Wasu daga cikin kayatattun hotunan Afirka da wasu 'yan nahiyar da ke wasu kasashen.
Asalin hoton, EPA
Bayanan hoto, Ranar Lahadi a birnin Cape Town, na Afirka ta Kudu, lokacin zanga-zangar kare muhalli kan malalar man fetur na kamfanin Shell...
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, ...masu zanga-zangar tsare a cikin teku, inda kamfanin mai na Shell ke son ci gaba da hakar mai da iskar gas.
Asalin hoton, EPA
Bayanan hoto, Mai tallan kayan kawa Naomi Campbell da mai dinki 'yar Najeriya Banke Kuku (a tsakiya) lokacin nuna kayan kawa a Hadaddiyar Daular Larabawa ranar Lahadi...
Asalin hoton, EPA
Bayanan hoto, Mai tallan kayan kawa sanye da tufafin Najeriya samfurin Ziva, a birnin Lagos lokacin bikin kayan kawa.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, A ranar Laraba a arewacin kogin Nilu da ke Sudan, an dauki wannan sojan a hoto lokacin da sojoji suke atisaye.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, A ranar Talata, a kasar Habasha wani soja na sumbatar alamar Kuros, a wani wuri da ke karkashin UNESCO, da dakarun gwamnati suka karbe daga hannun 'yan tawaye.....
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, ... wani mutum yana karanta littafin Injila.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Mawakiyar Benineseta na waka a wajen bikin kalankuwar mawaka a Faransa ranar Lahadi.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Ranar Litinin a Gambia, wani mutum sanye da tufafin da ake kira mythical Kankurang tsaye a bakin ruwa.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Duk dai a Gambia ranar Juma'a, dandazon mutane mata da maza sanye da tufafi ruwan dorawa, a ranar karshe ta gangamin yakin neman zabe.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, A ranar Alhamis a dai Gambia, wannan mutumnin na janye da Sa ya na jiran a kawo abin da za a dauke shi.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Mutane akan layi a birnin Dakar a Senegal , sun bi layin ne domin karbar magani a ranar Talata.