Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea: Takunkumin da Birtaniya ta saka wa Roman Abramovich ya hana shi sayar da Chelsea
Yunƙurin Roman Abramovich na sayar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ya tsaya cak sakamakon takunkumin da Birtaniya ta saka wa biloniyan ɗan ƙasar Rasha a matsayin martani ga matakin Rashar na mamaye Ukraine.
Attajirin ya saka Chelsea a kasuwa ne bayan bazaranar saka masa takunkumin daga majalisar wakilan Birtaniya.
Matakin da aka ɗauka na hana shi taɓa dukiyarsa, wanda ya haɗa da Chelsea, na nufin ƙungiyar ba za ta iya sayar da tikitin shiga kallon wasanninta ba.
An ɗauki matakin ne kuma saboda a hana Mista Abramovich samun kuɗi da ƙungiyar.
Gwamnati ta ba da wani lasisi na musamman ga ƙungiyar da zai ba ta damar ci gaba da buga wasanni, da biyan albashin ma'aikata, da kuma bai wa waɗanda suka riga suka sayi tikitin damar shiga kallon wasannin.
Kazalika, za a rufe shagon sayar da kayayyaki na kulob ɗin.
Gwamnati ta ce za ta sake duba wasu hanyoyi da za ta ba da ƙarin damar sayar da ƙungiyar.
Sai dai sharaɗin da aka saka kafin a ba da damar shi ne Abramovich - wanda ɗaya ne daga cikin manyan attajirai na kusa da Shugaban Rasha Vladimir Putin - bai samu wani kuɗi ba.
Tun farko ya ce za a yi amfani da ribar da aka samu ne bayan sayar da ƙungiyar wajen taimaka wa waɗanda yaƙi ya shafa.
Ya zuwa ranar Laraba, an samu mutum 20 da suka nuna sha'awar sayen Chelsea. Cikinsu har da wani ɗan kasuwar Birtaniya mai suna Nick Candy.
Sakatariyar al'adu da wasanni ta Birtaniya Nadine Dorries ta ce gwamnati "na da aniyar kare" kulob ɗin.
"Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa wani ɓangare ne na al'adunmu kuma dukiyar mutanenmu," a cewarta.
"Na san wannan lamari ya bijiro da rashin tabbas, amma gwamnati za ta yi aiki tare da hukumar lig da ƙungiyoyi don ci gaba da gudanar da wasanni yayin da takunkuman za su ci gaba da kasancewa kan waɗanda ake hari."
Me takunkumin ke nufi?
- Chelsea za ta iya biyan albashin ma'aikatanta, ciki har da 'yan wasa da kociyoyi
- Za su iya biyan kuɗaɗen tafiye-tafiye na zuwa buga wasanni da ba su wuce fan 20,000 ba a kowane wasa
- Za su iya biyan kuɗin ɗaukar nauyin buga wasanni a gida da ba su wuce fan 500,000 ba a kowane wasa
- Magoya baya da suka sayi tikitin shiga kallon wasa kafin 10 ga watan Maris za su iya shiga kallo
- Kafofin yaɗa labarai da ke da izinin haska wasannin ƙungiyar za su iya ci gaba da yin hakan