Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Pakistan: Gwamnti ta cimma yarjejeniya da Taliban
Gwamnatin Pakistan ta ce ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon wata daya da mayakan Taliban na kasar.
Kungiyar Tehreek-i-Taliban Pakistan, ko TTP ta tabbatar da hakan, kuma idan har dukkanin bangarorin biyu suka yarda za a iya tsawaita yarjejeniyar.
Kungiyar ta kai hare-hare na bam da yawa a kan fararen hula da soji a cikin shekaru.
A watan da ya gabata ne, Oktoba, gwamnatin Pakistani ta sanar cewa tana tattaunawa da wani bangare na haramtacciyar kungiyar ta Tehreek-i-Taliban ko a takaice, kan neman sasantawa.
Sai kuma Litinin din nan aka ji ministan yada labarai na Pakistan din na, Fawad Chaudhry na cewa, gwamnatin Taliban da ke Kabul ita ce ta kasance mai shiga Tsakani a tattaunawar.
Wannan mataki dai a iya cewa ya bude kofar samun damar yarjejeniyar zaman lafiya da ka iya kawo karshen zubar da jini da ake ta yi tsawon shekaru, musamman ma a yankunan kabilun kasar da ke arewa maso yamma.
Da yawa irin wannan yunkurin a baya na dakatar da bude wuta ya ci tura.
Ita dai kungiyar ta TTP daban take da ainahin kungiyar Taliban ta Afghan Taliban - duk da cewa ana ganin dubban mayakanta na cikin Afghanistan.
Tsawon shekaru take yaki domin hambarar da gwamnatin Islamabad, ta mulki kasar ta kudancin Asia, mai mutum miliyan 220, a bisa fahimtarta ta Shariar Musulunci.
Ana dai nuna fargaba cewa nasarar da Taliban ta samu a Afghanistan ka iya yi wa kungiyar ta Pakistan wadda a 'yan watannin nan ta zafafa hare-hare a kan sojojin Pakistan, kaimi.
Kungiyar ta kai dubban hare-hare na kunar-bakin-wake a Pakistan ciki har da harin shekara ta 2012 da ta kai wa, 'yar makarantar nan Malala Yousafzai, da ta taba cin kyautar Nobel, wadda ke fafutuka kan ilimin 'ya'ya mata.
Daga cikin hare-haren har da wanda ta kai kan wata makaranta da ke karkashin hukumomin soji a yankin Peshawar, kusa da iyaka da Afghanistan, inda ta kasha mutne 149, wadanda 132 cikin yara ne.
Jam'iyyun hamayya na Pakistan sun soki gwamnati kan yarjejeniyar dakatar da bude wutar da mayakan na Taliban da cewa, gwamnatin ita kadai ba za ta yi gaban kanta ba ta yanke wannan shawara ba tare da ta tuntubi majalisar dokoki ba.