Chelsea ta ƙara danna kan Norwich kasar tebur

An wallafa

Chelsea ta casa Norwich da ke kasan teburin Premier yayin da Mason Mout ya ci guda ya kuma bayar aka ci daya lokacin da kungiyar ke tsaka da fuskantar matsala.

Magoya bayan da suka halarci gasar sun rika ihu suna kiran sunan Roman Abromavich sa'o'i bayan sanar da gwamnatin Birtaniya ta kakaba masa takunkumi.

A filin wasa, yan wasan Chelsea sun dauki matakin nuna damuwa da kan lamarin a lokacin da yake cika shekara 117 a tarihi, ta hanyar zira kwallo biyu a minti 15 da fara wasan.

Wannan ne wasa na hudu da Chelsea ta ci a jere a gasar Premier.

Trevoh Chalobah ne ya fara zira kwallo a raga a minti uku na fara wasan, sai Kai Havertz ya bai wa Mount ya ci kwallo ta biyu a wasan, ta takwas a kaka.

Bayan dawowa hutun rabin lokaci ne Norwich ta jefa kwallo daya ta hannun dan wasanta na gaba Teemu Pukki a bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan Chalobah ya taba wata kwallo da hannu.

Daf da za a kammala wasan ne Kante ya janyo wata kwallo ya kuma bai wa Kai ya ci.

Wannan nasara ta kara tabbatar da Chelsea a matsayi na uku ta kuma kara tura Norwich kasan teburi.