Yadda ake gyara ƙwayoyin halitta don samar da macen ɓera

Beran da aka sauyawa kwayar halitta

Asalin hoton, Crick Institute

    • Marubuci, Daga Pallab Ghosh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Science correspondent
  • An wallafa

Masana kimiyya sun yi amfani da fasahar gyara kwayoyin halitta domin samar da macen bera daban da kuma namiji daban.

Dabarar da suka yi amfani da ita za ta taimaka wajen guje wa mutuwar dubban berayen da ba a bukata a binciken da ake yi.

Tawagar masana kimiyyar ta ce wannan dabarar ma za ta kare yadda ake yanka miliyoyin zakaru a Birtaniya saboda ba sa yin kwai.

Gwamnatin Birtaniya na duba yiwuwar kyale a rinka yin gyare-gyare a kan dabbobin gida a Ingila.

An tsara wannan dabarar ce domin a rinka samar da dan tayin mace ko namiji tun a farkon halittar sa.

Presentational white space

Masu bincike sun yi amanna cewa dabarar za ta iya aiki a kan dabbobin gida.

Dr Peter Ellis, na jami'ar Kent ya shaida wa BBC cewa, idan sakamakon wannan bincike da aka fitar da shi daga dakin gwaji zuwa hannun 'yan kasuwa hakan zai yi matukar tasiri ga rayuwar dabbobi.

Ya ce, " Ana yanka kaji tsakanin biliyan hudu zuwa biliyan shida a fadin duniya a duk shekara, bisa la'akari da haka zamu iya samar da wani tsari wanda a maimakon a rinka yanka kajin bayan an haife su alhali kuma suna da damar da za su iya yin kwai, sai a rinka amfani da kwan wajen samar da duk jinsin da ake so.

'Yan tsaki

Asalin hoton, DAVID AUBREY/SCIENCE PHOTO LIBRARY

Da farko yanzu an gano cewa sabuwar dabarar za ta rage yawan berayen da ake kashewa a dakin gwaji saboda dukkan berayen wala mace ko namiji ana bukatar a rinka yi musu gwaji ta yadda za a gano yadda za asamar da wata kwayar halittar daga jikinsu.

Dr James Turner, daga cibiyar Francis Crick a London, ya gano wasu mujallu dubu 25 da aka wallafa a cikin shekaru 5 da suka wuce wadanda ke bukatar a samar da mace ko namijin bera kadai.

Wani rahoto da aka wallafa a farkon makon da muke ciki, ya bayyana cewa, jin dadi da walwalar dabbobi yakamata ta kasance a zukatan jama'a ta yadda hakan zai bayar da damar a rinka sarrafa kwayoyin haliitarsu wajen samar da wasu.

Daya daga cikin wadanda suka rubuta rahotannin Peter Steveson, ya ce suna goyon bayan a inganta jin dadi da walwalar dabbobi, kamar tabbatar da cewa ana samar da kaji mata, saboda koda za a rinka yanka su to akwai wasu kaji matan da za su iya kyankyasa.

Ko da dabbobi masu haihuwa ne, to an fi son mata saboda kyankyasa.