Abin da ya sa har yanzu ilimin ƙananan yara ke cikin barazana a kudu da hamadar Sahara

Asalin hoton, Getty Images
Daga nan har zuwa shekara ta 2030, za a ci gaba da samun aƙalla kashi takwas cikin 100 na ƙananan yara da shekarunsu suka kai shiga firamare amma ba sa zuwa makaranta a yankin kudu da hamadar Sahara.
Wannan wani ɓangare ne na rahoton da Hukumar bunƙasa ilmi, kimiyya da al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO ta fitar kenan mai taken ba a sa ran ƙasashe za su cimma burin bunƙasa ilmi a shekara ta 2030.
Fitar da rahoton ya zo ne daidai da Ranar Ilmi ta Duniya wadda ake gudanarwa duk rana mai kamar ta yau 24 ga watan Janairu.
Sabon rahoton da Cibiyar tattara alƙaluma ta UNESCO da wata ƙungiya mai suna Global Education Monitoring Report suka fitar, na cewa a mizanin da suka shatawa kansu, ƙasashen duniya ba za su cimma buri na huɗu na Muradan Ci gaba Mai ɗorewa nan da shekara ta 2030 ba.
Rahoton ya ce har yanzu akwai kalubale ta fuskar shigar da kowa, da tabbatar da daidaito wajen samun ilmi mai inganci da damammakin koyo tsawon rayuwa ga kowa.
A cewarsa, wannan wata farkarwa ce ga shugabannin ƙasashen duniya yayin da miliyoyin ƙananan yara za su ci gaba da rasa damar shiga makaranta da koyon ilmi ingantacce.
Sai dai ya ce ƙasashe za su iya ko za su kusa cimma burin samar da ilmin firamare ga kowa. In ban da a yankin kudu da hamadar sahara, inda a yanzu kashi 19 cikin 100 na ƙananan yara ba sa zuwa makaranta.
Rahoton ya ce nan da 2030, ana sa ran ƙasashe a kudu da Sahara za su samu raguwar yaran da ba sa zuwa babbar makarantar Sakandire daga kashi 47 cikin 100 zuwa 32 cikin 100.
Ya ce ƙasashe sun fi sanyin gwiwa game da yiwuwar hanzarta ci gaba a fannin ƙwarewar lissafi a faɗin duniya.
Mizanin ya nuna cewa ana sa ran nan da 2030, kashi 26 cikin 100 ba za su iya sassauƙan lissafi a farkon shekarunsu na shiga firamare ba, kashi 32 cikin 100 kuma a ƙarshen shekarun firamare yayin da kashi 32 cikin 100 a shekarunsu na ƙaramar Sakandire.
Rahoton da aka yi wa laƙabi da, mizanin Muradan Ci gaba mai Ɗorawa na huɗu: cika alƙawurranmu, ya tattara sakamako daga ƙoƙarin da duniya ta yi a cikin shekara biyu.
Ƙasashen da ke cikin tsarin sun sanya burinsu kan shekara ta 2025 zuwa 2030 dangane da muhimman fannoni guda shida: bunƙasa shigar da 'yan ƙanana-ƙananan yara makaranta, halartar makaranta; kammalawa; samun mafi ƙarancin ƙwarewa a fannin karatu da iya lissafi; malamai masu horo; da kuma kuɗin da ake kashewa a fannin ilmi.












