Kasuwar ƴan ƙwallo: CR7 zai bar United, Munich na shirin sayar da Lewandoski, Ramsey ya fusata Juventus

An wallafa

Bayern Munich za ta iya yanke shawarar siyar da dan wasan gaban Poland Robert Lewandowski a bazara idan bai sanya hannu kan sabunta kwantiragi ba. Kwantiragin ɗan wasan mai shekaru 33 zai kare a watan Yunin 2023. (Bild, via Marca.)

Manchester United za ta bar dan wasan tsakiyarta Jesse Lingard ya tafi a watan Janairu idan duk kungiyar da ke sonsa ta biya fam miliyan 3 da rabi (Talksport)

Atletico Madrid ba za ta bar dan wasan gaban Uruguay Luis Suarez, mai shekara 34, wanda ake alakanta shi da Aston Villa, ya tafi a watan Janairu ba. (Goal)

Barcelona na tattaunawa da dan wasan bayan Chelsea Andreas Christensen, mai shekara 25, inda kwantiragin dan kasar Denmark zai kare a karshen kakar wasa ta bana. (Sport - in Spanish)

Bayern Munich na shirin kalubalantar Manchester United a takarar neman dan wasan tsakiyar Switzerland da Borussia Monchengladbach Denis Zakaria, mai shekara 25. (Christian Falk)

AC Milan na sha'awar sayen dan wasan bayan Tottenham Japhet Tanganga, mai shekara 22 a matsayin aro, amma kungiyar ta Premier ta fi son sayar da dan Ingilan. (Sun)

Arsenal ta kara kaimi wajen zawarcin dan wasan tsakiyar Juventus Arthur Melo. Gunners na fatan daukar dan kasar na Brazil mai shekaru 25 a matsayin aro na tsawon kakar wasa ta bana. (Goal)

Har ila yau Arsenal din ta shirya tsaf don mayar da dan wasan gaban Fiorentina Dusan Vlahovic, mai shekara 21, daya daga cikin 'yan wasan da ke karbar albashi mafi tsoka a duniya, amma har yanzu dan wasan na Serbia bai da tabbacin komawa Gunners din. (La Nazione via 90Min)

Paris St-Germain na da kwarin gwiwar cewa tsohon kocin Real Madrid Zinedine Zidane, mai shekara 49, zai jagoranci Parc des Princes a kakar wasa mai zuwa. (Marca)

Burnley na sa ido kan abubuwan da ke faruwa da dan wasan baya na Ingila Chris Basham, mai shekara 33, wanda kwantiraginsa a Sheffield United zai kare a bazara. (Mail)

Juventus ta fusata da dan wasan tsakiyar Wales Aaron Ramsey bayan da dan wasan mai shekaru 31 ya ki amincewa da tayin barin Italiya daga kungiyoyin Ingila da Spain. ((Calciomercato, via Mail)

Wakilan Cristiano Ronaldo sun shaidawa Manchester United cewa dan wasan gaban na Portugal mai shekara 36, zai nemi barin Old Trafford a bazara idan kungiyar ta kasa tsallakewa zuwa gasar zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa. (Sun)

Tsohon dan wasan Faransa da Arsenal, Thierry Henry, na cikin masu neman zama kocin Bordeaux bayan ya ajiye aiki a matsayin kocin Montreal Impact a watan Fabrairu. (RMC Sport - in French)

Stoke City na shirin dauko dan wasan Aston Villa dan kasar Ingila Jaden Philogene-Bidace, mai shekara 19 a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasa ta bana. (Athletic - subscription required)