Sabuwar shekarar 2022: Yaya mutane suke tarbon sabuwa shekara a sassan duniya?

An wallafa

Matukar murnar bikin sabuwar shekara da za a yi a fadin duniya a daren ranar 31 ga watan Disamba zai faru ne da cikar 12:00 na safe, sai dai bikin ba za a yi shi bai daya ba, zai sha banban saboda lokuta da suka banbamta.

Amma da zarar lokacin ya yi, tsarin sabuwar shekara shi ne fatan ta zo da abubuwa masu kyau.

Ga yadda mutane ke bikin tarbon sabuwar shekarar a fadin duniya.

Wasan wuta

Daya daga cikin hanyoyin da ake yin murnar sabuwar shekara shi ne yadda ake harba wuta mai tartsatsi.

Ana yin wannan a fadin duniya baki daya, sai dai mafi yawan kasashe na da banbancin lokacin da ranar 31 ga watan Disamba ke karewa.

A New Zealand, Inda ake fara bikin sabuwar shekara - Wannan waje na Auckland Sky na daya daga cikin wurare da ake wasa da wuta cikin kayatarwa, kuma irin haka ne ke faruwa a birnin Sydeny a Australia.

A Rio de Janeiro da ke Brazil inda nan Copacabana yake ana wasa da wuta, haka ma a Hong Kong a filin Victoria Harbour da Dubai inda ake wasan gani a fada a Burj Khalifa.

Fasa balo

A birnin New York da ke Amurka, dandalin Square Times nan ne cibiyar da ake zama domin jiran sabuwar shekara.

Amma abin da kowa yake kallo a mafi yawan lokaci fasa katon balo da ake makalawa a sama.

A sakamakon haka, birane da dama suna yin nasu salon na sauke balon din kamar yadda ake yi a yammacin sabuwar shekara.

A Vincennes da ke Indiana, mutane na jefo kankana daga sama!

A wannan shekarar akwai dokokin annobar korona da aka sanya, an hana tarukan mutane da dama a fadin duniya, wasu kuma takaita yawan mutanen da za su halarta aka yi. Amma akwai tara da za a ci duk wanda ya karya dokar yayin wannan biki.

Fasa rumman

Ruman a Girka da Turkiyya wata alama ce da bunkasar arziki da yalwa. Kamar yadda aka saba mutane da dama a wadannan kasashe na fasa ruman a kofar gida je a matsayin murnar bikin sabuwar shekara da fatan kyakkyawar nasara.

Kada kararrawa

A kasashe irinsu Japan da Korea Ta Kudu kada kararrawa ana yin sa ne a farkon ko wacce shekara.

A Japan ana kada kararrawar ne sau 108, don haka ana sa ran ta cika ko ina da ihu.

Fasa kwanika

Idan ka fito harabar kofar gidanka, ka tsinci tangarai ya fashe, za ka shiga ruɗani.

Amma abin da mutanen Denmark suke fatan yi a tsakiyar dare, domin hakan na nufin fatan alheri.

Don haka idan kai ɗan Denmark ne, za a ka iya zuwa ka farfasa kwanon tangarai a ƙofar gidan abokinka yi masa fatan alheri a tsawon wata 12.

Waken lentils

A Brazil, akwai al'adar cin waken Lentil a ranar sabuwar shekara, wanda wannan na nufin kudi - ma'ana fata mai kyau a shekara mai zuwa.

Inibi 12

Lokacin da 12 ta yi a Spain, za ka samu mutane suna neman inibi.

Saboda wannan al'ada ce ta cin inibi ɗaya duk lokacin da agogo ya kai ƙarfe 12

Wannan na nufin zai kawo wa mutum fata mai kyau a wata 12 na shekara mai zuwa.

Shiga irin ta dabbar bear

A Romania, akwai al'adar da mutane suke yi ta yin shiga irin ta dabbar bear domin kawar da duk wani mugun abu

Saboda wannan wani abu ne mai muhimmanci a cewar labaran Romania kuma yana kare mutane da warkar da su.

Tafiya da akwati ba komi ciki

A ƙasashen kudancin Amruka, za ka ga wasu mutane a jajibirin sabuwar shekara suna tafiya ɗauke da akwati ba komi cikinsa.

Wasu sun yi imanin cewa ɗaukar akwanin ana tafiya yana nufin mutum zai riski shekara cike da abubuwa.

Watsi da kayan gida

A Johannesburg a Afirka Ta Kudu, mutane suna fara shekara ne ba tare da duk wani abu da ba su so.

Wasu na yin haka ta hanyar watsar da kayayyakinsu musamman kujeru ta taga.

Amma bikin bai tsaya kawai a ranar 1 ga Janairu ba.

Kyautar kuɗi

Ana kiran wannan yawanci "kuɗin sa'a" kuma ba yara da kanana a dangi da manya ke yi a farkon shekarar China da ƴan Koriya da Vietnam.

Yadda ake bayar da kuɗin ya banbamta tsakanin al'adu. Launin ja na mutanen China ne, yayin da ƴan Koriya yawanci suke saka kuɗin cikin takarda su rufe a rubuta sunan yaro a ciki.

Wasa da ruwa

Wasa da ruwa da jiƙe juna daga daga cikin bukukuwan farkon shekara a Thailand musamman mutanen Songkran da Thingyan na Myanmar.

A Thailand ana amfani da bindigar ruwa, kuma yara sukan yi wasan da manya inda suke wanke hannu da kafafunsu a matsayin nuna girmamawa.

A Myanmar mutane kan fito kan titi suna wasan ruwa domin murnan sabuwar shekara.

Wasa da ruwan na nufin wanke duk wani mugun abu daga shekarar da ta gabata zuwa sabuwar shekara.

Dabino

Kiristoci a Masar na murnar sabuwar shekara a watan SAtumba kuma ɗaya daga cikin al'adarsu shi ne cin dabino mai launin ja.

Jan dabino yana wakiltar jini, farin cikinsa yana wakiltar tsarki, kuma ɗan dabino yana wakiltar ban gaskiya.

Sauran kasashen duniya na iya kasancewa cikin yanayin liyafa a jajibirin sabuwar shekara, amma wasu al'adu suna ɗaukarsa a matsayin lokacin duba.

Sabuwar Shekarar Musulunci - a watan Yulin wannan shekara - ana daukarta a matsayin ranar hutu a mafi yawan al'ummar musulmi amma ranar farkon ta na kunshe da ayyukan addini.

Musulmai suna yin addu'a tare da abokai da dangi kuma wasu na iya yin azumin kwanaki goma na farko.