Tartsatsin wuta a sama da bikin kayan ado a hotunan Afirka na mako: 26 November - 2 December 2021

An wallafa

Wasu kayatattun hotuna daga yankin Afirka, har ma da waje.

Short presentational grey line
Woman in red outfit standing behind a black wall. There is a red doorframe that matches her outfit

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Lahadi wata 'yar gudun hijira daga Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ta tsaya don yin hoto a birnin Rio de Janeiro da ke kasar Brazil...
A woman's two hands with several rings, holding a pink garment.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan 'yar gudun hijirar ta rike kayanta sosai...
A woman with a yellow headscarf posing under a tree with flowers.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata mata yayin da ta tsaya don yin hoto a karkashin wata bishiya.
A ballet dancer standing on pointe in front of a crowd of people outside. The skies are cloudy with some blue creeping through.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A Lahadin, wata mai rawar ballet na atisayenta gabanin shirin rawar Nutcracker.
Babou Ngom playing a drum-like instrument with a drum stick in the air. He is smiling. Others around him are performing and visibly having a good time.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A Senegal ma akwai raye-rayen da aka yi a ranar Asabar lokacin da mawaki Boubou Ngom ya yi waka a gangamin bukin Great Carnival na Dakar da aka yi.
A man with a horse drawn carriage. In the background there is vast arid land and some trees. It looks hot.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A Masar kuwa, a ranar Juma'a wani mutum ya tuka motar da dokuna ke ja kusa da ginin Temple of Luxor.
People walking past a mural of a woman with a mask. She has hoops on and a bantu hair style. It is a graffiti mural.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar Talata a birnin Soweto na kasar Afirka ta Kudu, wasu mutane a lokacin da suka wuce zanen wata mata.
Two football players celebrating. They are close to one another and appear to be shouting or cheering.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Laraba wasu 'yan kungiyar kwallon kafa ta Algeria sun yi murnar cin wata kwallo yayin gasar Fifa ta Arab Cup Qatar 2021.
A group of Ethiopian men cheering and shouting. Some of their fists are in the air. They are wearing the colours of the Ethiopian flag.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Sai kuma wasu Karin hotunan murna a ranar Litinin yayin da wasu 'yan kasar Habasha ke wata zanga-zanga a kasar Afirka ta Kudu.
A woman walking the runway, surrounded by smoke. The background the is black.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Juma'a wata mai tallan kayan kawa yayin da take tafiya a wani taron masu tallan kayan kawa da aka shirya wa masu fama da cutar sida a birnin Kampala na kasar Uganda.
Halima Aden smiling behind a large poster which says: "Voices".

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Halima Aden, wata musulma mai ------ 'yar asalin Somalia da Amurka ta tsaya don yin hoto a wani taron tallan kayyayaki a kasar Ingila a ranar Alhamis.
Wizkid and Burna boy performing on stage. Burna Boy is smiling and wearing a cowboy hat. Wizkid is wearing a big fur coat. Both have on sunglasses and jewellery. There is a red background.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shahararrun mawaka Wizkid da Burna boy sun yi wakoki tare a taron da aka yi a filin London O2 Arena ranar Laraba.
A large crowd in an arena with their phone lights on watching Wizkid perform.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wuta a kashe yake amma mutane na ta haska wayoyinsu yayin da suke jin dadin taron.

Dukkan hotunan na da hakkin mallaka.