Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Sulaiman Sulaiman
Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Sheikh Muhammad Sulaiman Sulaiman asalin ɗan Gombe ne da ke arewa maso gabashin Najeriya amma ya gudanar da akasarin rayuwarsa ce a birnin Jos na Jihar Filato.
Haka kuma ya yi galibin rayuwar karatunsa ne a garin na Jos.
Malamin ya soma karatunsa na firamare a wata makaranta da ke wani ƙauye mai suna Umoko a Jihar Ribas da ke kudancin Najeriya. Bayan malamin ya kammala firamarensa sai ya kuma yi sakandare inda ya yi H.I.S wato Higher Islamic Studies a wancan lokaci inda ya yi karatun a garin Jos.
A lokacin da yake karatun na H.I.S, Sheikh Sulaiman ya haɗa abu biyu a lokaci guda inda ya rinƙa karatu a Arabic Teachers College Grade 3.
Bayan ya kammala, sai da taimakon Sheikh Musa Ibrahim Sagagi Malam Muhammad ya samu gurbin karatu a kwalejin ilimi ta Kano.
Malam ya shafe shekara uku yana karatu a kwalejin ilimi ta Kano inda ya samu takardar shaidar karatu ta NCE, inda a cewarsa, daga kansu aka soke yi wa ƙasa hidima ga waɗanda suka kammala NCE wanda hakan bai bar su sun yi NYSC ɗin ba.
Bayan nan ne kuma sai malamin ya koma karantarwa a makarantun da ya kammala a baya, amma kuma daga baya an ɗauke shi aikin koyarwa a makarantar Al-Iman inda ya rinƙa karantarwa a sashen ƙananan yara inda yake koyar da su Addinin Musulunci.
Shekara guda kawai ya yi a ɓangaren sai Allah ya ba shi ikon tafiya Saudiyya inda suka tafi Madina domin karatu.
Ɗaya daga cikin ƙalubalen da suka soma fuskanta a lokacin da suka soma karatu a Madina shi ne idan malamai da sauran ɗalibai suna larabci ba su gane me suke faɗa sakamakon Larabci ne na gargajiya suke yi, amma daga baya sun zage damtse domin koyon irinsa.
Sheikh Muhammad ya bayyana cewa a shekarar da ya je Madina karatu ya haɗu da mutane irin su Dakta Mansur da Farfesa Sani Umar Rijiyar Lemo da Sheikh Jafar Mahmud Adam wanda yana gabansu da shekara ɗaya da kuma Sheikh Abdulwahab Abdullah da Dakta Bashir Ali.
A halin yanzu dai Sheikh Muhammad shi ne babban limamin Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna haka kuma yana koyarwa a Tsangayar Ilimin Addinin Musulunci Mai Zurfi Na Jami'ar Jihar Kaduna wato Kaduna State University.
Surar da ta fi ba malam wahala wajen hadda
Sheikh Muhammad ya bayyana cewa surar da ta fi ba shi wahala a wajen hadda ita ce Suratul Al-An'am.
Ya ce surar ta ba shi wahala wajen hadda matuƙa sakamakon akwai wasu wurare mutashabihai da suke shiga ciki, kamar yadda ya ce.
Haka kuma Malam ya ce a duk surorin Al-Kur'ani ya fi son Suratul Al-An'fal saboda akwai wata aya a ciki mai kwantar masa da hankali, haka kuma ya bayyana cewa yana son Ayatul Kursiyu ta ce cikin Suratil Al-Bakra.
Me yake faranta wa Malam rai?
Sheikh Muhammad ya bayyana cewa babu abin da ya fi faranta masa rai irin ganin mutumin da aka zalunce shi kuma aka cutar da shi lokaci guda ya zo ya ce ya yafe kuma ya haƙura.
Malam ya ce wannan abu yana matuƙar faranta masa rai. Ya ce shi ma ya sa hakan a cikin zuciyarsa cewa duk mutumin da ya zalunce shi ko ya cutar da shi ba zai kwana da shi a zuciyarsa ba domin kwana da shi a zuciya zai baƙanta masa rai kuma ba ya son abin da zai baƙanta masa rai.
Abin farin cikin da ba zai taɓa mantawa da shi ba
Malam ya ce abin farin cikin da ba zai taɓa mantawa da shi ba a duniya shi ne wani lokaci da mahaifiyarsa ta karɓi aron keken ɗinki, sai mai keken ta yi ta matsa mata da ta mayar mata da kekenta, shi kuma cikin ikon Allah sai ya sayo mata wani sabon keken ɗinki wanda a cewarsa, hakan ya sa mahaifiyarsa ta yi matuƙar farin ciki.
Batun iyalin malam
Sheikh Muhammad ya bayyana cewa yana da mata biyu da kuma ƴaya 15 amma uku daga ciki sun rasu.
Ya bayyana cewa 'ya'yansa uku maza ne sauran duka mata ne.
Babban burin Malam
Malam ya ce babban burinsa a rayuwa shi ne ya taimaka wa al'ummarsa ta ɓangaren ilimi da harkar rayuwarsu da kuma gajiyayyu