Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Karnunka: Ta yaya - kuma me ya sa - suka zama 'manyan abokanmu'?
- Marubuci, Daga Fernando Duarte
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
Dangantakarmu da karnuka dadaddiya ce.
Masu nazarin tarihi sun sanar da mu cewa sun gano cewa tun kusan shekaru 14,000 da suka gabata dan Adam ke binne karnuka kusa da masu su.
Sai dai an dade ana muhawara kan yadda dangantakar ta samo asali, duk da cewa karnuka ne dabbobin farko da 'yan Adam suka fara mayarwa dabbobin gida.
Tarihin asali
Akwai rassa biyu na muhawarar da ake yi kan asalin dangantaka tsakanin 'yan Adam da karnuka wadda aka ce ta samo asali tsakanin shekaru 15,000 zuwa 40,000 da suka wuce a Turai ko Asia.
Akwai masu hasashe cewa babu shiri dan Adam ya mayar da dabbar kerkeci ta wancan zamanin zama dabbobin gida. Ana hasashen cewa daga dabbar kerkeci aka samo karnukan farko.
Wasu kuma na cewa dabbar kerkeci ce ta mayar da kanta ta gida ta hanyar rabar kauyuka da garuruwan da dan Adam ke rayuwa domin roron kalacin da mutane ke jefar wa.
Daya daga cikin wadanda ke amanna da bayani na biyu shi ne Krishna Veeramah na jami'ar Brook University ta birnin New York.
"Wadancan kerkecin da ba su cika fada ba, su ne suka fi iya zama dabbobin gida," kamar yadda ya ce.
Pat Shipman, wadda tsohuwar farfesan tarihin ilimin dan Adam ne, ta ce dan Adam da kare sun kulla wata dangantaka mai karfi ne - wadda a da can babu irin wannan shakuwar.
"Idan muka tuna dukkan kere-keren da muka yi da kuma abubuwan da muka samar na ci gaban duniya, mayar da dabbobin dawa su zama na gida misali ne mai matukar ban al'ajabi," inji ta.
Tsohon farfesan ya kuma kara bayani cewa sannu a hankali 'yan Adam da karnuka sun gano amfanin zama tare - ga dan Adam, ya gane cewa kerkeci dabba ce mai kare shi daga hare-haren muggan dabbobin dawa, kuma kerkecin na taimaka ma sa wajen farautar manyan dabbobi.
Kamar yadda ilimin tarihin dan Adam ke cewa, kerkeci da karnuka sun zama tamkar 'ya'yan gidan dan Adam - da kuma wuraren da ake binne dan Adam, kuma akwai zane-zane a cikin dadaddun koguna da ke nuna dabbobin a matsayar abubuwan wasan dan Adam.
Mis Shipman ta kuma yi wani bayani cikin sabon littafinta mai suna Our Oldest Companions cewa dangantakarmu da karnuka yana cikin dalilan da dan Adam ya yi nasara a duniyar da yake rayuwa a wancan lokacin.
"Hadakar dan Adam da kerkeci ta sha gaban ta sauran dabbobi masu rayuwa tare a wancan zamanin."
Rainon halayya
James Serpell, wanda kwararre ne a fannin dangantakar dan Adam da dabbobi a Jami'ar Pennsylvania, ya ce bai ga illar hasashen da ake yi kan fa'idar mayar da kare ya zama dabbar gida.
Sai dai Serpell ya ce hasashen cewa dabbobin sun amince da dan Adam ne da kansu yafi zama gaskiya, bayanin da ya rubuta cikin wata mujalla mai suna Veterinary Science journal, wadda aka wallafa a watan Afrilun bara.
Ko zamanin kare ya zo daidai da na dan Adam ne?
Tarihin yadda kare ya zama dabbar gida tsoho ne matuka, wanda ya sa zai yi wuya mu iya sanin ainihin yadda lamarin ya faru. Saboda haka ne za a dade ba a san gaskiyar batun ba.
"Mun rika kallon kerkeci a matsayin abokan farauta ne," inji Pat Shipman.
"Abubuwan da muke bukata a wancan zamanin sun yi kama da abubuwan da kerkecin ma ke so."
James Serpell ya kuma yarda cewa kerkeci daa dan Adam "sun karbi juna sosai".
"Yawancin abubuwa game da mu da su suun kasance masu kamanceceniya matuka."