Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Warner, Henderson, Traore, Kounde, Ziyech, Dalot

Timo Werner

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Timo Werner
An wallafa

Barcelona na zawarcin dan wasan gaban Chelsea dan kasar Jamus Timo Werner, mai shekara 25, kuma za su iya daukar tsohon dan wasan RB Leipzig aro a watan Janairu.

Werner ya fara buga wasanni hudu kacal a gasar Premier bana. (Marca - in Spanish)Manchester City za ta bijirewa duk wani matakin da Barcelona za ta yi na sayen Raheem Sterling, mai shekara 26, a watan Janairu.

Ana danganta Barca da zawarcin dan wasan na Ingila, wanda ya fara wasanni uku kacal a gasar Premier bana. (ESPN)

City ta kuma shirya don gwada yunƙurin Tottenham a watan Janairu ta hanyar farfado da sha'awarta ta zawarcin ɗan wasan Ingila Harry Kane, bayan gaza komawarsa Etihad a bazara. (ESPN)

Kocin Ingila Gareth Southgate na dab da sanya hannu kan tsawaita kwantiragi, wanda zai kai kusan fam miliyan 5 a shekara, wanda zai sa kocin mai shekaru 51 ya jagoranci zakarun na turai karo uku har zuwa karshen Euro 2024. (Telegraph )

Dan wasan Chelsea na Morocco Hakim Ziyech, mai shekara 28, zai iya komawa Borussia Dortmund a watan Janairu, watanni 18 bayan ya koma Blues daga Ajax kan fan miliyan 33. (Mirror)

Jules Kounde

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jules Kounde

Sevilla ta kuduri aniyar ci gaba da rike dan wasan bayan Faransa Jules Kounde, mai shekara 23, har zuwa bazara mai zuwa duk da sha'awar da Manchester United ke yi. (Marca - in Spanish)

Tottenham na zawarcin dan wasan gaban Club Bruges dan kasar Belgium Charles de Ketelaere amma suna fuskantar hamayya daga AC Milan kan sayen dan wasan mai shekaru 20. (Calciomercato - in Italiyanci)

Valencia na neman dan wasan Wolves dan kasar Spain Adama Traore, mai shekara 25.(Sun)

Dan wasan bayan Portugal Diogo Dalot yana fatan ci gaba da zama a Manchester United duk da sha'awar da Roma ke yi, wadda Jose Mourinho ke jagoranta, kocin da ya kawo dan wasan mai shekaru 22 Old Trafford a 2018. (Caught Offside)

Dean Henderson

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dean Henderson

Golan Ingila Dean Henderson, mai shekara 24, na neman barin Manchester United bayan da David de Gea ya samu riga mai lamba daya. Henderson ya buga wasa daya kacal a kungiyar ta Red Devil a wannan kakar. (Mail)

Dean Smith, wanda Aston Villa ta kora a ranar Lahadin da ta gabata, na shirin komawa Norwich City bayan Frank Lampard ya fice daga cikin wadanda ake sa rai (Sun)

Paulo Fonseca bai yanke fatan jagorantar wata kungiya a gasar Premier ba, duk da kocin dan kasar Portugal mai shekaru 48 ya rasa aikin yi a Tottenham da Newcastle. (Sun)

Tsohon dan wasan Aston Villa Dwight Yorke, mai shekara 50, ya ce bai samu amsa ba lokacin da ya tuntubi tsohuwar kungiyarsa game da matsayin koci kafin nadin Steven Gerrard. (Sky Sports)