Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yemen: Mutum fiye da 70 sun mutu a hari ta saman da kawancen da Saudiya ke jagoranta ya kai
Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah-wadai da hari ta saman da kawancen da Saudi Arabia ke jagoranta ta kai a wani gidan yari a Yemen lamarin da ya haddasa mutuwar mutum fiye da 70.
Lamarin ya faru ne a ranar Jumma'a bayan jefa wani abu a Saada, wata matattarar da 'yan tawayen Houthi ke zaune.
Sakatare Janar na Majalisar Antonio Guterres, ya ce akwai bukatar a dakatar da karuwar tashin hankali a yankin, in da ya yi kiran da a yi bincike a kan hare-hare ta saman da aka kai a ranar Jumma'ar.
Tun a shekarar 2015 ne kawancen sojin da Saudi Arabia ke jagoranta ke gwabzawa da 'yan tawayen Houthi.
Dubban fararen hula ciki har da kananan yara fiye da dubu 10 ne aka kashe ko kuma aka jikkata a sakamakon fadan.
Yayin da wasu miliyoyi kuma suka rasa matsugunnansu, baya ga yadda ake fama da matsalar yunwa a wuraren da rikicin ya shafa.
Sa'oi bayan harin, jami'an ceto suka fara zakulo gawawwaki a cikin baraguzan gini, in da fatan da ake dashi na samun wasu da rai ya ci tura.
Kungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières, ta ce har yanzu ba a san adadin wadanda suka rasa ransu ba.
Wani gidan talbijin mallakin 'yan Houthi ya nuna hotunan abubuwan da suka faru a wajen da kuma yadda mutane ke kwashe baraguzan gini da hannunsu,
Kungiyar likitocin ta Médecins Sans Frontières, ta ce an kai wadanda suka jikkata fiye da 200 wani asibiti da ke yankin da lamarin ya faru.