Tsananin sanyi da kankara na kashe yara a sansanin 'yan gudun hijirar Syria

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Jarirai biyu sun mutu sakamakon tsananin sanyi bayan saukar dusar ƙanƙara da sanyi a kan tantunan 'yan gudun hijira a arewacin Syria.

Wani jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ya faɗa wa kamfanin labarai na AFP cewa jaririya mai kwana bakwai da kuma 'yar wata biyu sun mutu a yankin Idlib.

Mutum aƙalla miliyan biyu da dubu 800 ne suke zaune a sansanin 'yan gudun hijira a yankin da 'yan tawaye ke da ƙarfi, bayan sun bar gidajensu sakamakon yaƙin basarar ƙasar na shekara 10.

Da yawa na zaune ne cikin tsoffin tantuna ba tare da kayan sanyi ba ko kuma makamashin ɗumama jiki.

MDD ta yi gargaɗin cewa lamarin na ƙara ƙazancewa saboda taɓarɓarewar tattalin arziki a Syria, inda farashin kayan abinci suka ninka cikin shekara ɗaya, da kuma ƙarancin kuɗin ba da tallafi don sayen kayan sanyi da sauran buƙatu.

Ƙungiyar kare haƙƙi da ke Birtaniya ta Syrian Observatory for Human Rights ta ce mutuwar yaran da aka ruwaito ranar Talata na zaune ne a sansanonin da ke al-Ziyara da al-Sheikh Bahr a arewacin Idlib.

Ƙungiyar ta ƙara da cewa wani jaririn ɗan wata ɗaya ya rasu saboda sanyi a sansanin da ke Jarablus, wanda ke yankin Aleppo ranar 23 ga watan Janairu.

Kazalika, wani yaron ya mutu a Qastal Miqdad ranar 18 ga Janairu bayan dusar ƙanƙara ta lalata rufin tantinsu.

A cedwar MDD, sansani 287 na 'yan gudun hijira ne suka taɓu a Idlib da Aleppo sakamakon dusar ƙanƙara da ambaliya da iska mai ƙarfi waɗanda guguwa ta haddasa a 18 da 19 da 25 ga watan Janairu.

Ƙanƙara ta lalata aƙalla tanti 935 sannan ta taɓa fiye da 9,500.

MDD ta ƙara da cewa an samu gobara 68 a sansanoni tun daga farkon wannan shekarar, wadda ta kashe mutum biyu sannan ta jikkata wasu 24. Akasarin gobarar sun faru ne saboda kunna risho don jin ɗumi.

Shugaban ƙungiyar Save the Children a Syria, Sonia Khush, ta ce abu ne "da bai kamata ba a ce wani yaro ya shiga hunturu cikin fargaba game da tsira da rayuwarsa".

"Kusan shekara 11 kenan tun bayan fara yaƙin Syria, amma da alama duniya ta manta da rayuwar yara a arewa maso yammacin ƙasar," in ji ta.

"Waɗannan bala'o'i da za a iya kaucewa na nuna yadda yara ke tsananin buƙatar tallafi. Sannan suna buƙatar kawo ƙarshen yaƙin Syria kwata-kwata."