Fashewar bama-bamai a Kampala: Abubuwan fashewa sun tashi a babban birnin Uganda

Wata mace na lallashin wata a kusa da inda abin ya fashe a birnin Kampala na Uganda ranar 16 ga watan Nuwamba 2021

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mutane sun firgice da jin karar fashewar abin
An wallafa

An tayar da wasu abubuwan fashewa guda biyu a Kampala, babban birnin Uganda, lamarin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutum shida, a cewar hukumomi.

Daya daga cikin abubuwan fashewar ya tashi ne a kusa da majalisar dokokin kasar, yayin da dayan ya tashi a kusa da hedikwatar rundunar 'yan sandan kasar.

Ana yi wa mutum akalla 33 da suka jikkata magani a asibiti, a cewar ma'aikatar lafiyar kasar. Ganau sun ce abubuwa sun dagule a wurin da lamarin ya faru, inda motoci suka kama da wuta yayin da wunduna suka tarwatse.

Har yanzu ba a san abin da ya yi sanadin fashewar ba amma hukumomi a Uganda sun dora alhakin irin wannan fashewa da ta faru a baya a kan masu ikirarin kishin Musulunci.

Dakarun sojin Uganda na cikin kawancen sojojin wanzar da zaman lafiya na Tarayar Afirka da ke yaki da kungiyar masu tayar da kayar baya ta al-Shabab mai alaka da al-Qa'ida a Somaliya.

A watan da ya gabata, kungiyar ta dauki alhakin harin da aka kai wata mashaya da ke birnin Kampala, lamarin da ya rutsa da wata matashiya mai shekara 20.

An bai wa 'yan majalisa shawarar kaurace wa ginin majalisar saboda harin da aka kai na ranar Talata.

Wani dan sanda Edward Ochom ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa motocin da ke wurin ajiye motoci a farfajiyar majalisar sun kama da wuta a lokacin da abin fashewar ya tashi a kusa da ofishin 'yan sanda, inda tagogin gilashi suka tarwatse.

"Abin da kawai za mu ce, an kawo hari ne, amma ba mu san wanda ya kawo shi ba, amma muna gudanar da bincike kan lamarin," in ji Ochom.

Kakakin ma'aikatar lafiya Ainebyoona Emmanuel, ya ce hudu daga cikin wadanda aka kawo asibiti domin duba lafiyarsu na cikin mawuyacin hali.