Ku San Malamaku tare da Sheikh Muhammad Khamis Muhammad

An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

An haifi Sheikh Muhammad Khamis a ranar Juma'a, 3 ga watan Satumbar 1976, ya kuma yi karatu daban-daban tun daga karatun allo zuwa Islamiyya har zuwa karatun boko.

Malamin ya haddace Al-Ƙur'ani tun yana kimanin dan shekara 14, yana da shekara 16 kuma ya shiga Islamiya mai suna Madarasatul Abdulaziz Al-Islamiyya. Malamin da ya soma karantar da shi shi ne Malam Muhammad Umar.

Sheikh Khamis ya yi musabaƙar izifi daban-daban tun daga izu biyu har zuwa sittin da tafisiri. Ya bayyana cewa haddar Al-Ƙur'ani da ya yi a lokacin da yake da ƙuriciya ta ba shi damar halartar kowane irin zaure da ake yin karatu.

"Na halarci zaure irin na Malam Abubakar Tureta, sannan kafin ya rasu, yana karantarwa kuma akwai zaƙaƙuran ɗalibansa waɗanda idan ba shi nan ko yana da uzuri su ke zama kan kujerarsa su karantar, kamar Malam Umar Jibril wanda aka fi sani da Al-Basawiy kuma na yi karatu sosai a wajensa, sannan akwai Muhammad Yahya shi ma na yi karatu a wajenshi," in ji shi.

Malamin ya bayyana cewa ya kammala karatun sakandirensa a makarantar Government College Kaduna a 1994, kuma bayan ya kammala karantunsa na sakandiren ya yi difloma a Islamic Studies da Education a Ɗanfodio Institute da ke Kaduna, sannan kuma ya yi karatun Larabci a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna, kuma a kwalejin ya yi difloma a harshen Turancin Ingilishi.

Ya kuma yi NCE sa'annan ya kammala digirinsa a cikin shekara uku wanda tun kafin sakamakon digirinsa ya fito ya sayi form na masters inda nan ma ya yi ya gama, inda daga bisani ya tafi jami'ar jihar Kwara domin yin digiri na uku inda a nan ne ya zama dakta.

A halin yanzu Sheikh Khamis na daga cikin masu karantar da Larabci a Jami'ar Jihar Kaduna, kuma shi ne shugaban alƙalai na gasar karatun Al-Ƙur'ani na jihar Kaduna

Batun Iyali

Sheikh Khamis na da mata biyu da kuma ƴaƴa 11, duk da uwargidansa wadda ta haifi ƴaƴa biyar Allah ya yi mata rasuwa, haka kuma cikin ƴaƴa biyar da ta haifa ɗaya ya rasu.

"Ita kuma wadda nake tare da ita har yanzu ita ma akwai ƴaƴa shida, don haka ƴaƴana goma sha ɗaya yanzu Alhadulillah".

Surar da fi ba malam wahalar hadda

Shekih Khamis ya ce surar da ta fi ba shi wahala wajen hadda ita ce suratul Saba.

"Wa ƙalal ladhina kafaru lan nu'uminu bi hadhal Ƙur'an, waɗannan ayoyin da yake na yi hadda ne ayoyi biyar-biyar, tun daga kan waɗannan ayoyin zuwa ayoyi biyar sun zama mani yadda ka san wani dutse mai ƙarfi, yadda ka san ƙarfe, waɗannan ayoyin sun ba ni wahala ƙwarai da gaske," in ji shi.

Tambayoyin da aka fi yi wa malam

Ya ce akwai tambayoyin da mata suka fi yi masa da kuma waɗanda maza suka fi yi masa. Galibin tambayoyin da aka fi yi masa su ne waɗanda suka shafi zamantakewa ta auratayya ko abubuwan da suka shafi gado ko kuma abubuwan da suka shafi tarbiyya.

Su kuma maza tambayoyin da suka fi yi masa su ne na bangaren tarbiyya ganin cewa al'umma tana fuskantar barazanar tarbiyyya, kamar yadda ya bayyana.

Abincin da malam ya fi so

Malam ya ce shi a rayuwarsa babu wani abinci na musamman da yake so, duk wani abincin da ya samu na halal zai ci.

Ya ce abinci ko da nama ko ba nama zai ci, shi haka Allah ya yi shi.