Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Uganda: Hotunan masu wa'azin turmi da lasifikokinsu da suka mamaye titunan Kampala
- Marubuci, Daga Miriam Watsemba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Kampala, Uganda
- An wallafa
Da taimakon lasifika, muryar Kayemba Stephen ta mamaye hayaniya da kai kawon mutane da ke faruwa a wani titi a Kampala, babban birnin Uganda.
"Ka yarda da Yesu yau!" in ji mai wa'azin, wanda aka fi saninsa a titunan da suna Sulphur Teacher, yana mai yin kiran masu wucewa cikin karsashi kamar wanda ya yi amannar cewa duk mai wucewa yana sauraron abin da yake cewa ka'in da na'in.
Wasu kan wuce da sauri, wasu kan tsaya suna kallo, masu bin diddigi kuma kan biye masa suna ihun "hallelujah" da "amen" a matsayin amsawa addu'o'insa.
Abin da yake yi ɗin da shi da sauran masu wa'azi - ya zamo batun tattaunawa a birnin, a yayin da hukumomi ke gabatar da hanyoyin gyara birnin.
Auma Laura, wata mamba ta wannan tawaga, ta karɓi lasifikar, tana addu'a cikin salon sallamawa.
Muryar matar mai shekara 28 na rawa sosai a yayin da take addu'ar.
Kuma hakan ba ya karya gwiwarta, duk da yake ita ma'aikaciyar banki ce.
"Ina ganin kaina a matsayin wacce ke isar da saƙon ubangiji. Ina yi wa marasa lafiya addu'a kuma suna warkewa, don haka ba zan iya dainawa yanzu ba," ta gaya wa BBC.
"Uganda ta Ubangiji ce," kamar yadda masu wa'azin ke ayyanawa a yayin da wasu ke durƙusawa a gabansa don neman tubarraki.
Wasu kuma na matsawa gabansa don neman albarka.
Uganda ƙasa ce ta addini sosai kuma a watan da ya gabata an samu ce-ce-ku-ce a ƙasar bayan da wani babban jami'i a Kampla ya ce dole ne kiristoci masu yaɗa bushara da ke wa'azin turmi su bar ƙasar.
Daga baya ya ce an sauya kalamansa ne kuma shi bai shirya "yin ja in ja da Ubangiji ba". Amma yana son masu wa'azi su daina damun mutanen da ke wucewa a cikin ababen hawansu ko kuma amfani da lasifika ta yadda za su dinga damun jama'a.
Amma ga alama da wuya a hana wa'azin nan na kwararo-kwararo.
"Ina son kwararo, ina son jan hankalin mutane. Muna yin wannan wa'azi na turmi duk safiya tun 2 ga watan Janairu, kuma muna fatan ci gaba da yi har ƙarshen shekarar nan," in ji Janet Musisi, wacce ta haɗa wannan tawaga.
Wani injiniyan na'ura mai ƙwaƙwalwa Pius Eritu mai shekara 28, ya shafe shekara uku yana wa'azinsa mai take "jawo hankulan mutane".
Wasu mutanen ƙalilan suna da saurin tunzura, amma ya koyi kawar da kai daga abubuwa marasa dadin, ya ci gaba da abin da yake yi, a cewarsa.
Fasto Masasi Edson ya sha alwashin a wannan shekarar sai ya yi wa'azin turmi kullum.
Ya yi amannar cewa saƙonsa mai ƙarfi ne "amma ga waɗanda suka ƙi mayar da martanin a nan take, to a ƙalla mai wa'azi na gaba ya shirya musu".
Kuma tabbas za mu gabatar da mai wa'azi na gaba, ko da hukumomi sun ɗauki mataki.
Dukkan hotunan haƙƙin mallakar Miriam Watsemba ne