiga yaki a matsayin sojin sa-kai na amutu ko a yi rai, kuma ya tattara duk wasu takardu da ya kamata ace yana da su har da takardar cancantarsa.

"Na wuce ofishin 'yan sanda kai tsaye domin karbo takarduna, "in ji shi, inda suka yi bayanin ban taba aikata wani laifi ba.

"Ba karamin bacin rai na shiga ba, bayan na ji ofishin jakadancinsu yace ya fasa daukar 'yan Afrika."

An kuma dawo masa da sakon email da ya aika wa ofishin jakadancin Ukraine, Yanzu yana kallon zabi na gaba shi ne zuwa kan iyakar kasar.

"An yi mini jarrabawa a ofishin jakadancin Poland da ke Najeriya," in ji shi.

Nkem Nduche, wanda shi ma muka gani a ofishin jakadancin Ukraine, yana da cikakkiyar masaniya kan abin da yake faruwa a kasar tare da kyakkyawan fatan zai je inda yake so.

Ya dauki dogon lokaci a Rasha a matsayin wani matashin tauraro, yana da katin dan kasa biyu kuma y shiga makarantar sojin Rasha - amma an taba tsare shi a gidan yari na wani dan lokaci inda aka zarge shi da leken asiri bayan ya kai wata ziyara ofishin jakadancin Amurka.

Yace ya tsere daga kasar ne shekara bakwai baya, ta cikin Ukraine - kuma a yanzu zai so ya yaki Rasha sai dai bukatarsa ba ta amsu ba.

"Na so na je a radin kaina amma gwamnatin Najeriya ta ce ba za mu iya ba... zan yi biyayya ga kasata," ya shaida wa BBC.