An saki sauran 'yan Mishan 12 da aka yi garkuwa da su a Haiti

An wallafa

An sako sauran 'yan mishan 12 da ke cikin wata tawaga da yawansu ya kai 17 da wani gungun 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a Haiti a watan Oktoba.

Mujami'ar Christain Aid Ministries ce ta tabbatar da hakan a shafinta na intanet.

A cikin makonni biyar da suka gabata ne aka ski mutum biyar da cikin ayarin.

Tawagar - wacce ta kunshi Amurkawa 16 da wani dan kasar Canada daya, ciki har da kananan yara, an sace su ne bayan da suka ziyarci wani gidan marayu da ke yankin da ke karkashin wata babbar kungiyar masu aikata laifuka.

Suna dawowa daga ziyarar ne wasu gungun 'yan daba suka kama motar bas da suke ciki a wani babban titi a garin Ganthier da ke gabashin babban birnin Port-au-Prince.

Ƙungiyar, wadda ta ƙunshi masu wa'azi a ƙasashen waje da iyalansu, sun haɗa da maza biyar, mata bakwai da yara biyar. Manya daga shekara 18 zuwa 48 ne, yayin da yaran duk 'yan kasa da shekaru 15 ne.

A lokacin da aka sace su ranar 16 ga watan Oktoba, jaridar Washington Post ta ruwaito cewa daya daga cikinsu ya wallafa sakon WhatsApp na neman taimako.

"Don Allah a yi mana addu'a! An yi garkuwa da mu, sun sace direbanmu, ku yi addu'a, ba mu san inda za su kai mu ba."

Kungiyar, wacce aka fi sani da 400 Mazowo, tana neman kudin fansa na dala miliyan 1 ga kowane mutum 17 da aka yi garkuwa da su.

An sako mutane biyu a watan Nuwamba, wasu uku kuma a farkon watan Disamba, amma ba a bayyana sunayensu ba.

A karshe dai an sako dukkan mambobin kungiyar watanni biyu bayan sace su.

Sakin na su ya biyo bayan tattaunawar makonni da aka shafe ana yi da wadanda suka yi garkuwa da su , kamar yadda kakakin 'yan sanda Gary Desrosiers ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP, abin da kuma ya kawo karshen al'amarin da ya jawo hankalin duniya kan matsalar sace mutane a Haiti.

Sai dai ba a san ko an biya kudin fansa ba, kuma ba a san abin da ya faru da direban kungiyar na Haiti ba.

Ƙungiyar masu aikata miyagun laifuka ta kasar Haiti

Satar mutane na daya daga cikin manyan ayyukan da kungiyar masu aikata laifuka ta Mazowo 400 ke amfani da su wajen samar da kudaden shiga.

A cikin watan Afrilu, mambobinta sun yi garkuwa da wasu limaman darikar Katolika da aka sako daga baya, kuma babu tabbas ko an biya kudin fansa.

Haiti tana daya daga cikin kasashen duniya da ake yawan sace mutane yayin da miyagun kungiyoyi masu karfi ke amfani da yanayin rashin bin doka don cin gajiyar biyan kudin fansa.

Wannan shekarar ta yi muni musamman, inda aka samu rahoton yin garkuwa da mutane kusan 800 kafin karshen watan Oktoba.

Hakan dai ya biyo bayan kisan gillar da aka yi wa shugaba Jovenel Moïse a watan Yuli, yayin da bangarorin da ke hamayya da juna ke fafutukar ganin sun mamaye kasar a kasar da 'yan sand aba su tabuka wani abin a zo a gani