Covid-19: Fiye da Amurkawa 800,000 sun mutu sanadiyyar Covid

Asalin hoton, Getty Images
Fiye da Amurkawa 800,000 sun rasa rayukansu ga annobar korona, alkaluma mafi yawa da aka samu daga kasa daya tun bayyanar annobar a fadin duniya.
Wannan mummunan labarin na zuwa ne yayin da Amurka ke cewa mutum miliyan 50 ne suka kamu da Covid-19 zuwa ranar Litinin da ta gabata.
Yawancin mamatan na daga cikin manyan mutane ne da ba su riga sun karbi alluran rigakafi ba, kuma Amurkawan da suka mutu a 2021 sun zarce na 2020.
Kawo yanzu Amurka na samin karuwar masu kamuwa da cutar, lamarin da ke tayar da hankula.
Alkaluman mutum 800,000 sun zarce yawan al'ummar birane kamar Boston ko Washington DC.
Sannan yawan Amurkawa da suka mutu ya zarce na dukkan sojojinta da suka mutu a yakin Duniya na Biyu.
Kasar da ke bi ma ta ita ce Brazil mai mamata fiye da 616,000, sai Indiya mai mamata fiye da 475,000.









