Ko Afirka ta Kudu za ta rungumi fasahar makamashin hasken rana?

Boulders Way, Muizenberg, Cape Town, South Africa

Asalin hoton, Tom Podmore

Bayanan hoto, Yawancin sassan Afirka ta kudu na amfani makamashin da ake samu daga hasken rana wato sola
    • Marubuci, Daga Jesse Preyser
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Johannesburg
  • An wallafa

Har yanzu kasar Afirka ta Kudu ta dogara ne da amfani da makamashin kwal wajen samun wutar lantarki, duk kuwa da cewa yawancin yankunan kasar na samun akalla sa'o'i 2,500 na hasken rana a kowacce shekara.

Idan aka kwatanta da Birtaniya mai samun sa'o'i 1,500 a duk shekara, domin haka samun wata hanyar fasahar da Afirka ta Kudu za ta yi amfani da ita wajen samun wutar lantarki zai yi matukar inganta abubuwa da dama a kasar.

Ana hasashen lamarin ka iya sauyawa nan da shekaru goma masu zuwa.

A watan Yuni ne babban kamfanin samar da wutar lantarkin kasar Eskom, ya sanar da zuba dala biliyan 10 a shirin rufe wau daga cikin cibiyoyin lantarkin da ke amfani da makamashin kwal daga nan zuwa shekarar 2050, tare da rungumar makamashin hasken rana.

A lokacin babban taron koli kan sauyin yanayi na COP26 da aka yi a birnin Glasgow na yankin Scotland, kasashen Birtaniya da Amurka, da Jamus da Faransa da Tarayyar Turai, sun nemi a tara tallafin dala biliyan 8 da miliyan 500 nan da shekaru biyar masu zuwa, domin taimaka wa shirin na Afirka ta Kudu.

Shugaban kamfanin Eskom André de Ruyter, ya ce sanarwar da aka yi a COP26 za ta kai Afirka ta Kudu matakin cika burin da ta sanya a gaba.

Wani ma'aikaci ya na yanke wutar lantarkin da aka jona ba bisa ka'ida baa ranar 25 ga watan Agustan 2013 a Soweto, da ke kasar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana yawan samun matsalar wutar lantarki a Afirka ta Kudu

Sai dai ana yawan tambyar ko kamfanin Eskom zai iya rungumar wannan gagarumin sauyi.

A yanzu haka kamfanin na fadi tashin biyan wasu basuka da ake bin shi da suka kai daba biliyan 27, wanda aka zuba jarinsu da ayyukan ababen more rayuwa.

A bayyane take cewa ya kamata a yi saurin yin wani abu akai. Afirka ta Kudu ita ce kasa ta 12 a duniya da ke fitar da sinadarin carbon dioxide, sannan wadda ta fi kowacce fitar da hayaki mai gurbata muhalli a Afirka kamar da hukumar da ke sa ido kan hakan ta Global Carbon Atlas ta bayyana.

Ko da Eskom ya ci gaba da amfani da makamashin kwal, kamfanin ya ce zai bukaci dala biliyan 20 domin sake yi wa tsohuwar tashar makamashin kwal din kasar garambawul domin rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli.

Domin haka ne wasu daga cikin 'ya kasuwa ke cewa shirin na kamfanin Eskom da Mista de Ruyter ke bayyanawa abu ne da kamar wuya.

Cibiyar makamashin kwal da ke wajen birnin Pretoria.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana bin kamfanin wutar lantarki n Eskom dala biliyan 27 kan zuba jari da tsofaffin ayyukan ababen more rayuwa.
Presentational grey line

Sharief Harris, wani babban jami'i a kamfanin makamashi na Red Rocket Energy, ya ce idan akwai wani fata na komawa amfani da makamashin da ake sabuntawa, da farko sai Eskom ya magance matsalar ganawar da kayayyakinsa ke famu da ita da kuma matsalolin kudu.

Kazalika Mr Harris ya ce baya ga gina cibiyoyin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana, akwai bukatar Eskom ya kashe karin kudade wajen hada su da layukan wutar lantarki da aka saba amfani da ita.

"Akwai bukatar a jajirce wajen inganta tashoshin lantarki domin hada su da layukan wutar kuma $10bn ba za ta isa gudanar da aikin ba," in ji shi.

Babbankamfanin na hasken wutar lantarki ya yarda cewa a kiyasin da aka a kwanan baya ya nuna cewa yana bukatar kusan $35bn nan da shekara 15, idan yana so ya sauya baki daya zuwa tsarin samar da hasken ruwar lantarki ta makamashin da ake sabuntawa.

Fatan da ake yi shi ne a samu riba mai gwami daga kudin da aka zuma tun da fari wadanda suka kai $8.5bn daga Amurka da Turai, abin da zai karfafa gwiwar samun masu zuba jari daga kasashen waje.

Sharief Harris, the Head of Development at Red Rocket Energy

Asalin hoton, Red Rocket Energy

Bayanan hoto, Sharief Harris daga kamfanin samar da wutar lantarki ta hasken rana Red Rocket Energy ya nuna shakku kan ko Eskom zai sauya zuwa samar da makamashi mai sabunta kansa

A gefe guda, shirin Afirka Ta Kudu na sauyawa zuwa amfani da makamashin da ake sabuntawa zai iya samun taimako daga kamfanonin makamashi masu zaman kansu.

Idan ban da a baya bayan nan, tsauraran dokokin da gwamnatin Afirka Ta Kudu ta sanya kan kamfanoni masu zaman kansu na samar da hasken wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana, sun yi tarnaki kan sana'arsu. Sai dai a wannan shekarar an sauya dokokin domin bayar da dama ga kamfanoni masu zaman kansu su gina manyan tashoshin wutar lantarki - wadanda suka kai megawat 100.

A halin yanzu Red Rocket yana da tashoshin wutar lantarki masu amfani da hasken rana guda biyu da ke aiki Afrika kuma yana da niyyar fadada tashoshin.

The 75 megawatt Kathu plant in South Africa's Northern Cape.

Asalin hoton, Red Rocket Energy

Bayanan hoto, Afirka Ta Kudu tana bukatar daruruwan tashoshin wutar lantarki ta hanyar hasken rana kamar wannan da ke Kathu, Arewacin Cape

Sai dai Afirka Ta Kudu tana bukatar daruruwan tashoshin wutar lantarki ta hanyar hasken rana idan tana so ta daina amfani da kwal.

Sauyawa zuwa amfani da lantarki ta hanyar hasken rana wani babban kalubalen siyasa ne. A kasar da adadin matasan da ba su da ayyukan yi ya kai kashi 34 cikin dari, akwai alamomin tambaya kan ko sauyawa daga wutar lantarki ta hanyar kwal zuwa ta hanyar amfani da makamashin da ake sabuntawa yana da kyau ko ba shi da kyau ga ma'aikata.

Ministan Makamashi na Afirka Ta Kudu, Gwede Mantashe, ya nuna damuwa game da yiwuwar rasa yukan yi idan aka rufe tashoshin kwal. Ya bayyana shirin a matsayin wani "kisan kai na tattalin arziki".

Eskom ya kalubalanci hakan, kuma Mr De Ruyter ya ce samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana zai samar da ayyukan yi fiye da 300,000 a Afirka Ta Kudu.

Trainees at the Solar Green Academy in South Africa

Asalin hoton, Solar Green Academy