Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Garin da kyanwoyi suka fi 'yan Adam yawa
Bayan luguden wutar da garin Kafr Nabl na kasar Syria ya sha daga dakarun sojin Rasha da na Syria, yanzu kyanwa ta fi dan Adam yawa a garin.
Wakilin BBC Mike Thomson ya ce yanzu maguna ne ke debe wa junansu kewa.
Zaune a cikin baraguzan karkashin wani ginin gidan kasa, Salah Jaar ne (hotonsa ne a sama) yake neman tsira daga luguden bama-bamai daga sama. Kusa da shi wasu maguna ne a firgice kamar yadda shi ma yake a firgice suna tausar juna.
"Ina samun natsuwa idan ina jin dumin wadannan magunan," ya fada. "Hakan yana saukaka mani yayin da ake luguden wutar."
Kafin yanzu, mutum 40,000 ke zaune a garin Kafr Nabl amma yanzu kasa da 100 ne kacal suka rage. Amma da wuya a iya kintata yawan magunan da ke garin - tabbas daruruwa ne ko dubunnai.
"Mutane da dama sun bar garin Kafr Nabl. Magunan suna bukatar wanda zai kula da su ya ba su abinci, saboda haka sai suka koma gidajen 'yan kalilan din da suka rage. Kusan a kowanne gida yanzu akwai mage 15, wani gidan ma sun fi haka," in ji Salah.
Salah dan jarida ne, wakilin wani gidan rediyo mai suna Fresh FM. Duk da cewa an ragargaza ginin gidan rediyon a wani harin baya-bayan nan amma sun yi sa'a, kafin harin sun yi kaura zuwa wani garin mai makobtaka.
Gidan rediyon ya saba da mutane da kyanwoyi, wadanda da yawa suka mayar da ginin wurin kwana. Wani mai fafutikar kare hakkin dan Adam Raed Fares, wanda kungiyar IS ta halaka a 2018, har alawus ya rika ba su don saya masu madara da nama.
"An haifi maguna da yawa a nan. Daya daga ciikinsu mai launin ruwan kasa ta shiga ran Raed. Ta saba da shi sosai ko bacci a kusa da shi take yi." Salah ya bayyana.
Magunan sun taso wa Salah da sowa yayin da yake kokarin fita daga rusasshen gidan nasa, ya ce ai kusan kowa ya saba da hakan a garin.
"Wani zubin idan muna tafiya za ka ga maguna kamar 20 ko 30 suna yi mana rakiya, wasu daga ciki har gida suke biyo mu."
Idan dare ya yi kuma haushin karnuka ne ke karade garin domin su ma suna cikin yunwa kuma hakan ke saka su shiga rige-rigen neman abinci tsakaninsu da magunan.
Akasarin magunan dai ababen kauna ne a gidaje a wurin iyalai da dama kafin dakarun gwamnatin Syria su fara kaddamar da hara-haren kwace garin Idlib a watan Afrilu da ya gabata. Saboda haka dole ne yanzu su nemi matsuguni a cikin baraguzan gine-gine.
Duk da cewa mutane irin su Salah ba su san inda za su samu abincin rana ba ko na dare, ko ma za su ci gaba da zama da ransu, da alama abokansa maguna ba sa rasa inda za su samu nasu abincin.
"Duk sanda na ci abinci suna ci su ma. Kayan marmari ko taliya ko kuma dai busassun abubuwa duka suna samu. A wannan yanayin ina jin cewa dukkanmu abin tausayi ne kuma ya kamata mu taimaki juna." Salah ya ce.
Duk da irin halin yaki da mutane har ma da dabbobin garin ke ciki, a haka suke bai wa kyanwoyin kulawa idan an raunata su a harin bam.
"Akwai wani abokina da ke da maguna a gidansa. Sai aka raunata daya daga cikinsu a wani harin makamin roka, a haka muka lallaba muka kai ta garin Idlib domin nema mata magani. Yanzu haka tana tafiya kamar abin bai faru ba," Salah ya ce.
Kasancewar sojojin gwamnatin Syria ba su da nisa da garin na Kafr Nabl, akwai yiwuwar za a kawo hari nan kusa.
Salah ya ce a firgice yake ba wai don kansa da abokansa ba, saboda al'ummar magunan da ke garin.
"Mun sha fama da abubuwan tashin hankali da kuma na jin dadi tare da su. Sun zama abokan rayuwarmu," in ji Salah.
Sannan ya ce idan ma wani abu ya faru da zai tilasta masu barin garin, to za su debi maguna iya yawan wadanda za su iya tare da su.