Korar malamar makaranta mai rawa da ƙugu ta jawo muhawara a Masar

Asalin hoton, AYA YOUSSEF
- Marubuci, Daga Yolande Knell
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Middle East correspondent
- An wallafa
Bidiyon wata malamar makaranta mai rawa da ƙugu a Masar da ya yadu a shafukan sada zumunta ya haifar da zazzafar muhawa dangane da hakkin mata a kasar da ake kallo a matsayin mai tsauraran dokokin da suka shafi rayuwa da zamantakewa.
Bayan yaduwar bidiyon sai mijin Aya Yousef ya sake ta, kana aka kore ta daga aiki. Wata abokiyar aikinta ce ta dauke ta bidiyon a wajen wani biki ba tare da sahalewarta ba.
Bidiyon ya nuna ta tana tiƙar wata rawa da ake karkaɗa ƙugu a kusa da wasu abokan aikinta malamai maza.
Wannan salon rawa ta ƙugu ta samo asali ne tun zamanin mulkin Fir'auna a Masar, kuma mutane da dama na takaicin yadda mata ke rawa a bainar jama'a.
Bidiyon ya nuna Ms Yousef wadda ke sanye da mayafi da riga mai dogon hannu, a hanyarta ta zuwa tafki da rana, bai yi kama da al'adun kasashen Yamma ba.
Kazalika, an yaɗa bidiyon sosai a shafukan sada zumunta a yankin Larabawa a makon da ya gabata, hakan ya jawo Allah-wadai a tsakanin masu ra'ayin riƙau na Masar.
Masu sukar matar dai na cewa ta yi abun kunya. "Wannan ya nuna ƙarara irin halin da muke ciki da kowa zai iya yin abun da ransa yake so!! Yanzu yin komai ya zama dai-dai kamar ba laifi ba ne," a cewar wani mai amfani da shafin tuwita.
"Yanzu darajar ilimi ta yi faɗuwar baƙar tasa a Masar" kamar yadda wani da ya yi sharhi a rubutun ya wallafa a ƙasa, inda ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su shiga lamarin.
Biyo bayan yadda jama'a suka yi ta sukar abin da ta yi, sai makarantar firamaren Dakahija da Aya ke koyarwa ta kore ta daga aiki, bayan shafe tsawon shekaru tana koyar da Larabci.
Ta lashi takobin cewa daga yanzu ba za ta sake yin rawa ba, kuma abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun sa ta tunanin kashe kanta.
"Minti 10 kacal a cikin jirgin ruwa don zuwa Kogin Nilu sun kusa zama sanadin rasa rayuawata," kamar yadda ta shaida wa ƴan jarida.

Asalin hoton, Getty Images
To amma suma a nasu bangaren masu kare hakkin mata a Masar sun yi martani dangane da wannan al'amari, suna cewa malamar ba aikata komi ba.
A wani martani da zummar goya mata baya, ita ma mataimakiyar shugabar wata makaranta ta wallafa nata bidiyon tana rawa a wajen bikin 'yarta.
Ita kuwa shugabar kungiyar kare hakkin mata ta Masar Dr Nihad Abu Qusman, ta yi wa Aya tayin sabon aiki ne a ofishinta, sannan kuma ta buƙace ta da ta shirya kai ƙara kotu don ƙalubalantar matakin da aka ɗauka na sallamar ta daga bakin aiki.
A halin da ake ciki dai mahukunta a yankin da matar take sun ba ta sabon matsayi a wata makarantar ta daban.
Malamar dai ta ce an shiga huruminta ta hanyar nadar abin da ta yi cikin sirri ba a bainar jama'a ko gaban ɗalibanta, don haka za ta maka wacce ta naɗi bidiyon a watan da ya gabata a kotu.











