Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Joseph Kabila: Yadda aka aike da miliyoyin kudin al'umma ga iyalai da abokan tsohon shugaban Kongo
Wani babban bincike da aka gudanar a Afirka ya nuna cewa kamfanonin da iyalai da abokan tsohon shugaban Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo Joseph Kabila suka mallaka sun yi wadaka da miliyoyin dalolin 'yan kasar ta hanyar amfani da asusan bankunansu.
An tura kudaden ne a asusan bankunan kamfanonin da ke reshen Kongo na bankin BGFI.
Daga nan ne aka cire miliyoyin dala na tsabar kudin daga asusan bankunan.
Mr Kabila ne shugaban kasar a lokacin da aka cire kudaden daga bankin.
Ya ki cewa komai game da tambayoyin da muka yi masa a kan cire kudaden.
Takardun da aka kwarmata sun zarta miliyan uku kuma suna dauke da miliyoyin bayanai na fitar da kudidaga bankin BGFI (Banque Gabonaise et Française Internationale), wanda yake da rassa a kasashen Afirka da dama da kuma Faransa. Wata mujallar shafin intanet ta Faransa da ke gudanar da bincike mai suna Mediapart da kuma kungiyar Platform to Protect Whistleblowers in Africa (PPLAAF) su ne suka samo wadannan bayanai.
Shirin BBC Africa Eye ya samu wadannan shaidu, a wani bangare na hadin gwiwa da ake kira Congo Hold-up, wanda kungiyar 'yan jarida ta European Investigative Collaborations (EIC) take jagoranta.
Bincike ya aza alamomin tambaya a kan su wane ne suka ci moriyar kudaden da aka cire daga bankin da kuma ko hakan ya saba da ka'idodjin aiki.
Kamfanin man da ba shi da mai
Manajan daraktan bankin BGFI reshen Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, BGFI Banque RDC, daga shekarar 2012 zuwa 2018 shi ne Francis Selemani, kanen Joseph Kabila.
Kanwar Mr Kabila, Gloria Mteyu, ta mallaki kashi 40 na bankin BGFI reshen Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, wanda aka bude a 2010.
An nuna cewa wani kamfanin mai zaman kansa, Sud Oil, ya karbi $86m na kudaden al'ummar kasar daga watan Nuwamban 2013 zuwa watan Agustan 2017.
Kudaden sun hada da $46m daga hukumar sa ido kan bakunan Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, BCC, da $15m daga kamfanin hakar ma'adinai na kasar Gécamines, da kuma $1.3m daga hukumar zaben kasar, Ceni.
Shaida daya tilo da BBC ta samu daga wadannan bayanai da aka kwarmata game da biyan kudaden ita ce wasta takardar shaidar biyan kudi ta abin da ya ɗan ɗara $1m daga Ceni zuwa Sud Oil game da kudin fetur.
BBC ba ta samu wata shaida da ta nuna cewa kamfanin mai na Sud Oil yana sayar da man fetur a wancan lokacin ba.
Matar Mr Selemani, Aneth Lutale, ta mallaki kashi 80 na kamfanin man na Sud Oil yayin da Mrs Mteyu ta mallaki ragowar kashi 20 daga shekarar 2013 zuwa 2018.
An fitar da miliyoyin daloli daga asusan kamfanin mai na Sud Oil da ke bankin BGFI zuwa asusan wasu kamfanoni masu zaman kansu da ke bankin na BGFI. Wasu daga cikin asusan mallakin 'yan uwa da abokan kasuwancin Mr Kabila ne, wanda ya shugabanci kasar daga 2001 zuwa 2019.
Daya daga cikin kamfanonin shi ne, Kwanza Capital, wanda akasarinsa mallakin dan kasuwar Kongo ne Pascal Kinduelo, yayin da kamfanin Sud Oil ya mallaki kalilan daga cikin hannuin jarin kamfanin. Mr Kinduelo shi ne shugaban bankin BGFI reshen Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo a wancan lokacin.
Kazalika Mr Kinduelo shi ne tsohon mamallakin Sud Oil, kafin ya sayar da shi.
Binciken ya gano cewa bankin yana bari a fitar da makudan kudade daga asusan Sud Oil, wadanda suka hada da fitar da $6m. Doka ta ce bai kamata a cire sama da $10,000 na tsabar kudi daga asusu ba a kowacce rana. Za a saba wannan doka ce kawai idan za a fitar da kudi wajen yin wasu ayyuka na musamman, wadanda suka hada da yanayi na gaggawa na kasa ko kuma dalilai na tsaro.
Shirin BBC Africa Eye bai gano wata shaida ba da ke nuna cewa an bi ka'ida wajen fitar da kudaden. Kudaden da aka fitar daga asusan bankin kamfasnin mai na Sud Oil sun kai akalla $50m a cikin shekaru hudu. Da zarar an fitar da kudaden, an yi imanin cewa ba a sake sanin inda suka yi.
'Akwai matukar hatsari'
Bincikenmu ya nuna cewa daga 2013 zuwa 2018 kamfanin mai na Sud Oil, yana da ma'aikaci guda daya ne kawai, manajan darakta David Ezekiel, da kuma karamin ofishi a babban birnin kasar Kinshasa a matsayin adireshinsa. A watan Okotoban 2013 Sud Oil ya sayi rukunin gidaje a babban birnin kasar a kan $12m, inda kamfanin yake.
Ya gudanar da kwangila ta bankin BGFI Banque na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo domin sayo sabbin ababen hawa ga manyan ma'aikata, wadanda suka hada da Mr Selemani. Ya karbi $70,000 domin sayo wasta mota.
Shirin BBC Africa Eye bai ga wata shaida da ke nuna cewa kamfanin yana gudanar da wasu harkokin kasuwanci ba.
Binciken ya samu damar ganin tsarin yadda ake kashe kudi da bin diddiginsu na BGFI, wanda aka kammala a watan Yulin 2018, inda aka yi matukar sukar bakin reshen Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo. Ba a so kowa ya ga tsarin yadda ake kashe kudin bankin ba.
Ya bayyana cewa "akwai matukar hatsari" game da yadda reshen Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo na bankin yake gudanar da harkokinsa. Ya kuma bayyana cewa babu gaskiya da bayyana abubuwa karara game da yadda bankin yake gudanar da lamuransa.
Binciken ya bayyana cewa Mr Selemani ya gudanar da ayyukan da suka ci karo da ka'idar aiki guda 16, wadanda suka hada da alakarsa da asusan bakunan kamfanoni masu zaman kansu. Ya kuma bayyana jerin harkokin kudi masu muhimmanci da Sud Oil ya gudanar.
Makonnin biyu bayan kammala binciken, an sauya wa Mr Selemani wani sabon mukami a hedikwatar bankin BGFI da ke Gabon. Rahotanni sun ce ya karbi $1.4m lokacin da ya bar reshen bankin da ke Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo. Rahotanni sun ce ya bar bankin na BGFI a watan Nuwambar 2018.
A shekarar 2018 ne aka sauya mamallakin Sud Oil changed sannan aka rufe Kwanza Capital. An fahimci cewa Mrs Mteyu ta sarayar da kashi 40 na hannun jarinta a BGFI Banque reshen Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kong.
BBC Africa Eye ya tuntubi BGFI, Joseph Kabila, Francis Selemani, Aneth Lutale, David Ezekiel da Gloria Mteyu game da bayanan da ke cikin binciken. Babu daya daga cikinsu da ya amsa tambayoyinmu. Mun tuntubi Pascal Kinduelo, wanda ya ki cewa komai.
Gecamines da BCC ba su bayar da amsa kan tambayoyin da BBC ta yi musu ba.
Shugaban Ceni a lokacin da suka yi alaka da Sud Oil, Corneille Nangaa, ya ki cewa komai a kan biyan kudin, yana mai bayyana tsarin majalisar dokoki na boye sirri.
Za a wallafa binciken BBC Africa Eye a shafin intanet domin kallo ranar 29 ga watan Nuwamba.