Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Phillips, ten Hag, Pochettino, Tuchel, Rudiger, Sanches

An wallafa

Manchester United ta fara nuna sha'awarta kan kocin Ajax Erik ten Hag a laluben da kungiyar ta fara na sabon koci, kuma ana ganin kocin dan Holland mai shekara 52, zai so ya yi magana da kungiyar ta Old Trafford idan har suka bukace shi. (Sky Sports News)

Yayin da ake wannan shi kuwa kocin Paris St-Germain Mauricio Pochettino yana son ya samu tabbaci ne daga Manchester United din cewa lallai shi suke so, kafin dan Argentinar ya yarda ya karbi aikin horas da kungiyar. (Mail)

Game da rigingimu da ake samu a bayan fage a tsakanin 'yan wasa kuwa an ce darektan 'yan wasa na kungiyar ta Manchester United Darren Fletcher shi ne ke shiga tsakani a bayan fage saboda sabanin da ake samu a tsakanin 'yan wasan. (Sun)

Mai kungiyar Chelsea Roman Abramovich wanda gwamnatin Birtaniya ta dauki matakin sanya masa takunkumi saboda rikicin da kasarsa, Rasha ke yi da Ukaine ya bai wa Manchester United damar daukar kociyan Chelsea Thomas Tuchel, in ji tsohon dan wasan Liverpool da Ingila Jamie Carragher. (Telegraph - subscription required)

Chelsea tana da 'yan wasa tara wadanda kwantiraginsu zai kare a bazara kuma za su iya barin kungiyar a kyauta sakamakon takunkumin da Birtaniya ta sanya wa Abramovich. (Metro)

Dan bayan Jamus Antonio Rudiger ya shirya tsaf domin barin kungiyar idan kwantiraginsa ya kare a bazara, saboda duk kokarin da kungiyar ta yi na ganin ta kulla sabuwar yarjejeniya da shi hakarta ba ta cimma ruwa ba. (Sky Sports News, via Star)

Ita kuwa Juventus na duba yuwuwar sayen dan gaban Chelsea ne dan Amurka Christian Pulisic, mai shekara 23. (Gazetta dello Sport - in Italian)

Watakila Tottenham ta bayar da dan bayanta Cameron Carter-Vickers, mai sheakara 24, ko dan tsakiya Harry Winks, mai shekara 26, a yarjejeniyar da suke yi ta sayen dan bayan Ingila Tino Livramento, mai shekara 19, daga Southampton. (Football Insider)

Kungiyoyin Italiya AC Milan da Juventus na nazarin neman sayen dan wasan tsakiya na Lille da Portugal Renato Sanches, mai shekara 24. (Goal)

Valencia na son ci gaba da rike dana wasan gaba na gefe na Tottenham Bryan Gil, da ke zaman aro, a kaka ta gaba, kuma kila kungiyar ta nemi kara wa dan Sifaniyar shekara daya ma. (Star)

Arsenal na nuna alamun sha'awar sayen matashin dan wasan tsakiya na Aston Villa kuma dan tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 19, Carney Chukwuemeka, mai shekara 18. (Evening Standard)

Shi kuwa kocin Roma Jose Mourinho yana sha'awar sayen dan wasan tsakiya na Arsenal da Switzerland Granit Xhaka, mai shekara 29, a lokacin bazara. (Calciomercato)

Ya kamata Kylian Mbappe, ya koma Liverpool ko Manchester City, in ji tsohon dan wasan baya na gasar Premier Micah Richards. (Liverpool Echo)

Neymar, ya musanta rahotannin da ke cewa ya yi sa-in-sa da abokin wasansa a PSG dan Italiya Gianluigi Donnarumma, saboda fitar da su daga gasar Zakarun Turai da Real Madrid ta yi. (Mirror)

Dan gaban Argentina Paulo Dybala, mai shekara 28, na ganin Juventus za ta bar shi ya tafi a lokacin bazara. (Gazetta dello Sport - in Italian)

Manchester United na shirin fara tattaunawa da dan bayanta na Portugal Diogo Dalot domin kulla sabuwar yarjejeniya da shi, kasancewar saura wat 18 ya rage yanzu a kwantiraginsa. (Teamtalk)

Aston Villa na shirin sayen dan wasan tsakiya na Leeds, dan Ingila Kalvin Phillips, mai shekara 26. (Athletic - subscription needed)

Bisa ga dukkan alamu Brighton ce ke kan gaba a kokarin sayen dan gaban Blackburn Rovers Ben Brereton Diaz, inda Crystal Palace, Everton, Leeds United da kuma West Ham, duk suna son dan gaban na Chile mai shekara 22. (Teamtalk)