An tuhumi wata mace mai ciki da hannu a kai harin ta’addanci a Uganda

Mutane hudu ne suka mutu kana fiye da 30 suka samu raunuka bayan hare-haren kunar bakin wake uku a birnin Kamfana cikin watan Nuwamba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutane hudu ne suka mutu kana fiye da 30 suka samu raunuka bayan hare-haren kunar bakin wake uku a birnin Kamfana cikin watan Nuwamba.
An wallafa

Wata kotu a kasar Uganda tana tuhumar mutane 15 - da suka hada da wata mai juna biyu - da hannu a hare-haren ta'addanci da aka kai a ƙasar.

Akasarin wadanda ake tuhumar an zarge su ne da kasancewa 'yan kungiyar Allied Democratic Forces (ADF) ta masu rike da makamai wacce ke da alaka da kungiyar IS mai da'awar kafa Daular Musulunci.

Mahukuntan sun ce kungiyar na da hannu a hare-haren bama-baman da suka faru a baya bayan nan.

Kasar Uganda ta kaddamar da farmakin soji kan kungiyar ta ADF a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo makwabciyarta.

A shekarar 1990 ne wasu 'yan kasar Uganda da suka fusata da yadda gwamnati ke yi wa Musulmai suka kafa kungiyar masu tayar da kayar bayan, amma aka fatattake su daga sansanoninsu a yammacin tsaunukan yankin Rwenzori, inda mayakanta suka rika kai farmaki kan kauyuka tare da kone makarantu a farkon shekarar ta 2000.

Hare-haren a cikin watan Oktoba da harin kunar bakin wake uku a Kampala babban birnin kasar cikin watan Nuwamba ya tayar da mahukunta tsaye game da sauya salon da kungiyar ta yi.

Yan sanda sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mutane 15 da ake zargi na fuskantar tuhume-tuhume kan ta'addanci, da haddasa ayyukan ta'addanci, da kasancewa cikin kungiyar 'yan ta'adda, kuma za a c igaba da tsare su har ya zuwa lokacin da za su sake bayyana a gaban kotu a ranar 13 ga watan Janairu.

Wadanda ake zargin ba su shigar da batun daukaka kara ba.

A farkon wannna watan ne Jumhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta amince da bukatun kasar Uganda na ta kaddamar da farmaki da suka hada hare-hare ta sama da ta kasa a gabashin yankin a kan masu tayar da kayar bayan na ADF.