Kotu a Saudiyya ta ba da izinin kunyata mutumin da aka kama da laifin cin zarafin mata

File photo shows a Saudi police officer directing traffic in Mecca (26 July 2020)

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Dokar, wacce ta fara aiki a shekarar 2008, tuni ta sanya sharuɗɗa na shafe shekara biyu a gidan yari da kuma biyan tara har ta dala 27,000
An wallafa

Wata kotu a yankin Makkah a ƙasar Saudiyya ta wanke wani limamin masallaci daga tuhumar da ake yi masa ta cin zarafin mata masu aikin gidansa.

Kotun ta yi watsi da ƙarar bisa hujjar cewa waɗanda suka shiga da ƙarar sun gaza gabatar da ƙwararan hujjojin da za su tabbatar da zarginsu.

Daga ƙarshe kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukuncin korar ƙarar, kamar yadda jaridar intanet ta Saudi Gazette ta ruwaito.

Mai shigar da ƙara na gwamnati ne ya miƙa ƙarar bayan da ya gudanar da bincike kan ƙorafin cin zarafin da aka shigar a kan limamin masallacin, wanda ɗan asalin Saudiyyan ne.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wata kotu a Saudiyya a karon farko ta bayar da izinin bayyana sunan wani mutum da aka kama a laifin cin zarafin mata da kuma kunyata shi a bainar jama'a, kamar yadda kafafen yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito.

Wata kotun hukunta masu manyan laifuka a Madina ce ta kama Yasser al-Arawi da laifin cin zarafin mata ta hanyar amfani da kalaman batsa.

An yanke masa hukuncin ɗaurin wata takwas a gidan yari da tarar dala 1,330.

An yi wa dokar yaƙi da cin zarafi garanbawul ne shekara ɗaya da ta gabata don bayar da damar wallafa sunayen masu irin laifin a jaridun ƙasar, kan abin da suka jawowa kansu.

An bai wa alkalai sauran damar ta yanke hukuncin duba ko "girman laifin da tasirinsa a cikin al'umma" ya ci a ɗaukar masa wannan matakin.

A wancan lokacin mutane da dama sun yi maraba da sauya dokar a ƙasar, inda har wani mai sharhi ya ce "abu ne da ya kamata a ce an daɗe da yi."

Dokar, wacce ta fara aiki a shekarar 2008, tuni ta sanya sharuɗɗa na shafe shekara biyu a gidan yari da kuma biyan tara har ta dala 27,000 ga waɗanda aka kama da laifin cin zarafin mata.

Waɗanda suka sake aikata laifin kuma za su yi shekara biyar a gidan yari tare da biyan tarar dala 80,000.

Duk da wadannan matakai na shari'a, wasu matan a Saudiyya na ci gaba da yin ƙorafi cewa hukumomi ba sa ɗaukar matakai sosai na hana cin zarafin.

Wata ta shaida wa BBC cewa irin tsokacin da ake yi a kan bidiyon intanet da ake tattara bayanan abubuwan da ke faruwa suna yawan zargin mata ne da cewa su suke jawowa ana cin zarafinsu, hakan kuma zai iya sanya wa a hukunta matan da ake cin zarafin fiye da masu aikata laifin.

line