Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amurka: Ƙasar ta juya wa dubban 'yan gudun hijira baya
Ma'aikatar tsaron cikin gida ta Amurka ta kwashe kusan mutane 2,000 daga wani sansani a wani gari da ke kan iyaka a Texas zuwa wasu cibiyoyin tsare 'yan gudun hijira da baki.
A cikin sama da kwanaki biyu da suka gabata kiyasin 'yan gudun hijira dubu goma zuwa goma sha biyu ne yawancinsu 'yan Haiti suka tuɗaɗa zuwa garin, kuma galibinsu sun je ne daga Latin Amurka a kokarin da suke na neman mafaka a Amurka.
Yayin da 'yan gudun hijirar da suka tattaru a karkashin wata gada a garin Del Rio na kan iyaka a Texas ke ta karuwa har zuwa sama da dubu goma, yanayin sansanin na wucin-gadi sannu a hankali ya fara tabarbarewa.
Kasancewar ba wata wahala sosai wajen tsallaka kogin da ke tsakanin Mexico da Amurka ta daidai wannnan wuri na kan iyaka, 'yan gudun hijirar da dama sukan koma Mexico su siyo abinci su koma.
Mafi yawansu 'yan Haiti ne amma kuma akwai 'yan Cuba da Nicaragua da Peru da 'yan Venezuela a cikinsu.
A yanzu gwamnatin Shugaba Biden na Amurka ta fara kwashe 'yan gudun hijirar daga sansanin, inda ta debe kusan dubu biyu zuwa wasu cibiyoyin tsare mutane da ke kan iyaka.
Ma'aikatar tsaron cikin gida ta Amurkar ta ce an dauki wannan matakan haka ne domin tabbatar da an ware 'yan gudun hijirar da ba su cancanta ba, a dana su, kafin daga bisani a fitar da su daga Amurka.
Jami'ai sun ce za a gaggauta kara samar da jiragen sama da za su mayar da 'yan gudun hijirar Haiti a kwanakin da ke tafe.
Kusan da yawa daga cikin 'yan gudun hijirar suna zaune ne a Brazil ko kuma wasu kasashen Latin Amurka sakamakon mummunar girgizar kasar da aka yi a Haiti a 2010.
Wasunsu kuwa wadanda suka je ne a kwanan nan a sanadiyyar illar da annobar korona da kuma rikicin siyasar kasar suka yi wa Haitin.
Haka su ma 'yan Cuba suna tserewa daga kasar tasu sakamakon matsalar tattalin arziki mafi muni da kasar ta taba samun kanta a ciki tun dan wani lokaci bayan yakin cacar-baka..
Da yawa daga cikin 'yan gudun hijirar a Texas kila sun yi tattaki ko tafiya mafi hadari a Latin Amurka ta hanyar ratsawa ta kungurmin dajin da ke tsakanin Colombia da Panama da kafa.
A ranar Alhamis wani alkalin tarayya ya dakatar da gwamnatin Biden daga amfani da doka ta 42, kan mayar da 'yan gudun hijirar, inda mai shari'ar ya ce dokar ba ta ba wa gwamnati ikon korar 'yan gudun hijira ko hana su damar neman mafaka ba.
Zuwa kwana goma sha hudu ne dokar za ta fara aiki, abin da ke ba wa gwamnatin damar daukaka kara a kan hukuncin.
Tun bayan da ya hau mulki, Shugaba Joe Biden, wanda ya lashi takobin yin gyare-gyare a tsarin shige da fice na Amurka, ya kafa wani kwamiti da zai hada 'ya'yan 'yan gudun hijira da iyayensu.
Sannan ya dakatar da aikin gina ganuwa da Donald Trump ya fara a kan iyaka da Mexico, sannan kuma ya nemi da a sake tsarin shirye-shirye na shige da fice da doka ta amince da su wadanda gwamnatin Trump ta soke.