Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaben 2023: A shirye muke mu ƙalubalanci APC domin farfaɗo da Najeriya - PDP
Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP ta ce a shirya take ta sake farfaɗo da Najeriya daga yanayin da take ciki muddin 'yan ƙasar suka ba ta goyon baya a zaɓen 2023.
PDP ta bayyana hakan ne a tattaunawa da sabon shugabanta Iyorchia Ayu da Sashen Hausa na BBC bayan wani taro da suka gudanar a Abuja.
Mista Ayu ya ce babu shakka a baya sun tafka kura-kurai, kuma sun amsa laifinsu ba kamar wasu gwamnatocin da ke yaudara ba, a cewarsa.
"Kowa ya san tun hawan gwamnati mai ci ta kasa cika alkawuranta, mu ba mu yi ƙarya ba abin da ba mu yi ba muna amsawa, kuma a yanzu a shirye muke mu gyara."
Shugaban ya ce sun shirya taron sanin makamar aiki tsakanin sabbin shugabannin jam'iyyar domin nazarin yadda za su tunkari tabarbarewar tsaro a Najeriya.
Ya ce abin takaici ne a ce yanzu mutum ba shi da kwanciyar hankalin tashi daga Abuja ya ratsa hanyar Kaduna, don haka yanzu a shirye suke su nemi hanyar kawo gyara.
"Kasarmu ta lalace daga Abuja zuwa Kaduna ko ta titi ko jirgi fargaba mutum ya ke, dole mu gyara Jam'iyyarmu ta yarda za mu samu goyon-baya a bai wa kowanne bangare damar tsokaci a yi aiki tare bisa abubuwan da mutane ke so."
Ya kuma ce: "Za mu tattauna da mutane domin jin bahasi domin ba za mu aminta da Najeriyar wannan zamanin ba da mutane ke juya akalarta daga ofis ba sa zuwa ga talaka.''
Mista Ayu ya ce tsarinsu zai kunshi kowa da kowa domin sanin kowa ne tun 1999 da suka soma karbar mulki sun samar da abubuwan ci gaba da more rayuwa.
Sabon shugaban ya kuma tabo batun mulkin tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo da Marigayi Yar'adua yana mai cewa kowanne ya tunkari matsalolin tsaro kuma an ga nasara.
Jam'iyyar PDP dai ta bugi kirjin cewa idan ta karɓi mulki a 2023 za ta kawo gyara da sauyi domin ta san hanyoyin ɓullo wa matsalolin tsaro.
Ya kuma ce, a yanzu komai ya tsaya iya yadda suka bar abubuwa babu wani cigaba da ake gani, wanda haka ke nuna gazawar jam'iyyar APC da rashin iya mulki sannan da kuma gazawa wajen cika alkawuran da ta yi wa 'yan Najeriya, in ji Mista Ayu.
Sannan ya soki yawan ciwo bashin da shugaban kasar Muhammadu Buhari yake yi da cewa ya sa kasar ta zama mabaraciya. Haka matsalar tattalin arziki ta mayar da Najeriya cibiyar talauci a duniya, a cewar shugaban na PDP.