Neom: Da gaske Saudiyya za ta gina sabon birni na zamani a tsakiyar Hamada?

Art work shows a woman walking through a desert with technological projections

Asalin hoton, Neom.com

Bayanan hoto, Wani tallan sabon birnin na Neom na cewa birnin zai zama kamar wani wurin wasa ne
    • Marubuci, Daga Merlyn Thomas da Vibeke Venema
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa

Yashin gabar teku mai haskawa cikin duhu, shuka biliyoyin bishiyoyi a kasar da hamada ta mamaye, jiragen kasa masu lilo a sama, samar da wata amma na jabu, birnin da babu mota ko hayakin mota mai tsawon kilomita 100 a tsakiyar hamada.

Wadannan na cikin shirye-shiryen da Saudiyya ke da su na gina wani sabon birni wanda kasar za ta yi amfani da shi a matsayin turken komawa kan tafarkin kulawa da yanayi.

Sai dai anya wadannan abubuwa ne masu yiwuwa?

Neom shi ne sunan katafaren sabon birnin da Saudiyya ke shirin ginawa, wanda ta ce "tsarin biranen gobe ne da dan Adam zai gina ba tare da ya illata lafiyar rayuwar halittun duniya ba." Birni ne da za a kashe dala biliyan 500 wajen gina shi, wanda zai kasance karkashin wani shirin Saudiyya mai suna Vision 2030 da zai yaye ta daga dogaro da albarkatun man fetur - albarkatun da suka azurta kasar.

Girman birnin zai kai murabbu'in kilomita 26,500, wanda zai fi girman kasar Kuwait ko Isra'ila - kuma masana sun ce birnin Neom zai kasance cikin wani tsari na shari'a daban da na sauran kasar Saudiyya, wanda masu zuba jari ne za su samar da tsarin shari'arsa.

Ali Shihabi wani tsohon ma'aikacin banki ne kuma yana cikin masu bayar da shawara kan gina birnin Neom, ya ce sabon birnin zai kasance mai tsawon kilomita 170 da aka lakaba wa suna The Line, wanda ya ce a mike sambal babu kwana za a gina shi a cikin hamada.

Sai dai idan ana tunanin wannan abu ne mai wuyar yi, Shihabi ya bayyana cewa za a gina birnin The Line ne daki-daki. "Jama'a na cewa wannan wani mahaukacin aiki ne da zai zuke biliyoyin dalli, amma sannu a hankali cikin tsari za a gina shi, daidai da bukatar da ake da ita," in ji shi.

Bayan an kammala gina shi, The Line zai sami jiragen kasa masu matukar gudu, inda dukkan wurare "ana iya zuwa cikin kasa da minti 20", in ji masu tsara birnin.

Baya ga wannan, yankin na Neom zai zama yana da wani birni mai suna Oxagon, wanda za a gina a saman ruwa, wanda fadinsa zai kai kilomita 7 - wanda zai kasance birni irinsa mafi girma a duniya. Shugaban Neom, Nadhmi al-Nasr ya ce "masana'antun farko za su fara kafuwa a tashar jirgin ruwan birnin a 2022."

Oxagon - a floating city

Asalin hoton, Neom.com

Bayanan hoto, Birnin Oxagon da zai kasance yana cikin teku na cikin wuraren da za a gina a yankin na Neom

A dan nesa da wannan wurin amma a gabar tekun Bahar ul Ahmar, za a gina wani yankin kulawa da halittun ruwa mafi girma a duniya. Shafin Neom na intanet, wanda a wasu lokutan ke kama da wasu hikayoyin da aka rubuta na tafiye-tafiye zuwa taurari, na ikirarin cewa za a kammala kashin farko a shekarar 2025.

Wannan ne tunanin da ake da shi. Sai dai a zahiri, ba a cimma komai ba.

Wani hoton da aka dauka da tauraron dan Adam kawo yanzu na nuna cewa an gina murabbu'i daya na birnin The Line kawai. Baya ga jerin wasu gidaje, akwai wurin ninkaya biuyu da filin wasan kwallon kafa daya.

A completed square of the Neom project

Asalin hoton, Google Earth

Bayanan hoto, Wani hoton da aka dauka da tauraron dan Adam na birnin The Line, wanda bangare ne na yankin Neom

Sai dai akwai yiwuwar a gina irin wannan birnin mai kayayyakin ci gaba da zai raya yanayi a tsakiyar hamada?

Dakta Mahal Shehabi, wani kwararre a fannin ilimin makamashi da ke koyarwa a jami'ar Oxford ya ce akwai abubuan da ya kamata a mayar da hankali kansu idan ana son tantance ko aikin gina Neom mai yiwuwa ne. Shin za a rika samar da abinci a wurin ne ko kuwa za a rika shigar da abinci ne daga kasashen waje?

Shafin intanet na Neom na cewa Neom zai zama "yanki mai samar wa kansa da abincin da zai gamsar da mazauna cikinsa".

Shafin ya bayyana cewa za a gina wuraren noma abinci da a turanci ake kira 'greenhouse' - a wannan kasar da ke shigar da kashi 80 cikin 100 na abincin da jama'arta ke ci.

Akwai tambayoyi kan yiwuwar wannan aikin na lokaci mai tsawo.

Publicity material shows a greenhouse providing food for Neom

Asalin hoton, YouTube/Neom

Bayanan hoto, Wani hoton da aka wallafa da ke nuna irin wuraren noma na zamani da za a samar a Neom

Wasu na sukar Yarima mai jiran gado, Mohammed Bin Salman - wanda shi ne ke jagorantar wannan aikin - da kasancewa mutumin da ke yin manyan alkawura kan inganta yanayi domin kawar da hankulan duniya daga ainihin abubuwan da ke faruwa a zahirance.

A misali, Yariman ya yi alkawarin Saudiyya za ta rage yawan iska mai dumama yanayi baki daya nan da 2060.

Sai dai masana na ganin tilas kasar ta rage yawan man fetur din da take hakowa kashi 5 cikin 100 daga yanzu zuwa shekarar 2030.

Saudiyya ba za ta iya cimma wannan matsayar ba domin makonni kadan kafin Saudiyya ta yi alkawarin da ta yi a taron rage dumamar yanayi na COP26 na bana, ministan makamashin kasar Yarima Abdulaziz bin Salman ya ce Saudiyya ba za ta rage yawan man da ta ke samarwa a duniya ba.

Ya ce; "Za mu kasance na karshe cikin kasashen duniya, kuma za mu hako dukkan sauran man da ya rage cikin kasa."

Publicity material shows a sea of solar panels to power Neom

Asalin hoton, YouTube/Neom

Bayanan hoto, Wasu hotunan talla na yin alkawarin samar da "makamashin da ba ya karewa" ta hanyar kafa dubban madubai domin tattaro hasken rana.

'Ana bukatar sabon tunani da dabaru'

Masu kare kudurin na Saudiyya na cewa ya zama wajibi a fara sabon zubi ta hanyar gina sabon birni wanda za a rika amfani da makamashi mai tsafta, kamar na hasken rana da mai amfani da iska.

Ali Shihabi, mai bayar da shawara kan gina yankin na Neom ya ce, "Saudiyya na bukatar wasu sababbin dabaru saboda yankin Gabas ta Tsakiya na fuskantar hatsarin rashin ruwa.

Smoke emitting from seawater desalination plant, Jizan Province, Saudi Arabia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda hayaki ke tudada daga wata masana'antar tace ruwan teku zuwa na ruwan sha a Saudiyya

Akwai kuma tambayoyin da awasu ke yi kan ainihin wadanda aka gina wa yankin na Neom.

Wasu na iya cewa yankin da ke tsakanin gabar tekun Bahar ul Ahmar da yanki mai duwatsu a kan iyakar Saudiyya da kasar Jordan wure ne da ya dace da a gina irin wannan birnin na musamman.

Sai dai akwai jama'a da ke rayuwa a yankin, wata tsohuwar al'umma da a tarihi 'yan kabilar Huwaitat masu rayuwa irin ta Fulani.

An yi alkawarin wannan aikin zai haifar da ayyukan yi a wannan yankin da bai sami ci gaba na zamani ba, amma zuwa yanzu mazauna yankin ba su dandana wannan ci gaban ba.

Masu fafutukar kare hakkin dan Adam na cewa an tashi wasu garuruwa biyu kuma an raba 'yan kabilar Huwaitat da karfin hukuma ba tare da an biya su isasshen kudin diyya ba domin a gina wannan katafaren birnin.

Wani mutum daya ya rasa ransa. A watan Afrilun 2020, wani mai suna Abdulrahim al-Huwaiti ya ki yarda a fitar da shi daga gidansa da ke Tabuk, kuma ya rika wallafa bidiyo a intanet.

Bayan wasu kwanaki, jami'an tsaron Saudiyya sun harbe shi - kamar yadda yayi hasashen za su yi.

Abdul Rahim al-Huwaiti posted videos online saying he expected to be killed

Asalin hoton, YouTube

Bayanan hoto, Abdul Rahim al-Huwaiti ya wallafa bidiyo a intanet, yana cewa ya san za a kashe shi

Kakakin ofishin jakadancin Saudiyya a Washington DC, Fahad Nazer ya musanta ikirarin da ake yi cewa Saudiyya na tilasta wa Huwaitat barin garuruwansu, amma bai musanta kashe al Huwaitat da jami'an tsaro suka yi ba, sai dai ya yi watsi da batun, yana kiransa "wata karamar matsala".

Masu kare hakkin dan Adam na cewa wannan aikin zai amfani masu hannu da shuni ne kawai. Akwai labaran da ke cewa an gina wa 'yan gidan sarautar Saudiyya fadoji.

Hotunan da aka dauka da tauraron dan Adam na nuna wurin saukar jirgi mai saukar ungulu da wani wurin wasan golf da tuni aka kammala gina su.

Satellite image showing part of Neom called a tourist attraction, including a golf course and a helipad

Asalin hoton, Google earth

Bayanan hoto, Hotunan da aka dauka da tauraron dan Adam na nuna wurin saukar jirgi mai saukar ungulu da wani wurin wasan golf da tuni aka kammala gina su.

Ali Shihabi ya ce za a samar wa kwa da kowa wurin zama cikin sabon birnin, "akwai leburori da miloniyoyi", sai dai ya yarda cewa ba haka aka tsara lamarin ba tun da farko.

"Ina jin babbar matsalar Neom ita ce ta gaza a bangaren wayar da kan jama'a," inji shi. "Jama'a na kallon birnin a matsayin wurin shakaawar attajirai."

An oil installation in Saudi Arabia's northeastern Gulf port of Jubail

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata tashar tace man fetur a tashar bakin teku da Jubail ta arewa maso gabashin Saudiyya

Kakakin gwamnatin Saudiyya fahad Nazer ya musanta cewa kasar na kokarin yi wa duniya rufa ido ne, kuma ya kafe cewa za ta yaye kanta daga amfani da makamashin man fetur domin komawa ga wanda zai talafa wa yanayi da muhali.

Kuma yayin da ake da shakku kan ko zaa gina birnin na Neom da gaske, Ali Shihabi ya gayyace mu da nu yi odar gida a birnin The Line, "kafin kowa ya fara yin oda."