Hotunan tashin hankali da na kyakkyawan fata daga fadin duniya

Asalin hoton, Claire Thomas
Daga matan da suke koyon aikin ungo-zoma a Afghanistan, zuwa masu farautar mujiya a Mongolia, sai masu hawa dutsen Wyoming zuwa sansanin 'yan gudun hijira na Calais; Claire Thomas na dauke da hotuna daga sassa daban-daban na duniya.
'Yar jaridar mai daukar hoto, 'yar karkarar Carmarthenshire, ta shafe shekaru tana aiko hotunan da ta dauka daga sassa daban-daban na duniya masu kayatarwa, da ban sha'awa zuwa masu tayar da hankali.
Ayyukanta sun fito daga cikin jerin wadanda suka samu lambar yabo, da wadanda aka wallafa a jaridun New York Times, da Sunday Times da National Geographic.
Ta yi bayanin wasu daga cikin kayatatttun hotunan da ta dauka.

Asalin hoton, Claire Thomas

Asalin hoton, Claire Thomas
Claire, masoyiyar dawaki ce tun tana da shekara hudu, ta kwashe lokaci mai tsaho tana aiki a bargar dawakai da ke Wyoming, a Amurka.
Ta ce da fari, ta tsani yin aiki wuni guda, amma daga bisani sai kaunar wajen ta shiga ranta, ta sake komawa wajen bayan shekara guda domin kulawa da sama da dawakai 90.
A nan ne ta fara sha'awar daukar hoto, da dawakai da hawa wasu tsaunuka.

Asalin hoton, Claire Thomas
Bayan kammala karatu, Claire ta ci gaba da tafiye-tafiye, a lokacin da take Ghana ta gano cewa ayyukan da take yi ka iya kawo sabon sauyi a duniyar daukar hoto.
An yi amfani da hotunan da ta dauka, a lokacin gangamin taimaka wa mata masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki boye halin da suke ciki.
Hotunan sun taimaka wajen saya wa matan katifu, wanda a baya a dandabaryar siminti suke kwanciya, ga tsananin sanyi.

Asalin hoton, Claire Thomas
Hoton da ya tabbatarwa da Claire lallai za ta iya zama mai daukar hoto shi ne wanda ta dauki wani rakumi a gaban dalar gyada ta Giza a kusa da birnin Alkahira na kasar Masar.
An wallafa shi a mujallar National Geographic, kuma Claire ta ce shi ne "abin da ya zaburar da ni ci gaba da daukar hoto".

Asalin hoton, Claire Thomas
Claire ta ce ta "tsora ta matuka" da abin da ya faru a birnin Hebro na Falasdinu da ke yamma da gabar Kogin Jordan.
Ta ce ta ga wani taron dalibai matasa da ke zanen kalaman zaman lafiya da kyakkyawan fara.
"Kawai sai sojoji suka yi kan su da gudu. Sun ganni ina daukar hoton abin da ke faruwa, sai kawai suka jefo min gurneti. Abubuwa irin wadannan su na faruwa kusan kowacce rana."

Asalin hoton, Claire Thomas
A dajin da ya zamo sansanin 'yan gudun hijirar Calais, da ke arewacin Faransa, ta dauki hoton tashin hankalin da ke gudana a lokacin da hukumomi suka bukaci rufe sansanin.

Asalin hoton, Claire Thomas
Claire ta hadu da iyalai da dama a sansanonin 'yan gudun hijira da ke kasashen Faransa da Girka, wadanda suka ba ta kwarin gwiwar kwashe shekaru uku a kasar Iraqi, domin gano dalilin da ya sa mutanen ke tserewa daga muhallansu tare da rabe-rabe a wasu kasashen a matsayin 'yan gudun hijira.

Asalin hoton, Claire Thomas


Asalin hoton, Claire Thomas


Asalin hoton, Claire Thomas
Ta ganewa idanunta yadda yakin Iraqi ya daidaita kasar.
Ta kwashe tsawon lokaci a yankin Qayyarah, da ke arewacin Iraqi, ta kuma dauki hotunan 'yan kwana-kwana da ke kokarin kashe wutar da ababen fashewar da mayakan IS suka sanya ta haddasa.
Claire tace: "Na fara daukar yaki tsakanin gwamnati da mayakan ISIS, amma sai nake ganin kamar ba na bayar da labarin ainahin yadda ya kamata.
"Abu ne mai sauki ka sauya labarin yakin musamman idan ka duba kokarin da sojoji suke yi, don haka na yi kokarin shiga jikinsu, domin sanin kokarin da mutane ke yi na ganin karshen yakin.
"A lokacin ne na samu damar raka wata tawagar jami'an lafiya, wadanda ke aikin kula da wadanda ke sahun gaba a yakin. Sai na ji kamar hotuna da na dauka na kokarin nuna ainahin halin da mutane ke shiga a lokacin yaki.

Asalin hoton, Claire Thomas

Asalin hoton, Claire Thomas
A Iraqi, Claire ta makale sakamakon fari da aka yi fama da shi a lokacin.
Daya daga cikin hotunan da suka zama masu karfi fiye da kowanne, shi ne na jariri Suleyman dan watanni biyu da haihuwa, wanda wata likita mai suna Katie Batrouney ke kula da shi.
Ta ce: "Abin akwai daga hankali, da tsoratarwa. Ban taba ganin abu irin haka ba, ban taba ganin yadda rashin abinci mai gina jiki ke mayar da jarirai abin tausayi da tsoratarwa ba. A lokacin dukkanmu mun yi tunanin ba zai rayu ba."

Asalin hoton, Claire Thomas
Amma daga bisani ta samu bayanan Suleyman ya rayu.
Shekaru biyu bayan daukar hoton farko, sakamakon yadda jaridar Sunday Times ta wallafa labarin, sai gidan jaridar ya tura ta domin ganawa da Suleyman da mahaifiyarsa, wadanda ke zaune a wani sansanin 'yan gudun hijira.

Asalin hoton, Claire Thomas


Asalin hoton, Claire Thomas

Claire ta dade Afghanistan a shekarar 2019, kafin 'yan Taliban su sake karbe iko da kasar a farkon wannan shekarar.
A lokacin da take can, mata na tunanin shiryawa kansu rayuwa, misali suna zuwa koyon aikin ungo-zoma.
Sai dai Claire ta ce a yanzu ba ta son tunanin halin da suke ciki a yanzu ba.
Ta ce: "Kusan kowacce rana ina samun sakwanni daga wasu daga cikin irin matan, suna rokon na taimaka musu tserewa daga kasar.
"Abu ne mai ban sha'awa, ina fatan lokaci zai zo da kasar za ta samu kwanciyar hankali. Amma a yanzu abin mai ban tsoro ne da tayar da hankali."

Asalin hoton, Claire Thomas


Asalin hoton, Claire Thomas
Baya ga inda ake tashin hankali, Claire ta yi nasarar bibiyar wasu kabilu domin yin aikin da ya kara fito da soyayyar ta ga dawakai.
A tsaunin Altai da ke Mongolia, ta yi tafiya mai nisa da wasu kabilu, inda ta shiga cikin masu farautar mujiya.
Hotunan da ta dauka sun nuna yadda tsofaffin al'adun kabilu ke baraza ga bacewar wasu tsuntsaye da ingiza sauyin yanayi, duk dai daga kauyenta na Idole, kilomita kadan daga wajen Carmarthen.
Amma ta ce: "Ina ganin, muna fatan ayyukan da muke yi za su kawo gagarumin sauyi. Zan kuma iya cewa kwalliya na biyan kudin sabulu.
"Inda babu masu daukar hoto, babu masu bayar da labari, da babu mai jin labarin ainahin abin da yake faruwa a wasu yankunan na duniya musamman inda ake yake-yake da tashin hankali."












