Tarayyar Turai za ta yi ganawa kan tsaro da karbar Ukraine

An wallafa

Yayin da mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine ta shiga mako na biyu, shugabannin kungiyar Tarayyar Turai za su yi ganawa ta kwana biyu domin tattauna sabbin takunkumai a kan Rasha, da duba yiwuwar shigar da Ukraine kungiyar tare kuma da nazari a kan manufar tsaro ta bai-daya.

Shugabannin kungiyar ta Tarayyar Turai, EU, a yayin wannan taro na kwana biyu za su yi duba tare da kyakkyawan nazari kan samar da manufar tsaro ta bai-daya, inda za su duba karin kudaden da ya kamata su yi ta kara karfafa tsaro, tare da inganta tsarin tafiyar da karfinsu a fannin tsaro.

Sai dai duk da yadda Shugaba Eammanuel Macron na Faransa yake son ganin wadannan tsare-tsare da manufa sun samu karbuwa, ana ganin ba lalle ba ne, wani tartibin tsari ko tsare-tsare su biyo ganawar ta shugabannin na EU.

Sannan babu batun neman yin gogayya da kungiyar kawance ta Nato.

Batun yakin Rasha da Ukraine ko ba komai ya tayar da kungiyar ta Tarayyar Turai tsaye, inda take kara mayar da hankalinta wajen hadin kai.

To amma kuma irin munanan abubuwan da ake gani a sanadiyyar yakin da Rasha take yi da Ukraine na sosa rai da tayar da hankali.

Musamman harin baya-bayan nan da sojin Rasha suka kai kan wani asibiti a Mariupol, harin da ya sa Shugaba Volodymyr Zelensky, ya kara kira ga shugabannin na Turai da su kara tashi tsaye wajen taimaka wa kasarsa.

Alƙaluma sun nuna cewa harin na asibitin yara ya yi sanadiyyar mutuwar mutum akalla 17 tare da lalata wurin haihuwa da saurn muhimman wurare a asibtin.

Ana ganin shugabannin na Turai za su yi zazzafar muhawara kan ko a hanzarta batun shigar da Ukraine cikin kungiyar.

Haka kuma taron zai yi kyakkyawan nazari game da tashin farashin makamashi da kuma yadda kungiyar za ta yaye kanta daga dogaro da ta yi sosai ga mai da iskar gas ta Rasha.