Hikayata 2021: Labarin 'Ramat' da ya zo na uku

An wallafa

Wannan labarin haƙƙin mallakar BBC ne. Ba a yarda wani ko wata su yi amfani da shi ta ko wane salo ba, ko da yaɗa shi ne ta shafukan sada zumunta. Idan aka yi hakan kuma, to BBC za ta ɗauki mataki har da na shari'a.

RAMAT

Ramat ita ce mace ta farko a ƙauyensu, da ta gama digiri ta shiga aikin ɗan sanda. Yayin tirenin, ta haɗu da Mahmud, wanda ya zama tamkar abokinta. Ta ɗauki hankalin Mahmud a yadda take kame kanta. Ba ta wasa da ibada, ta kuma mai da hankali. Mafi yawan haɗuwarsu masallaci ne ko cikin aji. Ta haka suka shaƙu.

Mahmud ɗan jihar Katsina ne, Ramat kuwa 'yar jihar Kano ce da ta canja tunaninsa; game da mace a aikin ɗan sanda.

Ranar bikin yaye sababbin jami'ai, wato 'Passing-out Parade', Mahmud ya bai wa Ramat mamaki; ya bayyana soyayyarsa da zancen aure a gare ta. Ramat ta amince masa. Sai dai kuma kash! Aka kai ta jihar Ikko, shi kuwa a Maiduguri.

Tsawon lokaci, aure ya kankama, iyayen kowannensu na da masaniya. Hukumar 'Yan sanda ta ba su zaɓin jihar da suke son aiki, don su kasance a tare.

"Ramat, ina ya kamata mu zaɓa?" Mahmud ya ce wa amaryarsa.

Ta ce, "Ofisa, kai ne ya kamata ka zaɓa mana". Ba ta kiran sunansa.

"Ina sha'awar jihar Kaduna"

Ramat ta ce, "Ni ma hakan". Dukansu suna dariya.

A ranar aure, an ci, an sha, an yi fareti gwanin ban sha'awa. Ango da amarya ma tufafin farati na musamman suka sanya.

Bayan Aure, Ramat da Mahmud sun jima ba su haihu ba, abin damuwa, da ya kai zuwa asibiti don gano bakin-zaren.

A kwana a tashi, Ramat ta samu juna-biyu. Mahmud baki har kunne! Soyayyar da ke tsakaninsu ta ƙara ƙarfi. Ramat ta haifa masa ɗa kyakkyawa, da aka raɗa masa suna Yusuf.

Yusuf ya kasance tozali ga iyayensa. Yaro ya tasa, aka sa shi makaranta. Sun kashe maƙudan kuɗi wajen zaɓa masa makarantun da suka dace, har ya kammala sakandare, aka nema masa 'adimishin', don yin digirinsa na farko a Ingila.

Iyayen sun haɗa ƙarfi da ƙarfe domin tabbatar da tarbiyarsa, har lokacin da ya kammala jami'a, ya dawo gida Najeriya.

Paulina ce yarinyar da ke yi wa Ramat hidima, ta shirya ɗakinsa. Aka yi masa tuwon-shinkafa da miyar-kuka, abincin da ya fi so. Daga Kaduna International Airport, aka ɗauko shi, sai gida.

An sake dawowa da Ramat da Mahmud Kaduna ne, bayan da suka yi aiki a wurare da jihohi daban-daban, suna ta samun ƙarin-girma.

Bayan wata ɗaya, Mahmud ne ya fara dawowa daga aiki, ya tarar da Paulina kwance, a cikin wani mummunan yanayi, da ba ta iya magana. Ba a yi minti biyu ba, Ramat ta shigo.

"Me ya faru da ita?!"

"Shigowata kenan!".

"Yusuf!"

Ramat ta ƙwalla wa Yusuf kira, ya fito.

"Me ya faru da Paulina?!" Ta tambaye shi. Ya ce bacci yake, bai san abin da ya faru ba.

Jin haka, Ramat ta wuce ɗakinta. Ta soma duba CCTV (Na'urar ɗaukar hoto ta sirri), a saƙo-saƙo na gidan…

A ɗakin Yusuf, tsigar jikinta ya tashi, ta kai zaune tana kuka… Ta kira Mahmud, ya zo, ta nuna masa— Yusuf ne ke yi wa Paulina fyaɗe!

Cikin kuka, Ramat ta ce, "Inspector, ku zo gidana akwai…". Mahmud bai san lokacin da ya fizge waya hannunta ba! Jikinsa na rawa, ya ce, "Are you mad?! Kin san abin da kike kuwa?!"

Ramat ta ce, "Yana da bambanci da wasu 'ya'ya ne?"

"Kwarai kuwa! Yusuf jininmu ne", in ji Mahmud.

"Ofisa, ka bar ni na yi aiki!"

"Dakata ki ji! Idan kika sake maganar nan ta fita…, wallahi abu mafi muni zai faru a tsakaninmu!"

Shekaru 25, wannan ita ce magana mafi zafi a tsakaninsu.

Paulina dai, ba musulma ce ba! Wata yar maƙwabta ce, maraya, Ramat ta ɗauko. Ba ta yi la'akari da yare ko addini ba, take ɗaukar nauyin karatunta. Yarinya ta gama sakandare, sakamako ake jira, hakan ya faru. Bin ra'ayin Mahmud bai zama cin amana ba?

Aure darajar 'ya mace! Mace aka fi sani da son ɗa fiye da mahaifinsa; ciwon 'ya mace na 'ya mace ne; binne matsalar nan, ba a yi wa aiki ga ƙasa adalci ba. Da wane ya kamata Ramat ta ji?

Tabɗijam! Ramat ta yi fushin da ba ta taɓa yin irinsa ba! Ta wuce ta bar Mahmud a tsaye. Tana zuwa falo, ta samu Yusuf. Zai yi magana, ta kwashe shi da mari! Zai buɗe baki, ta sake marin sa!

Ganin haka, Mahmud ya gudu ya koma ɗakinta, ya goge dukan wata shaida da CCTVn ya naɗa. Yana mai cewa a ransa,

"Me 'ya mace ke ji, idan aka yi mata fyaɗe, ko aka yi wa 'yar'uwarta?"

Yana cikin haka, sai dai kawai ya jiyo Ramat na cewa, "Arrest him! Ku kama shi na ce!"

"Inspector, ku sake shi!" In ji Mahmud.

"Yes, sir!" Sufeton ya sara masa.

A tsarin aikin ɗan sanda, Ramat da Mahmud waye a gaba? Lambar Ramat ce ta gabaci tasa. Don haka, umurnin Mahmud bai yi tasiri ba. Suka tasa ƙeyar Yusuf, Mahmud na biye da su, har suka sanya shi mota, bai iya ya hana su aikinsu ba. Abin da ke faruwa gidansa ya wuce tunaninsa!

Ramat da ke ta kuka, ta ɗauki Paulina zuwa asibiti. Aka yi dukan abin da ya dace, ba a samu bakin Paulina ba, aka ba ta gado.

Wannan wutar da ta kunno kai, ta ja hankalin 'yan'uwan daga kowane ɓangare. Aka taso ta gaba! Matsi ta ko'ina! An kasa goyon bayan tsattsauran matakinta.

Da rana take aiki, dare ya kama, ido ya ce bai san bacci ba. Allah Sarki, ɗa da mahaifi! Duk dare na Allah, haka Ramat take, ba ta bacci, sai kuka, tana duban makomar ɗanta, da aikinta da kuma halin da Paulina ke ciki. Ga shi kuma, sun raba ɗakin bacci da Mahmud! Hakan ya haddasa mata ciwon zuciya, da a yanzu take fama da shi.

Ta ɓangaren Mahmud kuwa, duk abin da mahaifi zai yi don kare ɗansa, ya yi. Kama daga barazana ga matarsa; lalata bidiyon CCTV, da ƙoƙarin daƙile maganar a matakin 'yan sanda. Haƙarsa ba ta cimma ruwa ba, kasancewar tsayuwar Ramat kan koyarwar Allah da ManzonSa:

"Idan kuka tashi yin hukunci, to, ku yi adalci ko da a kan kawunanku ne".

Mahmud ya ɗaukar wa Yusuf ƙwararren lauya. Idan ta san wata, ba ta san wata ba!

Ranar Juma'a tunda safe, mutane ke tururuwa zuwa High Court, da ke Bida Road, Sabon Gari, Kaduna, don sauraron shari'ar da aka ce uwa ce da kanta ke ƙoƙarin ganin an yanke wa ɗan da ta haifa, tilo, ake zargin sa da yin fyaɗe hukunci.

Zaman farko, Yusuf bai karɓi laifinsa ba. Aka ɗaga shari'ar zuwa 2/12/2002, tare da umurtar ci gaba da tsare shi, yayin da ɓangaren mai gabatar ƙara, zai gabatar da shaidunsa. Ramat na fitowa 'yan jarida suka yi mata ca!

"Yallaɓai, ke kika haifi Yusuf, ko ɗan kishiyarki ne?"

"Ɗana ne".

"Bisa kiraye-kirayenku na a riƙa zartar da hukuncin kisa ko dandaƙe mai fyaɗe, ba kya tsoron idan kuka ci nasara, zargin da ake masa ya tabbata, za ki rasa ɗanki?"

"Ba kwa ganin Paulina ta rasa martabarta?"

"An ce Paulinar nan ba musulma ba ce, kike ta goyon bayanta".

"Maganar 'ya mace ake ba zancen addini ba".

"Yallaɓai, mene ne ainihin abin da kike son cimma a wanna shari'ar?"

"Adalci! Yaƙin da muka sa a gaba, ta'addancin da ake yi wa 'ya'ya mata, da gaske muke. Ba sani, ba sabo!"

"A yanzu, wane hali Paulina ke ciki?"

"Tana kan jin sauki.

"Yallaɓai, wai da gaske ne aurenku ya mutu?"

Ramat ta fara tari. Ta sa hankicif ta rufe bakinta. 'Yan jarida na biye da ita, har ta shiga mota, ba ta daina tarin ba.

Rana ba ta ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya! Kotu ta cika maƙil da jama'a, har wasu na ƙwalla. Muryar Paulina suka ji. (An killace ta), a sa'ilin da take bayani.

Bayaninta bai isa ba, aka gabatar da wasu shaiduka. A ciki har da bidiyon nan da CCTV ya naɗa, da rahoton asibiti, da ya tabbatar an yi mata fyaɗe.

Ta yaya bidiyon da aka goge ya bayyana? Sanin makamar aiki. Tun can farko, Ramat ba ta kira Mahmud ba, sai da ta tabbatar ta kwafe bidiyon a wayar salularta.

Wani nau'i daga burin Ramat ya cika! Sai dai kuma, ta samu saki biyu. Ma'ana Mahmud ya saki matarsa, an yanke wa Yusuf ɗaurin shekaru 15, da ba su taka kara suka karya ba.

Bayan wani lokaci, Mahmud da Ramat suka shirya, tare da mayar da aurensu. Sai dai kuma, an makara! Ramat ta shiga ciwon zuciya, da ya kai ga aman jini. Ashe son ɗanta na nan manne a zuciyarta!

Hukumar 'Yan sanda da wasu ƙungiyoyin mata na dab da karrama ta, da safe Ramat ta faɗi, aka ɗauke ta zuwa asibiti. Da yamma, ta ce ga garinku nan!

Mahmud ya yi kuka tamkar zai mutu!

Yusuf ya zama babban malami da ke koyar da Addinin Allah, bayan fitarsa daga kurkuku.

Duk sati yake ziyarar kabarin mahaifiyarsa don yi mata adu'a. Yana nadamar abin da ya aikata a baya.

Akwai abin da mahaifa, ko al'umma ke so da ya wuce wannan?