Aisha Zaki da Sudeenly: Rigimar TikTok ta janyo zubar da jini

Aisha Zaki and Sudeenly: How Arewa Tiktok challenge lead to physical beating for Kano

Asalin hoton, Suddenly and Aisha Zaki

An wallafa

Mummunan rikici ya ɓarke tsakanin wasu fitattun 'yan Tiktok a arewacin Najeriya, Aisha Zaki da Suddenly abin da ya kai har da zubar da jini tsakani.

Wannan kuwa na zuwa ne bayan wani bidiyo da ya rika yawo a Manhajar Tiktok kamar kwanaki biyar baya, wanda ya nuna wasu mata suna dukan Suddenly a wani gida da ake cewa gidansu ne.

Tiktok

Asalin hoton, Tiktok

Bayanan hoto, Suddenly a daya daga cikin bidiyoyinta da suka fi samun shahara

Cikin bidiyon an ji wata mata na cewa "dan rashin mutunci a gaban uwatta" ita kuma Suddenly bayan an shaketa tana cewa "Mama".

Wannan bidiyo ya janyo cece-kuce tsakanin 'yan Arewa masu amfani da wannan manhaja.

Daga baya Aisha Zaki ta saki wani bidiyon cikin farin ciki tana cewa Suddenly ba ta ga komai ba, yayin da ita kuma Suddenly a nata ɓangaren ta saki bidiyo tana cewa babu wata 'ya da take tsoro a Tiktok.

Ana cikin haka sai wani sabon bidiyo ya fito, cikin sa an nuno Aisha Zaki jina-jina da rauni a goshinta, ana kuma jin muryar wata mata na cewa "Suddenly ce ta sa aka yi mata haka, Suddenly 'yar fashi ce".

TIKTOK

Asalin hoton, AISHA ZAKI TIKOK

Bayanan hoto, Hoton da ke kan shafin Aisha Zaki kenan a Tiktok

Wannan bidiyo ya fara janyo magana tsakanin masu amfani da shafukan sada zumunta a arewacin Najeriya, inda suke tofa albarkacin bakinsu kan cewa abubuwan da ke faruwa tsakanin wannan mata sun fara wuce gona da iri.

Rikicin da ke tsakanin wadannan mata ba yau ya fara ba, sun kusa sama da shekara suna sa'insa tsakaninsu, duk da cewa wannan rikici ya fara ne daga irin kalubalen da yake tashe tsakanin masu yin Tiktok.

Duka matan biyu suna da mabiya sama da 250,000 kuma suna yawan samun wadanda ke nuna kauna ga bidiyon da suke sanya wa a shafukan nasu.

A wasu lokuta kuma sun rika rikici ne kan wanene ya fi wasu mabiya da samun da kuma samarin da suke mu'amala da su.

Sai dai wannan rikici bai tsaya iya wadannan mutane biyu ba a gefe guda akan samu masu bin bayan ko wacce daga cikin Aisha da Suddenly.

Wasu na ganin "alfahari da ji da kai da jin babu wanda ya isa ko ya kai ni, shi ne asalin abin da yake janyo wadannan rikice-rikice."

Sunddenly na da wasu abokan rikicin da babu abin da ya hada su da Aisha Zaki.

Tiktok

Asalin hoton, Tiktok

Bayanan hoto, Maizool ita ce daya daga cikin wadanda suka fi yawan rikici da Suddenly a Tiktok mazauniyar Saudiyya

Maizool na daya daga cikin matan Arewa da ke amfani da Tiktok kuma suka yi ƙaurin suna wajen rikici da Suddenly.

Mazauniyar Saudiyya ce, wadda kuma daga can ne suke sa'insar da suke yi da abokiyar rikicinta, a mafiyawan lokaci suna zama inuwa daya da Aisha Zaki saboda suna da abokiyar rigima guda.

Sun fara rikici ne da Suddenly, wani lokaci da Suddenly ta dauki jaka ta ce za ta koma Saudiyya da zama, wata murya ta nuna cewa me zaki je ki yi bayan kina da komai a Najeriya, sai Suddenly ta ce za ta je neman "Haja" ne.

Mazauna Saudiyya sun rika mayar mata da martani saboda yadda suka fahimci bidiyon tana musu yafuce ne kan cewa zaman da suke yi ba halattacce ba ne.

Masu amfani da Tiktok 'yan Arewacin Najeriya mazauna Saudiyya irin su Mai Zool da @Hajarayahaya da @MunnaMusa da dai makamantansu.

Tiktok

Asalin hoton, Tiktok

Bayanan hoto, @Daddylola2 namiji ne da yake yunkurin nemar wa wadannan mata da ke rikici da juna mafita a baya

Daddylola2 ya yi kaurin suna wajen tsoma bakin rikicin wadannan mata, a kwana a tashi sai kawai aka ji shi yana zagin Suddenly wani lokaci.

Lokacin da rikicin wadannnan mata ke ƙamari yakan hada su duka ya zaga a matsayin babba wanda ke taka rawar mai tsawatarwa a tsakaninsu.

Duka wadannan mutane suna da alaƙa kai tsaye da rikicin Aisha Zaki da Suddenly.

Me ake yi a Tiktok

Manhajar Tiktok manhaja ce da aka kirkira domin nishadi, akan sanya bidiyon fitattun mutane suna waka ko rawa ko kuma wani bayani da za a kwaikwaya domin nishadi.

Wasu mutanen su suke kirkirar abinsu kuma ya samu karbuwa tsakanin mabiyansu da wadanda ba mabiyansu ba.

Masu amfani da shafin na yawan kokawa da yadda ake samun rikici tsakanin masu amfani da manhajar a Najeriya musamman a Arewacin kasar, ta yadda ake zage-zage da fada da juna.

A wasu lokutan kuma idan mace ta sanya bidiyonta na nishadi sai a yi ta zaginta ana ci mata mutunci, abin da yake hana wasu da yawa ci gaba da amfani da wannan manhaja kenan.

Wasu da yawa sukan buɗe shafin ba tare da sa komai ba kuma ba za su bi kowa ba babu wanda zai bi su.