Poland ta yi tayin bayar da jirage don yakar Rasha

An wallafa

Poland ta ce a shirye take ta aika da dukkanin jiragenta na yaki kirar MiG-29 zuwa sansanin sojin sama na Amurka da ke Jamus, domin a yi amfani da su kyauta wajen yakar Rasha kan mamayar da ta yi wa Ukraine, sai dai Amurka ta ki yarda da tayin.

Ma'aikatar harkokin wajen Poland ta yi wannan sanarwa ne, bayan da jami'an Amurka da Birtaniya suka bayyana cewa za su tallafa wa Poland din idan har za ta bayar da jirgen ga Ukraine.

Rasha dai ta yi barazanar mayar da martani idan har NATO ta aika da jiragen sama na yaki zuwa Ukraine, kuma gwmnatin Poland na tsoron tunzura gwamnatin Rasha haka kawai, idan har ta aika da jirgen yakin kai tsaye zuwa Kyiv.

Wannan sanarwa wadda ta dauki hankalin kusan dukkanin masu ruwa da tsaki a yakin na Ukraine ta fito ne daga Ma'aikatar Harkokin Wajen Poland, inda gwamnatin kasar ta ce a shirye take ta mika dukkanin jiragen yakin nata samfurin Mig-29 kirar Rasha, ga Amurka, domin taimaka wa Ukraine yakar dakarun Rasha da suke mamayar ta.

Ma'aikatar Wajen ta Poland ta ce za ta kai jiragen saman na yaki kyauta, har zuwa sansanin sojin Amurkar da ke Ramstein a Jamus, ta kuma danka su a hannun Amurka domin amfani da su.

Sanarwar da gwamnatin Poland ta fitar ta kuma ce, Poland din ta bukaci Amurka da ta ba ta wasu jiragen saman na yaki, na hannu (ba sababbi ba) masu karfi da aiki kamar wadanda za ta bayar.

Ma'ikatar wajen ta Poland ta kuma ce tana rokon sauran kawaye na cikin NATO da suma su bayar da irin wadannan jirage kirar Rasha, MiG-29 ga Amurkar.

Sai dai kuma Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce, wannan shawarar da Poland ta yanke ta ba ta mamaki, inda kakakin Ma'aikatar Tsaron Amurkar, John Kirby, ya ce ga alama shawarar ba mai yuwuwa ba ce, hasali ma ta yi gaban kanta ne ta fitar da sanarwar domin ba ta yi tuntuba ba kafin ta bayyana hakan.

Ya ce batun tashin jiragen sama na yaki daga sansanin sojin Amurka zuwa sararin samaniyar Ukraine abu ne da zai tayar da hankali sosai ga kawancen NATO gaba daya.

Daman dai gwamnatin Polanda da ta Amurka na tattaunawa a kan ba wa Ukraine jiragen saman na yaki, amma kuma daman akwai babbar matsala dangane da batun, wadanda suka hada da ainahin yadda za a mika jiragen yakin ga Ukraine.

Da yake magana a kwamitin kula da harkokin waje na Majalisar Dattawan Amurka, shugaban kwamitin dan jam'iyyar Democrat Bob Menendez, ya bayyan fatana cewa za a mika jirgen ga Ukraine:

Ya ce, "Abu daya da muke ta jin magana a kai shi ne, neman shata yankin da jirgen sama ba za su ratsa ba, na fahimci kalubalen hakan, NATO da suran kasashe ba su so su shiga rikici da Rasha kai tsaye, to amma bai wa Yukireniyawa karfin yaki domin sararin samaniyarsu, don kuma su samu wani iko da samansu abu ne da ya dace karara.''

Gwamnatin Poland na dari-dari da irin martnin da Rasha za ta mayar, idan har ta bayar da jiragen kai tsaye ga Ukraine, abin da za ta kalla a matsayin wata tsokana.

A makon da ya gabata ne Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya bukaci kasashen Turai da su taimaka da jirgen saman a yaki kirar Rasha, domin agaza masa a yakin da ake yi saboda matukan jiragen sama 'yan Ukraine sun lakanci jiragen kirar Rasha.