Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Koriya ta Arewa na faɗaɗa gwajin nukiliya da kuɗaɗen sata na intanet - MDD
Wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya da aka gabatar wa manema labarai, ya ce Koriya ta Arewa ta saci miliyoyin kuɗaɗen intanet wato crypto ta kutsen intanet ɗin da take yi, domin ta yi amfani da su wajen shirye-shiryen makami mai linzaminta.
Daga tsakanin shekarar 2020 zuwa tsakiyar shekarar 2021 masu kutsen intanet sun saci fiye da dala miliyan 50 na kuɗaɗen intanet, kamar yadda masu bincike suka gano.
Irin waɗannan kutsen "muhimman hanyoyi ne na samun kuɗaɗen shiga" ga shirin nukiliyar Koriya, a cewarsu.
An miƙa wa kwamitin ƙaƙaba takunkumai na Majalisar Dinkin Duniya bayanan abubuwan da aka gano din a ranar Juma'a.
Kutsen ya shafi aƙalla hanyoyin musayar kuɗaɗen cyrpto a Amurka ta Arewa da Turai da Asiya.
Rahoton ya kuma ba da misali da wani bincike da aka wallafa a watan da ya wuce daga wani kamfanin tsaro na Chainalysis, da ya bayyana cewa kutsen intanet na Koriya ta Arewa ya sa tana iya samun kuɗin da yawansu ya kai dala miliyan 400 a bara.
A shekarar 2019 kuma, MDD ta ba da rahoton cewa Koriya ta Arewa ta samu dala biliyan biyu a shirinta na samar da makamai da nukiliya ta hanyar kutsen intanet.
Kwamitin Tsaro na MDD ya dakatar da Koriya ta Arewa daga yin gwaje-gwajen makamai masu linzami.
Haka kuma rahoton MDD ya ce duk da takunkumai masu zafin, Koriya ta Arewa ta ci gaba da yin gwaje -gwajen nata.
Ta kuma ci gaba da neman kayayyaki da fasaha da yadda za ta gudanar da abubuwa ta hanyar intanet da faɗaɗa binciken kimiyya.
Masu bibiyar takunkuman sun ce an samu ƙaruwar gwaje-gwajen makaman daga Koriya ta Arewa.
A ranar Juma'a Amurka ta ce a watan da ya gabata kaɗai Koriya ta Arewa ta yi gwajin nukiliya sau tara.
"Koriya ta Arewa ta nuna cewa ana samun ƙaruwar gwajen-gwajen da take yi har da a teku, da sake dagewa kan amfani da nukiliyarta," a cewar kwamitin da ke sa idon.
A ranar Juma'a, China da Rasha sun ƙi sanya hannu kan wata sanarwa da ta yi Allah-wadai da ƙaddamar da harba makamai masu linzamin da Koriya ta Arewan ta yi.
A ranar Lahadi kuwa, Amurka ta sanar da cewa wakilinta na musamman a Koriya ta Arewa zai gana da jami'an Japan da Koriya ta Kudu nan gaba a cikin makon nan don tattauna lamarin.
Rahoton MDD ya gano cewa yanayin halin jin ƙai da ake ciki a Koriya ta Arewa na ci gaba da munana. Ya ce wannan ya faru ne watakila a sakamakon matakin da ƙasar ta ɗauka na rufe iyakokinta a lokacin yaduwar annobar cutar korona.
Rashin samun bayanai daga Koriya ta Arewa na nufin zai yi wahala a gano irin wahalar da ake sha sakamakon takunkuman da ƙasashen duniya suka sanya mata.