Chelsea v Palmeiras: Watakila Mendy zai kama wa Chelsea a wasan ƙarshe na kofin duniya na ƙungiyoyi

Asalin hoton, Getty Images
Golan Chelsea Edouard Mendy a shirye yake domin ya kara a wasan ƙarshe na kofin duniya na ƙungiyoyi wanda kulob dinsa na Chelsea zai kara da Palmeiras, kamar yadda mataimakin kocin Chelsea Zsolt Low ya bayyana.
Mendy dai ya shirya ne bayan taimaka wa Senegal ta lashe gasar cin kofin Afrika .
Kepa Arrizabalaga ne ya maye gurbin Mendy a lokacin da ya tafi gasar Afcon kuma ya taka rawar gani a zagayen kusa da na ƙarshe bayan nasarar da Chelsea ɗin ta yi kan Al Hilal.
Haka kuma ƙungiyar Chelsea na fatan kocinta Thomas Tuchel zai samu damar halartar wasan ƙarshe bayan ya kasa zuwa wasan baya da aka buga saboda korona.
Low ya ce zai yi magana da Tuchel kafin a yanke shawara kan wanda zai kama gola a Abu Dhabi.

Asalin hoton, Getty Images
"Za mu yi magana da Thomas," in ji shi.
"Za a yanke shawarar ne sa'o'i kaɗan kafin wasan amma idan muka yanke shawarar zabar ɗaya daga cikinsu, kada wanda ba a zaɓa ba da ke zaune a benci ya shiga damuwa ko ya ji ba daɗi.
"Duka gololin sun taka rawar gani a makonnin da suka gabata wanda hakan ya sa ake ta tambaya kan wannan wasa."











