Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ashraf Ghani: Tsohon shugaban Afghanistan ya fadi dalilin tserewa daga kasar
Tsohon shugaban Afghanistan ya kare matakin da ya dauka na tserewa daga kasar lokacin da Taliban ke nausawa domin kwace mulki a farkon wannan shekarar, yana mai cewa ya yi hakan ne don kare birnin Kabul daga rugujewa.
Kungiyar Taliban ta kwace iko a cikin watan Agusta bayan karbe babban birnin.
Ashraf Ghani ya bayyana cewa ya wayi gari a ranar 15 ga watan Agusta da bai taba tunanin ita ce ranar shi ta karshe a kan mulkin Afghanistan ba.
A daidai lokacin da jirginsa ya bar birnin Kabul ne na fahimci lallai cewa zan fita daga kasar, Mista Ghani ya bayyana haka a wani shirin BBC na Radio 4.
An yi ta sukar lamirinsa tare da zargin barin kasarsa a daidai lokacin. Yanzu haka yana zaune a Hadaddiyar Daular Larabawa.
Misat Ghani ya furta wadannan kalamai ne a wata tattaunawa da Janar Sir Nick Carter, tsohon Hafsan Sojin Birtaniya a cikin shirin na ranar Alhamis.
Da wayewar gari, Mista Ghani ya tuna, mayakan Taliban sun yanke shawarar ba za su shiga birnin Kabul ba- "amma bayan sa'oi biyu batun ya sauya."
"Bangarori biyu na Taliban na tunkarowa daga wurare biyu daban-daban,'' Mista Ghani ya bayyana. ''Kana alamu suka nuna karara cewa arangama tsakaninmu da su za ta lalata birnin mai mutane miliyan biyar tare da haifar da damuwa a tsakanin al'umma."
Ya yanke shawarar barin mai ba shi shawara kan harkokin tsaron kasa kana ya fice daga birnin Kabul tare da mai dakinsa, inda ya jira motar da za ta kai shi zuwa ma'aikatar tsaro.
Motar ba ta zo ba. A maimakon haka, ''cikin firgici'' babban jami'in tsaro a fadar shugaban kasa ya zo ya sanar cewa muddin Mista Ghani ya dauki wani mataki, ''za a kashe dukkanninsu''.
"Bai bayar da fiye da minti biyu ba,'' Mista Ghani ya ce. ''Umarnin da na bayar shi ne a shirya ficewata zuwa birnin Khost. Ya kuma bayyana min cewa birnin Khost ya fada hannun Taliban har ma da birnin Jalalabad.
"Ban san inda za mu do saba. Sai lokacin da muka tashi sama be, na fahimci cewa muna barin kasar [Afghanistan]. Don haka wannan a gaggauce ne."
Bayan da ya bar kasar, Mista Ghani ya fuskanci suka ta ko ina a kasar Afghanistan da suka hada da mataaimakin shugaban kasa Amrulla Saleh, wanda ya kira hakan da ''abin kunya''.
Sharhi - Lyse Doucet, babbar 'yar jarida kan kasashen duniya
Ba a rana daya ne Taliban ta karbe iko ba. Amma da dama na jadadda cewa ficewar Ashraf Ghani cikin sauri a asirce a ranar 15 ga watan Agusta ya yi nuni da wata yarjejeniya ce, wacce aka yi, don mika mulki cikin sauki.
Ko ta halin kaka, Taliban za su iya mamayewa. Amma kuma kafar da mutumin da ya sha lasar takobin '' sadaukar da ran sa'' ya bayar, ta kara haifar da rudani. Kana fiye da abinda ya aikata a ranar 15 ga watan Agusta, mutane da dama na zarginsa kan abinda ya kasa yi a cikin shekaru kafin nan.
Gaskiya ne Amurkawa sun saka shi a hanya, amma ya yi amfani da damar da mummunar hanya.
Yanzu ana yi masa kallon shugaba fiye da dan siyaasa, wanda ya kasa karantar siyasar Amurka da kuma halin da ake ciki da suka hada da batun Taliban.
Za a dauki lokaci mai tsawo ana tattaunawa da sharhi game da labarinsa na baya-bayan nan.
Zarge-zargen cewa Mista Ghani ya kwashi makudan kudade shi ma ya bulla - abinda yake ta musantawa, tare da kiran da a gudanar da bincike na kasa da kasa cewa hakan ne zai wanke kan sad aga zargin.
"Ina son in bayyana karara cewa, ban kwashi wasu kudi daga kasar ba,'' ya ce, ya kuma kara da cewa: ''Tsarin yanayin rayuwata sanannen abu ne ga kowa. Me zan yi da kudin?"
Mista Ghani ya amince da kura-kuran da ya aikata, da suka hada da ''hakurin kasashen wajen zai dore.''
Amma kuma, ya yi nuni da cewa yarjejeniyar da aka yi tsakanin kungiyar Taliban da Amurka a karkashin tsohon shugaba Donald Trump, wacce ta bude hanyar abubuwan da suka faru ranar 15 ga watan Agusta.
"A maimakon tattaunawar zaman lafiya, mun samu tsarin janyewa,'' Mista Ghanai ya bayyana. Yadda aka gudanar da yarjejeniyar,'' in ji Mista Ghani,'' ya goge mu''.
A karkashin tsarin yarjejeniyar, Amurka ta amince da rage yawan dakarunta da na kasashe kawayenta, da kuma samar da tsarin musayar fursunoni - bayan da kungiyar masu tayar da kayar bayan ta amince da gwamnatin Afghanistan.
Tattaunawar ba ta yi amfani ba: a lokacin bazarar shekarar 2021, tare da alkawarin shugaban Amurka Joe Biden na janye tawagar karshe t dakarun zuwa 11 ga watan Satumba, 'yan Taliban na ta kutsawa fadin kasar Afghanistan, suna ta kwace birane.
Abubuwan da suka faru daga karshe, Mista Ghani ya bayyana, shi ne ''mummunan juyin mulki, ba yarjejeniyar siyasa, ko tsarin siyasa ba inda aka saka mutane ciki''.
A ranar da Mista Ghani ya fice daga birnin Kabul, kungiyar Taliban ta karbe mulki. Tun bayan wannan lokaci, kasar ta shiga matsanacin tashin hankali da durkushewar tattalin arziki wanda ya kara ta'azzara saboda janye tallafin kasashen waje bayan da kungiyar ta karbe mulkin.
Watanni uku da suka gabata, Mista Ghani ya bayyana cewa a shirye yake ya dauki alhakin aikata wasu abubuwa da suka haddasa kwace birnin Kabul - kamar na yarda da "hadin guiwar kasa da kasa".
Amma kuma, ya kara da cewa: "Ayyukan rayuwata sun lalace. An zubar min da kima da mutuncina. Kana an yi amfani da ni."