BBC ta kaddamar da gasar Komla Dumor ta 2022

An wallafa

BBC na neman zaƙaƙuran 'yan jaridar Afirka da za ta ɗaga sama, domin shiga gasar Komla Dumor ta wannan shekarar, kuma shi ne karo na bakwai a jere da ake yin wannan gasa.

Ana gayyatar 'yan jarida daga sassa daban-daban na duniya domin shiga wannan gasa, da nufin gano matasan 'yan jarida masu hazaƙa a nahiyar.

Wanda ya yi nasara a wannan gasa ta 2022, zai samu nasarar shafe watanni uku ya na aiki a hedikwatar BBC da ke birnin Landan, domin sanin makamar aiki ta fannoni daban-daban.

Za dai a rufe shiga gasar, ranar 16 ga watan Faburairu 2022, da misalin karfe 11:59 agogon GMT.

An kirkiri gasar ce domin tunawa da kuma girmama ɗan ƙasar Ghana Komla Dumor, fitaccen mai gabatar da shirye-shirye a tashar labarai ta BBC, wanda ya yi mutuwar fuju'a a shekarar 2014, a lokacin yana da shekara 41 a duniya.

Mai dakin marigayin, Kwansema Dumor ta shaidawa Victoria Rubadiri da ta yi nasarar lashe gasar a shekarar 2020, cewa ta na ''alfahari da rawar da mijinta ya taka a BBC'', sannan ita da iyalanta su na miƙa sakon godiya ga BBC da suke tunawa da mijinta ta wannan fanni na sanya kyauta saboda shi.

BBC dai na bai wa 'yan jaridar Afirka kwarin gwiwar shiga gasar, wadda manufarta shi ne fitar da zaƙaƙurin ɗan jarida, da zai sake koyon aikin da zai daukaka shi a nahiyar.

Sannan ɗan jaridar da ya yi nasara, zai samu horo, da ziyartar wata kasa a Afirka domin yin rahoton da ya yi bincike a kai sannan za a yada shi a tashar BBC duk duniya su kalla.

Dumor ya yi fice a Afirka, wajen salon aikin shi na jarida, da yadda ya ke gabatar da shiri da rahotanni cikin ƙwarewa da basira, haƙiƙa aikinsa ya shafi Afirka da ma duniya baki ɗaya.

BBC na son ci gaba da yin wannan gasa a kowacce shekara, domin taimakon 'yan jarida, yadda za su bada labarin da ya shafi Afirka domin duniya ta san da su.

Saboda annobar korona da ta barke a duniya, wadda ta yi nasara a shekarar 2020 wato, Rubadiri ba ta samu horon da ya dace ba sai aka dage zuwa shekarar 2021.

A lokacin da ta ke yin aiki, ta yi balaguro zuwa birnin Kinshasa, na Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo, inda ta yi rahoto na musamman a kan wata manhaja da aka samar da ta bunkasa harkar sufuri a ƙasar.

Kuma Darakta-Janar na BBC Tim Davie ne ya bai wa Rubadiri kyautar da ta ci.

"Baya ga samun damar girmama wani ɓangare na tunawa da marigayi Komla Dumor, da yadda BBC ta karrama aikina a matsayin 'yar jarida, na ga matukar sauye-sauye a rayuwata a tsawon watanni uku da na kwashe a birnin Landan," in ji ta.

"Horon da na samu da yadda ake tafiyar da komai, ya kara buɗe mun ido a harkar jarida. Wannan dama ta bude min idon sanin inda na dosa idan ana batun bada labari, ta nuna min sabbin hanyoyin yadda zan bada labaran da suka shafi Afirka."

Daraktar sashen turanci na BCC, Liliane Landor, ta ce: "Na yi farin ciki da BBC ta kirkiro wannan gasa saboda Komla Dumor, a kuma ga irin abin alfaharin da ya bari, ina farin cikin dawo da gasar nan, ga shi har an shiga shekara ta bakwai.

"Wadanda suka yi nasara a baya, sun nuna ƙwarewa da sadaukarwa kamar yadda Komla ya ke a lokacin bincike da bada labaran Afirka. Mun zaku mu karrama wanda zai yi nasara a wannan shekarar, da ganin abin da Komla ya bari na kyakkyawan aiki."

Dumor dai shi ke gabatar da wani shiri irinsa na farko da BBC ta fara, da kacokan ya maida hankali kan labaran da suka shafi Afirka, wato Focus on Africa, da ake gabatarwa a Talbijin da harshen turanci. Kuma shi ne ɗaya daga cikin masu jagorantar gabatar da shirin safe da ya shafi Turai.

A shekarar 2007 ya fara aiki da BBC, bayan shafe shekara 10 ya na gabatar da shiri da harshensa na gida wato Ghana, ya kuma taba cin kyautar ɗan jaridar shekara na Ghana.

Tsakanin shekarar 2007 zuwa 2009, ya fara gabatar da shirin "Network Africa" da sashen turanci na BBC, kafin daga bisani ya koma fannin shirye-shirye na "The World Today" duk dai a BBC.

A shekarar 2009, Dumor ya zama na farko da ya fara gabatar da labaran kasuwancin Afirka, wato African business da ake yadawa a tashar BBC. Ya yi tafiye-tafiye a nahiyar Afirka, inda ya rinƙa haɗuwa da manyan 'yan kasuwar Afirka, da dauko rahotannin abubuwan da ke faruwa ta fannin kasuwancin Afirka, a lokacin da suke cin kasuwarsu a duniya.

A shekarar 2013, Dumor ya fito da shahararriyar mujallar nan ta Afirka wato "New African magazine", wadda ta ke fitar da shahararrun mutanen nahiyar guda 100, kuma Komla na daga cikinsu.

Wadanda suka lashe gasar a baya:

  • 2015: Nancy Kacungira daga Uganda
  • 2016: Didi Akinyelure daga Nigeria
  • 2017: Amina Yuguda daga Nigeria
  • 2018: Waihiga Mwaura daga Kenya
  • 2019: Solomon Serwanjja dagaUganda
  • 2020: Victoria Rubadiri daga Kenya