TikTok zai dauki mataki a kan bidiyon koyar da cin abinci da basu dace ba

Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin shafin sada zumunta da muhawara na TikTok ya sanar da wasu sauye-sauye ga ka'idojin amfani da shafin domin kawar da hotunan da suke yada dabi'ar cin abincin da ba ta dace ba.
Sahafin zai rika cire duk wani hoton bidiyo da ke karfafa wa mutane guiwa kan su rika motsa jiki da yawa da kuma yin azumi na dan lokaci.
Haka kuma kamfanin zai faɗaɗa ayyukansa ta yadda shafin zai riƙa ganowa tare da cire hotunan bidiyo na tsirara na manya da ayyukan da suka saba ƙa'ida ko kuma masu jefa rayuwar ƙananan yara cikin haɗari.
Kamfanin zai yi sauye-sauye ne saboda damuwar da ƴan siyasa da hukumomi ke nunawa.
Shafukan sada zumunta da muhawara na fuskantar matsin-lamba a ƴan watannin nan a kan yadda suke barin abubuwan da suka shafi rayuwar matasan da ke amfani da su sakaka.
Gwamnatin Birtaniya na shirin ɓullo da wata sabuwar doka, da ta shafi amfani da shafukan intanet, wadda za ta ɗaura tara mai yawan gaske ga shafukan sada zumunta da muhawara, wadanda aka ga ba sa tashi tsaye sosai wajen hana sanya saƙonni ko hotuna ko bidiyo masu haɗari ko cutarwa.
Kamfanin shafin na TikTok na China ya fuskanci tambayoyi a Amurka a watan Oktoba a kan kariya daga hotunan bidiyo masu haɗari.
Sanatocin da suka halarci zaman sun nuna cewa ana yawan sanya hotunan bidiyo da ke koyar da tsarin cin abinci da bai dace ba.
Tsarin cin abinci
A watan Satumba, TikTok ya bayar da rahoton cewa kusan mutane miliyan dubu daya ne ke amfani da shafin a duk wata.
Kamfanin da ke da shafin ya kuma ce daga hotunan bidiyo miliyan 91 da ya cire daga watan Yuli zuwa Satumba na shekarar 2021, kashi 88 cikin dari an tare su ne kafin jama'a su kalla.
Kamfanin yace duk da cewa tuni ya hana sanya abubuwa masu yada aƙida ta ƙyama ko tsangwama ko tsana, kamar nuna bambanci ga jinsin mata ko maza ko tsanar mata da sauran abubuwa makamantan haka. TikTok ya ce a yanzu ya ƙara sanya wasu tsare-tsare na fayyace dokokinsa ga masu amfani da shi.
TikTok ya kuma ce yana kokarin ƙirƙiro da hanyar da zai riƙa ganowa da kuma hana yara ganin wasu hotunan bidiyo.
Kamfanin ya ma ce a yanzu haka yana gwajin hanyoyin da masu amfani da shafin za su iya tsarin da sai wanda suka zaɓa zai ga bidiyon da suka sa.
A wannan shekarar kamfanin zai buɗe cibiyoyin sanya ido tare da gudanar da bincike a kan abubuwan da ake sanya wa a shafin a Washington da Dublin da kuma Singapore a bana.
Matakin na daga cikin tsare-tsaren kamfanin TikTok na faɗaɗa ayyukansa na kokarin hana kutse domin ganin abubuwan da ake sanyawa a cikinsa da satar shiga shafin wani ko kuma satar bayanai.












