Hotuna Afirka na mako 7 zuwa 13 ga Janairun 2022

Wani mahayin rakumi na tsikarar rakumin da sandarsa a yayin tserern rakuma na Wadi Zalaga da ake yi duk shekara a Masar

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani matshi a kan rakuminsa yayin tseren rakuma da aka yi na shekara-shekara da ake kira Wadi Zalaga a kudancin Sinai a Masar a ranar Litinin...
An wallafa
Wani dan yaro da yake hawa rakumi yana murmushi yayin da rakumin nasa ke miƙe kafa a cikin yashi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An dauki wannan hoton lokacin da 'yan kabilar Bedu ke sanya yaransu gasar rakuma, rakumin ya kwanta a kasa ne domin miƙa bayan gajiyar da ya yi
Wata mai bin addinin Voodoo tana tafiya bayan kammala addu'o'i da aka yi a bikin da ake gudanarwa duk shekara wanda aka yi a Benin a ranar 10 ga watan Janairu 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Bikin ibada na Voodoo da aka yi ranar Litinin a Benin, wata mata cikin tsakiyar rana a bakin ruwa a garin Ouidah, ana daukar hakan a matsayin wajen wankan masu bin voodoo..
An ta ganin mabiyan Voodoo kamar yadda aka saba a duk lokacin bautar na shekara-shekara

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yayin da wannan mutumin ya baza wasu ƙasusuwa a gabansa wadanda aka ce suna da wani tasiri da ya wuce hankali.
An ta ganin mabiyan Voodoo kamar yadda aka saba a duk lokacin bautar na shekara-shekara

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An gudanar da abubuwan bauta ciki har da addu'o'i da sadaukarwa da kuma yanke-yanke.
Mutane na motsa jiki da safe a Abuja ranar 13 ga watan Janairu 2022

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Alhamis wasu masu motsa jiki da farar safiya a Abuja babban birnin Najeriya
Magoya bayan sarkin Khoisan a Afrika Ta Kudu suna wake da kona turare bayan da ake tsare da shugabansu a hannun 'yan sanda wanda aka kama saboda laifin shuka tabar wiwi a ranar 13 ga watan Janiru

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A Pretoria babban birnin Afrika ta Kudu mutanen yankin Khoisan suna ƙona wani turare a bakin kotun Majistare lokacin da suke jiran a saki shugabansu.
Sarkin Khoisan an lullube shi da ganye yayin da ake kama shi

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An kama shi kwana guda gabanin bikin al'ada na yawo da ganye a ginin Union Building na gwamnati.
Filin wasa na Olambe da ke Yaounde a ranar Asabar

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Asabar kenan yadda rana ta fito ake iya ganinta ta saman dutse a Yaounde babban birnin Kamaru, kwana guda kafin fara gasar AFCON
Magoya bayan Kamaru ya yin wasanta da Burkina Faso wanda har shugaban kasar Paul biya ya halarta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasan farko na gasar Afcon magoya bayan masu masaukin baki kenan Kamaru
Magoya bayan Burkina Faso ya yin wasantada Kamaru

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ga bangaren Burkina Faso, Stallions...
Magoya bayan Burkina Faso ya yin wasantada Kamaru

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutanen Burkina Faso sun ta yin murna har bayan kammala wasan duk da cewa an doke su 2-1
Yar Najeriya na ihu da wake gabanin fara wasan rukunin D wanda aka buga tsakanin Najeriya da Masar a ranar Talata

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wata mai goyon bayan Najeriya cikin murmushi bayan kasar ta doke Masar 1-0
Gambiya da take a rukunin F ta doke Mauritania da ci daya babu ko daya a ranar 12 ga watan Janairun 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Magoya bayan Namibia na da dukkan hujjar da za ta sanya su farun ciki saboda sun doke Mauritania da ci daya
Daliban makarantar Kankugulu a aji ranar farko da aka koma makaranta bayan da annobar korona ta sanya aka rufe karatu

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wannan kuwa a wani yankin ne na Kampala babban birnin Uganda, inda yara suka koma makaranta a ranar Litinin bayan rufe su da aka yi na tsawon shekara biyu saboda annobar korona
Ranar farko da aka koma makaranta bayan da annobar korona ta sanya aka rufe karatu

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A yankin kudu maso gabashin Mbale yara na wasa da lilo, cikin jin dadi da suke na komawa makaranta
Gilbert Chihoro na tafiya cikin gona domin cire amfanin masarar da ya samu bayan mamamon ruwan sama da aka fuskanta

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A Zimbabwe ruwan sama da aka samu kamar da bakin ƙwarya ya janyo asara ga manoma a ranar Laraba, wani mutum na tafiya ta cikin ruwan domin cire kayan amfanin masara

Dukkan hotunan na da hakkin mallaka